Alk'alamin JIKAR NASHE
Ya Abin Yake?
Page 9.
08033748387
Ina macen datake fama da ciwon mara in mijin yana saduwa dake kirinka jin xafi to kixo kimallaki female care
Ina masu fama da basir constfree tea yana magnin basir yana gyara fata tayi kyau
Royal jelly ya gyara mace yafito mata da shafe dinta kama daga breast hips duwawo
Fat bunner yana rage kitse ina wanda kitse ya mata yawa a jiki kigarxayo kimallaki naki 09131164861
Gamai bukatan yin register xai iyayi yasaya afarashin company
Company ght zakiyi registered akan 4500 kikawo mutun biyu suyi siyaya company zatabaki 36000 inbaki shiryaba karkimin mgn ngd
_________________
Haka suka d'unguma zuwa ainahin main House d'in su da ke unguwar Hotoro G.R.A.
Mutanen gidan suna jin shigowar motocinsu suka fita a guje domin tararsa.
Sakina ce kawai bata fito ba, da yaranta masu bak'in hali Najma da Nasma. Amma hatta da Muneerat sai da ta fito a guje duk da kiran da Ammin take zabga mata.
Tunda ya fito ya zubawa k'annensa ido yana mamakin yarda suka girma lokaci guda. Har zai shiga sashen mahaifiyarsa Hamood ya kama hannunsa had'e da fad'in "Big Bro rufa mana asiri idan ba so kake Didi tasa ayi yak'in duniya na biyu ba."
Ya d'an bud'e ido yana kallon k'aninnasa, saboda sam ya manta a irin wannan lokacin Didin tana kasancewa ne a gidansu.
Ya juya direct ya nufa sashenta, yaransa da matarsa suna bin sa da sauri. Mahmah da take tsaye a window Ta saki Hamdala don farin cikin ganin yaronta, duk da kawaici da Alkunya ya hanata fita ta ganshi.
Didi da azama ta mik'e tana janye k'afarta da Hamda take shafawa Man zafi. Cikin fara'a kamar bakinta zai yage take fad'in Maraba lale, Oyoyo da mutanen Birmingham Masha Allah tubarakallah. Ta rungumeshi cikin tsananin farin ciki.
Hamda kuwa idanunta cikin na Kamla tana mamakin tsananin kamarsu. Su kansu su Khairi kallonta suke musamman Nanna da ta kasa janye idanunta daga kallon yarinyar mai kama da tata d'iyar Kwabo da Kwabo. Saboda duk zuwan da take Hamda lokacin tana makaranta shi yasa basu tab'a had'uwa da ita ba.
Hamda cikin ladabi ta durk'usa ta gaida Nanna, ita kuwa ta jata a jiki tana kallon Didi da Hammad da ya rintse idanunsa yana mamakin yarda yarinyar ta sake girma, da gaske kuma tsananin kamanninsu ya sake bayyana da Kamla musamman yanzu da suke zaune waje d'aya.
Cikin Masifa Didi ta dinga korar mutanen da suka yi dandazo a falonta. "Haba yau naji masifa, a bar mutum ma ya huta da jikokinsa ba za'a bari an zo an zuba musu ido kamar me? Ni jaraba ta yaran gidannan ta fara isata, mutane ga ido k'wala-k'wala, duk sun bi sun gado manyan idona na masifa."
Ta dinga mita bayan sun tafi sun barta da jikokinnata sai kace su ba jikokinta bane, ko da yake su kansu sun san soyayyar da takewa Hammad daban ce, ko kuma don kasancewarsa shine Jikanta Babba a maza tunda Najwa da suke kira Yana ta girme masa.Sai da suka tafin sannan ta zuba idonta akan Hamda ta saki baki tana kallon kamanninsu da Kamla.
Gaza shiru tayi har sai da ta magantu "Ikon Allah, ikon gaske kai kuma Hammadu sai ka haifo mai kama da Hamda kwabo da kwabo, ko wa suka yo a dangi don mu dai kaf danginmu ba masu kama da mutanen itofiya (Ethiopian).
Idanunsa ya zuba yana kallonsu, a duk sanda kuma ya kallesu sai gabansa ya buga fad'uwar gaba ta sameshi, baya son ana yawan ambaton kamanninsu haka ne yake sawa yaji k'irjinsa kamar ya tarwatse.
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.