_~ALƘALAMIN JIKAR NASHE
YA ABIN YAKE ?
LIttafin Nazeefah Nashe.
08033748387
Follow me on wattpad
Nazeefah381
ELEGANT ONLINE WRITERS
**********************************
BIRMINGHAM
Dake k'asar England.
Unguwar padstow Road Birmingham B24.
A cikin d'aya daga cikin gidajen rent d'in masu bala'in kyau. Gida ne mai d'auke da 3 bedrooms da 1 parlour sai kitchen da dinning area.
Kamar yarda aka san gine-ginen turawa wannan ma gini ne da yake d'auke da tsari, da zarar ka kalleshi tun a waje zai birgeka balle idan ka shiga cikin ainahin building d'in.
Nanna ce zaune gefe guda da waya a hannunta tana kuka sosai bayan samun sak'on mutuwar Babanta.
Ta sake kallon Hammad mijinta a karo na biyu kafin ta ce "Kayi wa darajar girman Allah ka bini mu tafi tare har yarannan, yanzu fa Khairi shekararta Sha d'aya amma bata san danginka ba balle nawa, sannan yanzu ma Baba na ya mutu kace ba zaka ba, wannan wace irin masifa ce wai me aka yi maka a Nigeria?" Ta fad'i furicin hawayen na sake kwarara a fuskarta na zallar b'acin ran mijin nata wanda wani lokacin idan ya rikid'e mata sai ya zama kamar bak'in kumurci don fad'a da b'acin rai, wani lokacin kuma suyi zamansu gwanin sha'awa.
Wannan karan ma ya rikid'e d'in, don runannun idanunsa ya d'ago ya zuba su a kanta, wanda ya sata had'iye kukan babu shiri. Tayi saurin mik'ewa zata shige d'aki da azama ya fincikota, rintse idanunta tayi tana jiran taji saukar mari kamar yarda ya saba a duk sanda ta kawo masa zancen zuwan Sa Nigeria.
Madadin marin wannan karan hankad'ata kawai ya yi ya mik'e da sauri ya shige bedroom d'insa ya kulle k'ofar har da murza key.
Nanna ta runtse idanunta, don ta San tabbas abinnasa yazo, idan abin ya tashi zame mata yake kamar mahaukaci, sai kace mai aljannu. A hankali furucin Ya Allah ya fito daga bakinta.
Ba zata bishi ba don ta san ko zata shekara tana bugu ba zai bud'e ba a wannan bad condition d'in da yake. Allah ma ya taimaka yau baya zuwa aiki da bata san yarda zata yi da shi ba.
Wayarta ta shiga lalube ta fara danna kiran Mahmah, gwara ta gaya mata tayi iya yinta ya ce Ba zai zo ba.
Bugu biyu Mahmah ta d'au wayar, dafatan Allah yasa surukartata taci nasarar shawo mata kan d'annata. Madadin daddad'an labarin sab'anin haka ta samu. Mahmah ta runtse ido zuciyarta na karyewa bata san dalilin yaronta Na rashin son zuwa inda suke ba, ko su suke son ganinsa sai dai yayi Musu Visa suyi tattaki su je. Gashi wannan karan Didi ta takura ta gaya musu dole su saka Hammad d'in yazo gida musamman da surikinsa ya mutu.
Ta ja aijyar zuciya kafin ta ce "Shikkenan, ki kyaleshi zuwa anjima zan kira shi, dama har yanzu yana shiga wannan condition d'in?"
Nanna ta ja ajiyar zuciya kafin ta saki kuka na nuna alamun zallar damuwa ta ce "In dai zan masa zancen da ya shafi Nigeria sai yayi." Mahmah tayi jim kafin ta ce "Kin ga kuwa dole yazo ko dan na nema masa Magani, zuwa yanzu kam na tabbata ba k'alau tabbas akwai wani k'ulli da Allah ne kad'ai ya barwa kansa sani."
Daga haka suka yi sallama, Mahmah ta lalubi numberr Hammad ta tura masa text.
Slm.
Ya zama dole ka taho Nigeria a wannan gab'ar idan ba so kake na bayyana maka b'acin rai na ba ta hanyar sallamaka a cikin zuri'ata.
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.