Hankalinsa ne ya kai k'ololuwar tashi. Yana k'ok'arin zame Hamdan a jikinsa ita kuma ta sake cukuikuyeshi don ita ma ta gano tahowar Nannan ta tsakankanin kujera. Farin ciki ne ya kama shi ganin Nannan jiri ya d'ebeta ta rik'e kanta ta dafa wata kujera da take daf da ita ta zauna had'e da rik'e kanta. Ya saki ajiyar zuciya kafin ya zame Hamda daga jikinsa ya mik'e. Hamdan ta bi shi da kallo me nuna zallar haushin abinda ya yi mata sai kuma ta yi k'wafa ta mayar da kanta kujera tana cije gefen leb'enta da ya riga ya zame mata d'abi'a. Hammad ya shige ba tare da ya lura da kallon da Hamdan take masa ba. Abu d'aya ya sani ya san zuciyarta na nan tamkar ta buga don fushi.
A gefen kujerar Nannan ya tsaya ya dafa kafad'arta, da kyar ta d'ago idanunta da suka mata nauyi cikin jin barci ta ce "Ina kaje ina ta nemanka?" "Shi yasa kika taho jiri na kwasarki sai kace ni d'in k'aramin yaro ne balle na ce tunani ki ke zan b'ata." Ya fad'a cikin jin haushi da katse masa hutun da ta yi. Idanunta Dishi-Dishi ta dinga binsa da kallo har ta ga ya koma mazauninsa. A hakan duk da tana jin jiki sai da ta sake mik'ewa ta bi bayansa tana zuwa ta sanya kanta a cinyarsa ta k'udunduna a jikinsa kamar wani zai k'wace mata shi. A haka barci ya sake awon gaba da ita. Shi kuwa Hammad gaba d'aya ya raba hankalinsa kan Hamda da barci ya yi awon gaba da ita.
Cikin takaici ya sake zame Nanna da barcin ya d'an fara mata nauyi amma sai yaji ta sake rik'e shi gam murya a cikin barci take ce masa "please Dear na fi samun nutsuwa da barci mai dad'i a cikin jikinka."
Cikin takaici ya zabga matsakaicin tsaki kafin ya mayar da kansa jikin
Kujerar a hankali shima barcin ya yi awon gaba da shi.__________________
Cikin dare suka dira A airport d'in da ke garin kano Malam Aminu Kano International Airport. Hannun Nanna sak'ale da na Hammad. Ita kuwa Hamda da kyar take jan trolley d'inta ga jiri da take ji gaba d'aya yanayin ta ya canja kasala take ji sosai da alama kuma laulayin ciki ne. Wannan karan Hammad fuskarsa a d'aure ya janye Nanna daga jikinsa don ya tabbatar zuwa lokacin maganin barcin ya sake ta tana sane take sake narke masa a jiki uwa wata yarinya. Gurin Hamda ya je duk da banzan kallon da Nanna take wurga masa. Ya saka hannu ya janye trolley d'in da take ja da kyar ga wani amai da take ji yana taso mata. Idanunsa a kanta ya ce "Ya dai jikinne?" Kallo mai cike da harara ta wurge da shi kafin ta turo d'an guntun bakinta. Cikin mamakin lamarin shagawab'arta kawai ya ga ta saki hawaye yana gangaro mata ta kuma ya gaba da d'an sauri alamar bata son magana da shi. Murmushi ya saki yana jifanta da kallo. Sannan ya ja trolleynsa da nata ba tare da ya sake bi ta kan Nanna ba ya bi bayanta.
Taxi suka d'auka kasancewar ba wanda ya san da zuwansu sai Mahmah shi kuma ko su Humaid bai gayawa zai zo ba. Gidansu ya so wuce da su amma sai ya canja shawara ya wuce direct gidan Musty inda ya ajiye Hamda kafin su tafi. Ba'a gama gininsa ba shi kuma ba zai je gidansu a wannan daren ba mahaifinsa ya wulak'anta su. Sai da ya tsaya a Eatery ya yi musu take away ya siyi kayan tea sannan suka wuce. Nanna mamakin inda ta ga yace a nufa take don haka ta kalleshi ta ce "Me yasa ba zamu gidan naku ba? Za mu je gidan aro." Ya girgiza mata kai kawai ba tare da ya yi magana ba. Shi a gaban motar yake yayin da ita da Hamda suke baya. Bakinta ta ja ta tsuke ganin kamar baya son magana. Ga shi ya yi kicin-kicin da fuskarsa.
Kafin ya sallami maigadi Hamda ta shige gidan abinta ainahin bedroom d'in da ta mallakawa kanta nan ta shige kawai ta zube a gadon tana mayar da nunfashin wahala ita kad'ai ta san yarda take jinta bata san kuma me ya sameta ba. Nanna kuwa a parlour ta zube takaicin Hammad ne yasa ta kasa magana tana bin parlourn da kallo duk da tsarin gidan ya yi mata amma ita bata ga dalilin da zai kawo su gidan ba. Ga Gwanar na iya har ta shige bedroom d'in wanda da alama shine babba a gidan. Bari ta zo ta ji su kuma a ina za su sauka?
Yana shigowa hannayensa ya zuba a aljihu sannan ya dubeta "Ya baki shiga cikin bedroom ki samu ki yi freshing up ba?" Ta girgiza kai "Ta ya zan shiga ciki alhali ban san inda zan shiga ba." Mhmn" kawai ya ce yana tura d'ayan bedroom d'in wanda ya san Hamda bata cikinsa. Kuma shine k'arami don da alama ma d'akin yaran su Mustyn ne suke sauka idan sun zo. Nanna ta shiga cikin d'akin fuskarta a d'aure take bin gadon d'akin da kallo.
"Abu mafi dacewa dai kace da Hamda ta dawo nan, mu da muke mu biyu mu koma can." "Saboda neman rigima? Ta riga ta shiga na ce ta fito." Ya fad'a yana b'alle botiran rigarsa.
Nanna ta ja tsuka kawai "Amma ai nan gadon mu yayi mana kad'an?" "Sai ki bar ni ni na kwana da
hamda.."
Haka ya so ya ce sai kuma ya matse ya ce "Ba zai mana kad'an ba tunda dama duk fad'in gado da yalwarsa ba kya barina na sake nanik'ata ki ke." Ya fad'a yana kashe mata ido da d'an murmushi ya fad'a toilet d'in da Mustafan tuni yasa mai kula da gidan ya sake gyara musu duk da dama ba wani shahararren datti ya yi ba tsaf Hamda ta gyara shi kafin ta tafi.
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.