Na sake bin idanunsa da kallo kamarsa da mahaifinsa har ta b'aci. Ganin idanun Didi kafe a kaina yasa cikin cunkushewar murya na ce "Sadiya Allah ya raya." Ba komai a fuskarta ta amsa "Ameen" Didi kuwa jifana take da kallo mai cike da ma'anoni iri-iri. Na fita gwiwoyina a sage har jiri na fara ji kafin na dangana ga d'akina.
A ranar Umar bai shigo sashena ba Sai daf da magriba, yana can ya tare wajen Didi sun saka Yaron a gaba, Haka ma su Gadanga da Asma'u duk suna can tare da shi. Wanda ni a tawa haihuwar ba'a Yi min wannan karar ba, wannan ne yasa na sake yardar anfi son haihuwar d'a namiji fiye da mace.
Sai lokacin kwanciyar barci sannan Umar ya shigo d'akina yana washe baki kamar gonar auduga. Ya ja jelar gashina Kafin ya ce "Maman Najwa ya aka yi?" Wani abu ya tokareni a k'irji tabbacin yau na tashi daga Maman Hammad da yake Kirana da shi, ya mayarwa da wata sunan. Zuciyata ta dinga zafi na ji duk soyayyar da nake masa tana rikid'ewa tana komawa k'iyayya. Muninsa na dinga gani tamkar bak'in kumurci. Ya zauna a gefena ganin kamar bana cikin nutsuwar zuciya "Wai me ya faru ne ina ta magana shiru?" Hawaye kawai na ji ya b'alle min daga idanuna ina kallonsa. Hankalinsa ya tashi ya dinga tambayata ba'a sin hawayena. Sai da na gaji da tambayar da yake min sannan nace mai yasa zaka sakawa Babyn can Hammad alhali ka san ni ce Zan haifi su Hammad. Wannan karan mamakina k'arara ya Bayyana a fuskarsa ya ja hannuna cikin tausasawa ya ce "Menene abin damuwa ina ce shima Hammad d'in d'an ki ne?" Girgiza kai na hau yi cike da tabbatarwa na ce "D'anta dai, ita kafi so ita ka yiwa cikin d'a namiji ni kuwa da baka damu da ni ba sai ka yi min cikin y'a mace." Wannan Karan dariya na bashi sosai sai da ya dara "Yanzu ke fisabilillah a karatun da kika yi ne kika karanto cewa matar so ita ce take haihuwar maza?" Kuka na saka masa sosai. Ya gaji da jin kukan nawa ya ce " Kin ga tashi mu yi magana don na lura akwai yarinta cikin lamarinki. Ita haihuwa da ki ke gani Allah ne yake tsara kayansa Ba mutum ba. Ba ni da ikon da Zan Sa ki haifi d'a namiji wannan ikon Allah ne, ki cigaba da addu'a idan da rabon Zaki haifi namiji sai ki ga kin haifeshi." Duk da zuciyata ta yi sanyi da jin furucinsa hakan bai hanani cewa "To yanzu wa kafi so tsakanin Najwa da Hammad?" Ya dad'e yana kallon k'wayar idona kafin ya saki murmushi ya ce "Duka ina son su, babu wanda Zan iya zab'a na bar wani a cikinsu. Son su nake har cikin jinina tunda dukkansu jinina ne." Na gyara zama fuskata a had'e don Ba haka nake so na ji yace ba, tunda na san a tsakanin ni da Sadiya ko makaho ya shafa ya san ni yafi so, to don me ba zai fi son nawa yaran ba? Sai dai ban yi masa magana ba na ja bakina na guntse amma daga yanayin kallon da yake min na san ya gane ban yi na'am da amsar sa ba. Ina kallo ya d'au Najwa suka fita falo cin abinci. Na bi bayansa da harara ina ji tamkar na guntile igiyar Aurensa na huta.
Ban sare da lamarin ba, Sai da na sake samun ciki, wannan karan ma Sadiya cikina yana wata uku ta samu nata cikin. Kullum addu'ata har a cikin Sallah Allah ya bani y'an uku maza ziryan. A wannan k'adamin har wata rama na yi ta fargabar abinda Zan haifa na kuma k'i zuwa scanning don kada suce min mace Zan haifa.
A zuciyata na sakankance mace Zan haifa don haka sawai nake jina. Cikin hukincin ubangiji da haihuwar ta zo still mace na haifa wacce aka sakawa suna Nasma. Gaba d'aya duk wanda ya sanni ya san ban yi farin cikin haihuwar ba sai dai na dake na dinga yak'e. Sadiya duk sanda ta d'au yarinyar sai na ji tace Masha Allah ina ma ni na haifi wannan zuk'ekiyar yarinyar. Harara nake zabga mata a zuciyata na ce kinibabbiya don na tabbatar farin ciki take da hakan. Ana gobe suna su Ummeey suka zo daga can k'asar mu Jordan. Kasancewar duk haihuwar da bake ba su tab'a zuwa ba wannan karan da ta ji sunanta aka saka Abeey ya ce Su taho.
Murnar ganinsu da na yi ita ta mantar da ni bak'in cikin haihuwar Nasma. Na shiga cikin dangina da k'annena sai farinciki nake. Amma ina lura da yanayin kallon da Ummeey na take wa gidan ita da k'annenta. Bata dai yi magana ba ganin Didi na wajen ta ja baki ta tsuke. Sai dai yanayinta kawai zaka kalla ka tabbatar bata yi farin ciki da inda ta sameni ba.
Sai da kowa ya watse kafin su yi shirin tafiya masaukinsu na kalleta cikin yaren garin mu "Ummeey me yasa ba za ku kwana a gidana ba." Ta girgiza kai had'e da tab'e baki tana waige-waige ta ce "Nan ne wajen da kike kira gida? Allah ya kyauta miki ke dai da kika mak'ale sai d'an nigeria za ki aura. Ji gidan da kike ciki kamar kango." Gaba d'aya annurin fuskata ya d'auke. Ba tun yau ba na san Ummina bata farin ciki da Aurena da Umar, sai dai yau ne na tabbatar lamarin k'iyayyar aurena da shi ta girmama a zuciyarta. Kifa kaina na yi a cinyarta ina sakin kuka ta shiga shafa min kaina murya k'asa-k'asa ta ce "Kin san duk cikin yarana ke ce mafi soyuwa a wajena, amma ba zan b'oye miki ba, ba na son aurenki da Umar wallahi, gashi kinzo sai haihuwar yara mata ki ke. Alamar k'wayak'wayanki da nasa na samar da yara mata ne kawai kamar yarda nawa da na ubanki ya zama." Ta fad'a tana cizar leb'e "Allah dai ya kyauta tunda ke ki ka ji,ki ka kuma gani. Don haka ba ruwana." Duk maganganunta basu dameni ba, kamar yarda ta ce wai ba zamu haifi yara maza ba ni da Umar. Hankalina kam ya tashi na runtse ido ina jin yarda take sake kambama lamarin.
Haka dai aka yi suna, Umar ya yi bajinta k'warai da gaske har sai da na dinga mamakin yarda yake b'arnatar da kud'i, kuma na tabbatar don ya yiwa dangina bajinta ne ya kuma nuna musu Ba a wahala nake ba. Sati guda suka yi cur kafin su tafi, duk da dama a hotel suke kwana. K'anwar mahaifiyata da muke kira Hala ta dinga fanfani akan lamarin Aurena sai dai ban ji ba.
Bayan haihuwar Nasma da watanni Sadiya ta sake sankato d'a namiji. Haka mu ka yi ta yi ni na haifi mace Sadiya kuma ta haifi maza duk kuma haihuwar da zata yi sai na saka kaina a d'aki na yi kuka sosai. Hankalina bai fara tashi ba sai da naga Gaba d'aya hankalin Umar ya fara tattara ya koma kan yaransa maza wani irin so da k'auna ta musamman yake nuna musu. A hasashena tabbas ya fi son mazan fiye da su Najma da suke mata, duk da dai ni duniya ta shaida ya fi so na amma fa bai damu da lamarin yara na ba. Sau tari zai saka yaran a gaba su fice ni kuma ya bar min nawa y'ay'an. Kuka nake sosai a d'aki na yi masa k'orafi ya fi a k'irga amma sai ya ce Hidimar mace sai mace y'ar uwarta. Dukkanmu yaran mu uku.
Gashi mun koma sabon gida. Lamarin nasa ya sake girmama bayan Hammad ya k'ara girma ba ya iya b'oye k'aunar Hammad a zuciyarsa. Ga shi ba ni da wata aminiya a Nigeria, ban san kowa ba kafin Allah ya had'ani da Kady. Wanda Zan iya cewa ita ce sanadin komai ita ta gurb'ata min tunani ta bani shawarar da har abada ba zan daina nadama ba.Ranar da muka had'u da ita ba zan manta Ba a asibiti ne lokacin ina da tsohon cikin Munirat. Na fito daga wajen likita d'auke da takardar scanning. Kasancewar wannan karan da kaina na zo a yi min scanning d'in. Sakamakon yarda cikin ya yi girma sosai fiye da cikkuna na na baya. Hakan yasa mutane suka fara kyautata min zaton namiji zan haifa ko y'an biyu. Son tabbatar da lamarin yasa na je a haska min. Sai dai sakamako ya bayyana k'uru-k'uru macece rusheshiya a cikina. Tun daga wajen Likitan na fara kuka har san da na fito mu kayi kicib'us da Kady. Wanda ya zama sanadin had'uwar kenan. Cikin firgici ta rik'oni tana fad'in "Subhanallahi yi a hankali mana, ke kuwa baiwar Allah ya da tsohon ciki ki ke shiga irin wannan damuwar?" Ban bata amsa ba har muka isa wani waje da ba hayaniya sosai muka zauna. A wajen kuka na ya tsananta na shiga bajewa Kady sirrin zuciyata ba tare da la'akari da cewa wannan ce had'uwarmu ta farko ba. Madadin na ga ta tausaya min sai na ga ta saki murmushi ta yi tsaki ta ce "Ke ki godewa Allah ma kina haihuwar matsalarki mai sauk'ice. Ni nan da ki ke gani na ban tab'a haifewa mijina k'wansa ba, sai dai na haife k'waya-k'wayan y'an uwansa." Na ware idona ina kallonta ta girgiza min kai "K'warai kuwa, Mijina ba ya haihuwa amma shi kansa bai sani ba kuma ba mazauni bane, a duk sanda ya yi tafiya anan nake shek'e ayata da k'annensa guda biyu d'aya cikinsu d'aya ma'ana uwa d'aya ce ta haifesu d'aya kuma ubansu d'aya. Kuma y'ay'an suka d'ebo dangi ta yarda ba yarda za'a yi ace ba nasa bane, ba ma wannan ba ko mutuwa ya yi za su iya cin gadonsa tunda gadon nasa na iyayensu ne, wannan yasa hankalina kwance yake, balle ta ki matsalar ma mai sauk'i ce, shin ba shi da k'ani?" Wata zufa ta shiga karyo min murya a sark'e na ce "Yana da shi mana." Ta tab'e baki "Yana da aure?" Na d'aga mata kaya "Ya yi aure da matarsa da yaransa biyu maza" "Shikkenan kin ga ta yarda za ki samu namiji kenan." Cikin tsoro da firgici na ce "Kamar yaya Zina kike so na aikata?" Ta girgiza kai cikin tabbatar min da zancenta "Zina mai tsafta kenan Zinar cikin gida, hankalinki kwance zaki haifi d'a namiji, ki kuma ajiyeshi a gidan a zuwan d'an gidan ne ya d'ebo kamanni da komai na mutanen gidan, ta yarda ba mai tuhumarki." Murya har rawa take wajen ce mata "Kady ba zan iya ba, ta ina zan iya janyo hankalin Gadanga?" "Ta kissa da kisissina da zarar kin haihu a lokacin za ki fara kai masa hari idan ya k'i ta lislama sai a biyo masa ta bayan gida. Duniyar nan fa yanzu haka take." Na yarfe gumin goshina ina girgiza kai idan har na yarda da batunta tabbas abinda zan haifa zai zama JININ D'AN BORNO...
(Ku yi hak'uri idan na samu sauk'i zan k'ara muku yawan typing d'in ciwon kai nake fama da shi ina barar addu'arku. Nagode)
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.