ALK'ALAMIN JIKAR NASHE
YA ABIN YAKE?
BONUS PAGE 19...
08033748387
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
Nanna jiki na rawa take kallon Dida da nufin bata hak'uri, sai dai Didan ko kallonta ba tayi ba, saboda ranta ba k'aramin b'aci ya yi ba, Ta rasa wace irin k'wakwalwa ce da Nanna sam albasa ba tayi halin ruwa ba.
Ko da Khairi ta sanar masa da sauri ya fito daga motar duk zatonsa Nannan wani mugun abu tayi wa Hamda, tabbas yau da ta gane Kurenta.
Turus ya yi a bakin k'ofar falon Didan ganin Hamdan lafiya lau take. Cikin sakin fuska Dida ta ce ya shigo ya zauna. Kamar ba zai shiga ba sai kuma ya daure ya saka kai ya shiga.
Bayan amsa gaisuwarsa Dida ta ce "Gata nan Hammad tunda ba taji duk shawarar da na bata game da ta hak'ura ta rik'e yarinyar nan, ka saketa kawai saboda idan ka tafi da ita ba k'aramin tashin hankali zata sakawa zuciyarka ba. D'agowa ya yi idanunsa cikin na Nannan yana mamakin yarda gaba d'aya ta sauya kyawawan d'abiun da ya santa da su. Tsaki kawai ya ja kafin a hankali cikin ladabi ya ce "Ki rabu da ita Dida, kada ma ki sawa zuciyarki b'acin ranta. Da zarar mun je can zan yi solving d'in abin ba dai yarinyar ce bata son gani ba, to muna zuwa zan aurar da ita ta tare a gidanta." Dida ta saki tsakin takaici "Bata isa ba wallahi, kai da gidanka kana da ikon kawo duk wanda kake son ya zauna tare da kai, sai dai ita ta bar gidan." Agogo ya kalla murya a cunkushe ya ce "Ki yi hak'uri, ya zame mata tilas ma ta gyara,
Yanzu za mu wuce kada mu yi missing flight." "Shikkenan Hammad Allah ya tsare ya baka ikon sauke nauyin da yake kanka." Har bakin k'ofa ta raka su, tana sake jan kunnen Nanna cikin nasiha da lallashi. Jikinta dai ya yi sanyi a zahiri amma a bad'inance ita kad'ai ta san takaicin da yake nuk'urk'usarta.______________________
A tsorace Hamda take sosai a cikin jirgin, musamman kasancewar wannan shine first flight d'in ta. Duk ta bi ta takure kanta ta kasa sukuni, yana lura da duk wani motsinta shi yasa ya ce Khairi ta koma kusa da ita. Khairi kuwa ta murje idonta ta koma duk da hararar k'asan ido da Mommynta take zabga mata.
Tun tana tsoro har ta saki jikinta ta zauna ganin tafiyar ba nan kusa bace. Abincin jirgin ne dai sam ta kasa ci saboda aman da take ji, kuma ma yanayin abicin nasu bai yi mata ba.
Kusan asuba suka sauka a k'asar ta England cikin birnin Birmingham, sam ba tayi tunanin garin da sanyi har haka ba shi yasa bata tanadi rigar sanyi ba, shima kuma bai yi azancin siyo mata rigar sanyin ba. Sosai ta dinga rawar d'ari hak'oranta na kafkaf kamar za su datse harshenta. Samun kansa ya yi kawai da zare jibgegiyar rigar sanyin da take jikinsa ya mik'a mata. Hannu na rawa ta damk'i rigar ta saka. Tana jin nutsuwa na sauka a ranta. Tsaki Nanna ta ja a fili tana mamakin dalilinsa na kaffa-kaffa da yarinyar har da wani cire rigarsa ya bata, bayan ta san shi da matuk'ar jin sanyi. Bai damu da kallon da take wurga masa ba yayi gaba cikin takunsa na k'asaita.
K'arfe 8:00 daidai suka isa bakin gidan su. Ya saka mukulli ya bud'e y'ar madaidaiciyar k'ofa. Gidan na nan tsaf da shi kasancewar yayi wa mai hidimar gidan waya tun shekaranjiya shi yasa ya gyara gidan tas. Sai zabga k'amshi yake. Ta samu kujera ta rab'e ganin ba wanda ya bi ta kanta. Hannayenta zube a k'uncinta tana mamakin yarda rayuwa take juyin waina da ita. Dubi dai yarda lamarin ubangiji yake ikonsa a kanta ko a mafarki ba ta tab'a zatan zuwa k'asar nan ba, sai ga shi Allah ya kawota. Sai dai rashin sanin irin rayuwar da zata yi ne yake fad'ar mata da gaba daga yanayin matar gidan ta fuskanci k'warai ba tayi na'am da zamowarta cikin gidanta ba.
Ita kuwa Khairi suna shiga d'aki Nanna ta saka su a gaba da jan kunne, ko da wasa ku ka shiga sabgar shegiyar y'ar can wallahi sai na ci mutuncinku. Kamla idonta ya kawo ruwa sam bata son Mom take hanata huld'a da Hamda, saboda tana son ta sosai. Hakan yasa dole Khairi ta zauna ba tare da ta kira Hamdan sun shiga d'aki ba.
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.