Har bakin k'ofa ya ja hannunta ta raka shi sannan ya nuna mata yarda zata kulle k'ofar kasancewar ta mai password ce. Yana murmushi ya fice daga gidan da d'an sauri nishad'i fal zuciyarsa Na mallakar matar da yake buri.
Ko da ya isa gidansa ya dad'e tsaye a k'ofar gida cikin mota yana tunanin yarda za su kwashe da Nanna dama danginsa gaba d'aya idan aka gano ya aure Hamda. Tabbas ya san sai Nanna ta kusa zaucewa kasancewarta a bigiren mata masu d'an banzan kishi. Ya lumshe idanunsa yana sakin murmushin hango tak'addamar da za'a buga, hakan kuma shine hanya d'aya da Ammi zata fito ta fad'i sirrin da take k'udundunewa.
Ya fice daga motar yana sakin ajiyar zuciya. A falo ya ga Nanna zaune ta ci kwalliya kamar bata so da gaske ta yi kyau sosai ya d'an zuba mata ido ita kuma sai sakin murmushi take don yau dai kam hankalinta a kwance yake kamar tsumma a randa. Tana murmushin ta ce masa "Har ka dangana ta ga gidan mijin?" Ya d'aga kai yana jifanta da na sa salon murmushin da kai tsaye za'a kiransa na mugunta. Ta mik'e ta koma hannunsa had'e da zaunar da shi kusa da ita ba k'aramin missing d'insa ta yi ba d'an kwanakin da suka yi ba sa tare. Shiga jikinsa ta yi sosai kafin ta ce "Yanzu hankalinka ya kwanta ka aurar da y'ar so. Na san zan samu kulawa da duk ka banzatar da lamarina." Ta fad'a tana wasa da sumar kansa. Ta nan ta ke karya lagonsa ya kuwa hau lumshe ido yana amsar sak'onta. Har cikin ransa tunanin Hamda yake ina ma itace zaune daf da shi haka tana wasa da sumar kan sa. Ganin ya amshi sak'onta kamar yarda take so ya sa ta sake ba da k'aimi kasancewar yara basa nan sun yi barci yasa ta samu sake ta dinga yi masa abubuwan da suka lula shi duniyar Hamda. Da sauri ya mik'e suka shige bedroom.
________________
Hamda kuwa tana jin tashin motarsa ta rufe k'ofar tana sakin wata irin ajiyar zuciya had'e da zubowar wasu siraran hawaye da zata iya kiransu kai tsaye na zafin kishi. Tana da tsananin kishi ita kanta ta sani shi Yasa sam bata so auren mai mata ba. Amma ba zata ja da hukuncin ubangiji ba za ta yi ta addu'ar Allah ya sauk'ak'a mata. Jikinta a sanyaye ta shiga ta gyara kitchen d'in da komai na cikinsa ya zama fari. Tsaf ya fito yana walwali tabbas Hammad ba k'ananan kud'ad'e ya kashe a gidan ba, gaba d'aya ya d'auke mata nauyin komai da ya kamata ace uba ne ya yi.
Parlourn ma komansa fari ne da adon black kad'an. Ta sake gyare parlourn sannan ta koma d'aki wanka ta yi ta tada sallolinta nafiloli kafin ta yi shirin barci ta kwanta. Sai dai me tana kwanciya tunanin Hammad ya fad'o mata yanzu haka yana can sun tsunduma wata duniyar shi da matarsa hakan ya sa ta runtse ido zuciyarta ta yi nauyi saboda b'acin rai. Addu'a kawai take akan Allan ya sauk'ak'a mata.
*******************
An ci nasara sosai Bakin Didi ya bud'e bayan yawan addu'oi daga bakin manyan malamai na karya sihiri sai dai harshen ya d'an karye kad'an maganar bata fita yarda ya kamata. Mijin Asma'u ya tabbatar musu komai zai daidaita insha Allah.
Da asuba kawai suka ji Didi tana kiran Atma'u wai Asm'au. Mama Asma'u ta yi saurin bud'e ido cikin farin ciki take duban Didi tana fad'in Alhamdulillah Didi na ke ce kika yi Magana." Didi ta d'aga mata kai tana sakin murmushi ta ce "Ni te Atma'u Alhamdulillah Na ta mu lafiya." Didi dai (s) d'inta ta d'auke gaba d'aya shi yasa take mayar da ita (t) Asm'au ta kama hannunta tana dariya Alhamdulillah Didi ta lumshe ido tana farin ciki itama da maganar da ta fara. Ashe ba k'aramar k'una wad'anda ba sa magana suke ji ba tabbas ta na tausaya musu a kuma yanzu take sake jajanta musu ubangiji ya sa hakan ya zama kaffara a garesu kuma sanadin shigarsu aljanna. A tsawon lokacinnan tana da abubuwan cewa da yawa sai dai ba halin magana rubutun kuma ba wai ta k'ware a hausan bane.
Ta mik'e sosai ta gyara zamanta "Atma'u kira min d'an Ki Hammad a waya, tun da abin nan ya faru nake cewa a kira min shi a waya tun k'i" Asma'u ta d'au waya ta shiga kiran layin Hammad a waya da layinsa na Birmingham.
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.