Zufa ce gaba d'aya ta jik'eta, tun kafin ta ji ainahin zancen, duk da in dai kunnuwanta sun ji daidai bata buk'atar k'arin bayani ko kad'an. A razane bata San sanda ita kanta ta murd'a mabud'in d'akin ba ta bur ma kanta ciki ba tare da neman izini ba.
Yanayin kallon da take jifansu da shi ya tabbatar musu ta ji abinda suka ce, tashin hankali ya bayyana b'aro-b'aro akan fuskokinsa, shi tunanin da yake daban itama Nanna nata tunanin daban, duk da ko ji Mahmahn ta yi ba zai zama laifinta ba tunda ba kai tsaya ta je ta sameta da maganar ba, balle alk'awarinsa na sakinta da zarar wani ya ji zancen ya tabbata.
Yarda suke kallonta a tsorace haka itama take kallonsu, kafin cikin dakiyar murya ta ce "Wace magana na ji kuna yi? Ina son jin gaskiyar zance don samun akasin hakan daga bakunan ku yana nufin bayyana muku asalin wacece ni, don tsaf Zan cire duk wani abu a raina na ci mutuncinku, Kamla y'ar waye? Da ta zama ba y'arku ba?" Bugun da zuciyarsa yake yi ya k'ara tsananta, don bai so lamarin ya zo masa a gicciye haka, ya yi alk'awarin b'oye Sirrin har lokacin da gaskiya zata yi halinta. K'asa ya yi da kansa yana cigaba da sauraran bugun da k'irjinsa yake yi, idanun Mahmah a yau sun masa kwarjinin da ya kasa kallonta kai tsaye ya furta mata abinda yake zuciyarsa wa zai ce mata itace Uwar Kamla idan shi ya zama ubanta?
Kasa furta ko kalmar 'A' ya yi ga tarin mamakinsa yau duk tsaurin idanunsa ya kasa fitar da maganar da ta zamo sirri mai girma a gareshi.
Har a lokacin idanun Mahmahn yawo suke yi a jikinsa cike da mamakin yarda ya k'i ya kalli ko inda take, balle ya kalli cikin k'wayar idanunta wanda idanun takewa duk y'ay'anta tarko idan ta na son jin gaskiyarsu, ta tabbatar shi yasa kai tsaye ya k'i kallonta. Kai tsaye ta mayar da kallonta kan Nanna da ta takure guri guda, duk da ita kanta tana masa barazanar tonuwar sirrin amma iya kan fatar bakinta kawai yake ba wai har zuciyarta ba, ba burinta fallasuwar sirrin ba don tana son Kamla tana kuma jin ta kamar su Khairi da ta tsuguna ta haifa bata sani ba ko don kasancewar Kamlan ta sha nononta ne, shi yasa take mata wata iriyar zazzafar k'auna. Ta sake k'asa da kanta tana nadamar tashin tashinar maganar da ta yi har tasa Mahmah ta jiyo zancen a ranta ta furta 'Tsautsayi' da kuma ba mamakin Allah ne ya so bayyana sirrin da suke b'oyewa da ko su Khairi ba su sani ba. Jin maganar Mahmah ta yi kamar dirar aradu "Tunda shi ya k'i gaya min, ke idan ba ki raina ni ba, gaya min wacece Kamla?" Karan farko da Nanna taji matsanancin tsoron Mahmahn ya dirar mata, sam bata san hakan Mahmahn take da kwarjini ba sai yau da ta tsatstsareta da idanunta fuskarta a had'e babu alamar wasa a lamarin Mahmahn. Tsawar da Mahmahn ta daka mata ya sata firgita, jikinta na rawa ta dinga kallon Mahmahn "Zaki fad'a ko ba zaki fad'a ba sai na tara muku jama'a?" Hannunta ta dinga yamutsawa cikin d'aya hannun, zufa na kwarara mata daga jiki, murya na rawa cikin wata irin Ininar da bata san da ta fara ta ba ta ce "Zan fad'a Mahmah." Mahmah ta gyara tsayuwa kafin tace "Ina jinki." Kujere Nanna ta ja mata ta nuna mata da son ta zauna, duk da ba ta jin tana son zaman ba hakan ta zauna still idanunta cikin na Nannan. "Mahmah zan fad'i iya abinda na sani, wallahi gaskiyata zan fad'a miki. Bana manta wata ranar alhamis da daddare har mun kwanta na ji wayar Abban Khairi tana kira, na d'aga ina mik'a masa ganin numberr garin da muke ce wato Birmingham da barci a idanunsa kawai na ji yana cewa "Alhamdulillah, masha Allah ta haihu? Shikkenan gani nan." Da sauri ya mik'e ni kuwa tsammani na d'aya daga cikin matan abokansa ce ta haihu yasa na ce masa wacece ta haihu? Girgiza min kai ya yi kafin yace "Ina zuwa, idan na dawo zaki ga ko wacece duk da baki santa ba." Daga haka ya yi saurin ficewa a gaggauce kamar ya fad'i. Mamaki ya kamani da tunanin wacece a garin wacce ba santa ba, sai kuma na tab'e baki na mayar da kaina barci ya sake kwasheni.Cikin barcin na ji yana bubbuga kafad'ata "Nanna Nanna tashi mu yi magana." Cikin idanuwan barci da suka min nauyi na bud'e idanun ina kallonsa mamaki ya kamani ganinsa da jaririya a hannu. Na murza idanuna sosai ina jifansa da ayar tambaya, murmushi ya sakar min had'e da saka min y'ar a cinya "Ki yi hak'uri kyauta Allah ya bamu don Allah kada ki tambayeni alfarma d'aya za ki min ki sanar da duniya ke ki ka haifeta." Tsananin firgita ya sa saura k'iris yarinyar ta sub'uce daga jikina a tsorace nake kallonsa, kafin da kyar na had'a kalmomin "Ban gane ba?" Ya girgiza kai sai na ga ya d'an saki ajiyar zuciya ya ce "Shi yasa tun farko na had'aki da Allah akan kada ki tambayeni ki k'addara kyauta ce Allah ya ba mu." Dangwara masa y'ar na yi a cinya fuskata da mabayyanin b'acin rai na ce "Wallahi sai ka gaya min y'ar waye? Kuma ta wace hanya aka haifeta? Kafin ka saka ni rik'eta dole." Ya girgiza kansa yana murza goshinsa kamar yarda ya saba idan ransa ya b'aci murya a shak'e ya ce "Y'ata ce Nanna, kuma ta hanyar halak aka haifeta Wallahil azeem." Takaici na ya girmama jin ya alak'antata da y'arsa na ware idona ina kallonsa kafin na ce "In dai har y'arka ce to sai dai idan ba ta hanyar halak ka samar da ita ba, don ban san sanda aka d'aura auren ba." "Ba ku ma za ki sani ba, tunda ba huruminki bane" Na ji ya fad'a cikin wata irin kaurin murya da ya saka na kalleshi kafin na d'ora wani abin cewa na ji yace "Wallahi, idan ba ki rik'e y'ar nan ba, ina tabbatar miki a satin nan zan auri wacce zata rik'e min ita, kuma idan ki ka bayyana sirrin nan ga wani ina tabbatar miki a bakacin aurenki matuk'ar ke kika furta ba ni na fad'a da kaina ba." Hanjin ciki na ya hautsina ganin cewa ya riga ya yi min dabaibayi da duk abinda nake tsoro sakin aure da kishiya. Hawaye ya b'alle min na shiga tambayarsa "Amma Abban Khairi me yasa zaka min haka? Hakan ya yi min tsauri." "Hakan kad'ai zan miki na samu kan ki, gobe zan sanar da dangi cewa kin haihu, kuma uwarta ta saka mata suna Kamla." Kuka nake kawai takaicinsa da bak'in ciki na nuk'urk'usar raina. Na zame na kwanta ba tare da na karb'i yarinyar ba. A daren ya gaya muku wai na haihu, kwana ya yi yana kula da yarinyar don na k'i yarda na karb'eta. Kashegari da na tashi da safe ya sake turkeni a d'aki ya tabbatar min idan ban amsheta ba yana tabbatar min a yau ba sai gobe ba zai je jami'ar Birmingham ya samu bahaushiya ya aura, bisa tilas na amince muka je asibita aka bani magunguna na samu ruwan Nono yazo haka kawai sai na tsinci kaina da son yarinyar kamar yarda nake son Khairi, na kuma ja baki na k'ulle ba wanda na bayyanawa don ina tsoron saki da kishiya, wallahi Mahmah wannan shine abinda na sani, kuma har yau bai gaya min gaskiyar magana akan Kamla ba ni kuma ban sake tamabayarsa ba, ko su Khairi ba su san ba cikin su d'aya da Kamlan ba."
A gigice Sadiya ta watsa mishi mari, cikin b'acin rai take tabbatar masa ba zata bar d'akin ba sai ya sanar da ita Wacece Kamlan?" Rik'e yake da k'uncinsa ya kasa fitowa ya mata magana sai ajiyar zuciya yake, don shi dai zai iya cewa tun tashinsa bai tab'a ganin Mahmahn ta mareshi ba sai yau, kuma yana hango tsananin b'acin rai a idanunta, amma ya gaza furta mata wacece Kamlan? Alk'awari ya d'auka, abinda shi kansa ya san a yau ya kamata ya sauke alk'awarin amma ina? Ya riga ya d'au alk'awarin ba zai furta da bakinsa ba har sai lokacin bayyanuwar hakan ya yi.
Durk'ushewa ya yi a gaban Mahmahn cikin tashin hankali ya rik'o hannayenta ya saka fuskarsa a tafin hannayen "Allah ya huci zuciyarki Mahmah bakina ba zai iya gaya miki ba." Cikin b'acin rai ta janye shi daga jikinta murya a raunane ta ce "Idan baka gaya min ba, ai zaka gayawa Didi da ubanka don a yau ba sai gobe ba zan sanar da su." Ya dinga rok'onta tare da neman ta bashi kwana biyu zai sanar da ita wacece Kamlan, da kyar ta amince da hakan, shima don bata son ta tara masa jama'a ne ta fi son ta ji ta yarda ya samu Kamlan kafin ta san ta yarda zata b'ullowa lamarin. Cikin sanyin jiki ta fice daga d'akin tare da tabbatar masa kwana biyun jal da ya buk'ata ta bashi yazo mata da cikakken bayani.
Tana fita ya saki ajiyar zuciya ransa a b'ace ya dubi Nanna ya ce "Hankalinki ya kwanta..." bakinta na rawa ta dubeshi "Me kake nufi Abban Khairi ka san dai ba ni na gaya mata ba." Ya zuba mata narkakkun idanunsa kafin cikin b'acin rai ya ce "Ni na gaya mata kenan? Ba zan ce miki komai ba a yanzu amma ina tabbatar miki sai na d'au zazzafan hukunci a kanki." Daga haka ya yi k'wafa ya fice, Hamda kawai yake son gani a lokacin amma Didi ta yi masa katangar k'arfe da ita, ita kuma da yake mashiririyace ko ta neme shi, ya cije leb'ensa ya na son tattaro duk wata nutsuwa ya sawa kansa amma abu ya faskara, ya dinga zabga tsaki kafin ya isa Sashen Didin yana fatan ya tarar ta yi barci ko zai samu ganin Hamdan.
Umma Asma ce kawai a falon hannunta rik'e da waya da alama waya take da mijinta, ta ji ya turo k'ofar ya shigo, da hannu ta dinga nuna masa lafiya? Ya girgiza mata kai shima da hannun ya nuna mata wajen Hamda ya zo. Ta ware idonta kafin ta yi saurin katse wayar tana rik'e hab'a "Rufa min asiri Hammad, kada kasa Didi ta fige ni, baka ji me tace maka bane d'azu?" Idanunsa ya marairaice da son ta tausaya masa "please Umma mana, ko nan ta fito ni ba abinda zan mata zance na zo tunda ance sai na sake neman auren daga tushe." Ya fad'a yana murmushi. Asma'u ta girgiza kai "Zancen ne da Sha d'ayan dare? Duk zancen arziki ai da yamma ko magriba ake yin sa." Ni dai don Allah ki taimaka min wallahi akwai abinda zan tambayeta." Ta bishi da kallo tana hango fitina kwance a idanunsa ita ba ruwanta ba zata d'au hak'kkinsa ba kan wani zancen Didi mara tushe, ta mik'e had'e da cewa "Bari na turo maka ita, amma ka tabbata daga zancen ba a zarce k'aida ba?" Murmushin gefen kumatu ya bita da shi a zuciyarsa ya ce "Wasa kenan ni da Halak d'i na."
A zaune ta samu Hamdan hannayenta zube a kuncinta, sai ta ga ta mata haske ta sake kyau duk da ramar da ta yi. Ta zare mata hannun tana sakar mata murmushi "Ba kyau dogon tunani, ki je mijinki yana kiranki, kada dai ki sake ya wuce gona da iri Didi gata zata miki don ban tab'a jin irin aurenku ba ko a labari. Ki bari a kaiki gidansa cikin mutunci a kuma gyara miki jikinki ta yarda zaki martaba fiye da yanzu a idanunsa, kin ji na gaya miki, idan ki ka bari ya moreki ina tabbatar miki ba zai miki lefe mai nauyi ba, haka kawai ya sameki a araha." Sunkuyar da kanta ta yi tana jin zuciyarta tana amincewa da duk abinda Umma Asman ta ce mata. Ta tabbatar soyayyar da suke mata ita da Didi sam ba algus a ciki, dole ta siyawa kanta mutunci.
Hijabi ta saka zunbulele a jikinta. Sannan ta fita.
Tun daga nesa yake jifanta da kallo yana jin takaicin dogon Hijabin da ta zumbula, yaushe rabon idanunsa su ga halittun jikinta? Amma yau da ya samu dama ta wani saka dogon hijabi ta k'dudundunesu. K'aramin tsaki ya ja, yana mata kallon k'asan ido, cikin wata irin murya da bata san shi da ita ba ta ji "You better takeoff your Hijab, before coming here." Turus ta yi tana mamakinsa "Ina ruwansa da Hijabinta da zai ce sai ta cire sannan zata zo, ba ta cire d'in ba ta cigaba da isa inda yake. Tsam ya mik'e tsaye yana manna ta da jikinsa, sanin cewa ba wanda zai gansu "Ba ki ji me nace miki bane? Amma kika min kunnen uwar shegu." Ya fad'a yana k'ok'arin cire Hijabin ita Kuma ta k'i ba shi damar hakan, har sai da ya saka hannu ya doke hannunta sannan ya samu damar zare Hijabin. Saura k'iris ya yi suman tsaye kasancewr rigar barci kad'ai a jikinta, yana k'ok'arin manna ta da jikinsa ta yi saurin durk'ushewa tana duk'unk'une jikinta murya na rawa ta ce "Please mana Yaya Hammad don Allah ka bari." Ganin bashi da niyyar bari ya sa ta d'an saki kuka da ya saka shi k'ara mannata da jikinsa yana lalubar bakinta. Daidai lokacin da ya ji muryar Didi tana fad'in "Wani Kwalton ne anan cikin dare? Muhammadu rasulillahi." Zuciyar Hamda ta buga.. amma shi ko gezau bai yi ba....Hamda na k'ok'arin tureshi ya manna bakinsa a cikin nata, suman zaune ta kusa yi, tana nuna masa Didi da take kusan tosu hannun ta d'auke da sandan mopper...Jikar Nashe ce✍🏽✍🏽📖
❤️❤️❤️❤️❤️🙏
BẠN ĐANG ĐỌC
Ya Abin Yake?
Tiểu Thuyết ChungUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.