Likitoci sun yi rufdugu akan Abbu, don kuwa yana jin jiki sosai k'ok'ari kawai suke su ceci numfashinsa, hankalin zuri'ar d'an Borno ba k'aramin tashi ya yi ba, musamman Hammad da lamarin ya zame masa kashi-kashi. Ga can Hamda a kwance rai a hannun Allah itama don ba k'aramin wuya ta sha ba, kafin cikin ya fita, cikin da Hammad ya ji fitarsa har k'olouluwar zuciyarsa. A yanzu ba ya da buri irin ya ji shi kusa da Hamda yana lallashinta rungume a k'irjinsa. Hawayen da take ba k'aramin b'ata masa rai yake ba. Umma Asma ce a wajenta. Don Ammi ko kallonta ba tayi ba tana can wajen mijinta hankalinta a matuk'ar tashe duk da kallon banzan da Didi take jifanta da shi, jira take kawai Ummaru ya farfad'o ta ji hukuncin da zai yanke akan Sakna. Muddin hukuncin kuwa bai mata ba ita da kanta za ta zartar da nata hukunci. Don haka kallonta kawai take tana caccije leb'e cike da takaicinta. Don bata da kunya har da wani zuwa asibiti, ita kuwa Sadiya shashasha ko me ta zauna yi a gida? Nan ma takaicin Sadiyanne ya kamata sosai har bata san sanda ta kalli Hameed ta ce "Kai kila min gallafiriyal Uwalka ." Ransa a b'ace ya dubeta yana mamakin sunan da ta kira uwarsa da shi, ko kunyar idanunsu bata ji ba. Tsaki ta ja ganin yarda ya tsatstsareta da ido ta ce "K'alya na yi? Ai a haka aka mayalta bola mace ba kan gado kawai ta na abu te kace wani lokacin jahiliyya, ko ni sanda mu kayi rayuwal aule da Utmanu bana wannan shashancin, Allah wadalan naka dai ya lalace." Shiru su kayi mata cike da takaicinta, duk da suma Mahmahn ta ba su mamaki da har yanzu ba ta zo ba, don haka Hameed ya fita waje da niyyar ya kirata a waya. Ita kuwa Sakna gabanta sai fad'uwa yake, sam bata son had'a ido da kowa a wajen musamman Didi da take mata kallon tsana muraran.
A karo na biyu Didi ta kalleta ta ce "Wai ke Takna ban ga amfanin tsayuwalki anan ba, Fitabilillahi, ki tafi wajen y'alki mana tunda dai kin san duk nan kala ce za mu miki ba mu had'i da yalinyal nan ki wuce ki je wajenta Atma'u ta zo wajen d'an uwanta ina dalili? Kuma ki tabbata gobe ki kawo min gantalallun da ki ka ce sun d'aula miki aule da Buzu, don ni har yanzu tantamal lamalin nake." Sakna idon na zubar da hawaye ta yi k'asa da kanta. Gaba d'aya ranta a jagule yake ta kuma ji duniyar ta canja mata, don harta yawun bakinta k'afewa yake, idan kuma ya zo ma mai d'aci ne yake zuwa. "Dama ki san yarda za kiyi da y'arki, don ba amince da aurenta da Hammad ba, ki tattarata ki kaita duk inda ki ka ga dama mara tsoron Allah kawai, kika dinga cutar yarinya ba da hak'kinta ba, yanzu kuwa tunda mun gane ba jininmu ba ce dole ki amshi abar Ki, kuma tilas ki rik'eta wallahi tunda ta ki ce." Lauratu ta fad'a fuskarta cike da takaici. Gadanga ne ya ja tsaki ya ce "Wannan abin da ake fa kamar bai kamata ba a bari mana ma su samu lafiya kafin a samu matsayr zance haba?" Didi ta b'ata fuska tana jifansa da harara "Zancen banza zancen wofi, har akwai wata matsayar zance da ya wuce Ummaru ya yiwa y'ar banza saki uku, ni Gadanga ban gane nufinka na zak'alk'alewa a halkal Takina ba, haba ina dalili na ga dai ba k'anwal Uwaliya ba ce ko ta Ubaliya." Gadanga shiru ya yi mata bai tanka ba, ganin yarda ta d'au Abin da zafi. Daidai lokacin likitan ya shigo Inda suke fuskarsa a d'an washe alamar sun samu nasara. Yana kallonsu ya ce "Alhamdulillah, Alhaji ya samu lafiya sai dai ana buk'atar ya huta k'warai da gaske, don haka duk ku wuce gida a bar matarsa da d'ansa guda d'aya Kawai." Hajiya Didi ta gyara zama idanunta akan na Sakna ta ce "tai a tafi gida ko? Don wallahi ba zan balki a wajenta ki k'alasa min shi ba, ita waccan ballagazal tunda ta k'i zuwa shikkenan tai mu yi zamanmu da Hammadu." Hammad ya d'ago ya Zuba mata wani irin kallo kafin ya ciji leb'ensa kawai ya mik'e yana cewa "Ki dai nemi wanda zai ta ya ki zama ba dai Hammad d'an ballagaza ba." Daga haka ya fice ya bar Didi da masa kallon mamaki, su Gadanga kuwa k'unshe dariyarsu suka yi, shi da d'aukacin mutanen da suke d'akin. Ko bakomai Hammad ya yi maganin ta. Ta jijjiga kai ta ce "Ba takka, yau ka nuna min iyakata, wato haushi ka ji an kila uwalka ballagaza alhali ba k'alya na yi ba. Idan Banda sha ka tafi waye za'a kai mijinsa asibii Langa-langa sannan ya shale waje ya yi zaune a gida sabida lashin mafad'i, Allah na tuba ba ta inda wannan matal ta kankane mijin ba kenan?" Ta fad'a tana cuno baki tana nuna Sakna. Ba wanda ya tankata a d'akin suka fice don zuwa su ga Abbu.
A bakin k'ofar d'akin suka ci karo da Hammad ya fito daga duba shi kenan Zai wuce wajen Hamda da hankalinsa yake kansa tun d'azu. Da sauri ya shige don kada ma wani ya dakatar da shi.
Idanunta a lumshe yake, Duk da kana ganinta zaka san ba barci take ba, ta hanyar ganin hawayen da yake zubowa a gefen idanunta. Tun d'azu Asmau take aikin rarrashinta amma ba tayi shiru ba, tausayinta ya gama dabaibaye Umma Asma'un ta rik'e Hannayenta kawai. Tana murza mata su a hankali. Daidai lokacin da Hamdan ya shigo fuskarsa cikin ta Umma Asma'u. Ajiyar zuciya ta saki tana cewa "Gwara da Allah ya kawoka, likita ya tabbatar min jininta ya hau amma har yau ta kasa yin shiru, ta saka damuwa a ranta wallahi." Taku biyar ya yi jikinsa a sanyaye ya isa bakin gadon ya tsaya. Umma Asma'u ta mik'e tana cewa "Bari shima Yaya in je in duba jikin nasa, ga dare yayi zan ja Didi mu tafi gida ko don ta samu ta huta ta yi sahur." Ya jijjiga kansa kawai hakan ya yi masa zai zauna da matarsa. Har k'ofa ya rakata sannan ya saka key ya rufe gam. Zama ya yi a gefen gadon sosai ya mik'ar da ita ya jingina da jikinsa. Jinta a jikinsa ya sake damalmala zuciyarta ta shiga kuka ba ji ba gani. Dama jikin wani take nema inda zata yi kukanta sosai sai dai ta tabbata ba ta da wannan gatan, tunda ga UMMA Asma d'in ma ta tafi alamar shi Hammad d'in ne kawai gatanta a Yanzu.
Shi kansa tasa zuciyar bugun take kukannata yana jinsa tamkar d'igar dalma a tasa zuciyar. Ya lumshe idanunsa kawai yana jin sautin bugun k'irjinta, da yake d'agawa yana sauka a hankali. A kunne ya dinga rad'a mata wasu kalamai da suka samar da nutsuwa a zuciyata, sai dai hakan ba yana nufin yayewar duka damuwarta da bak'in cikinta bane, amma kaso goma cikin d'ari ya tafi daga yanayin zafin da k'irjinta yake yi. Murya a dashe ta ce "Ba ni da gata, ban kuma san inda zan fara nemo mahaifina ba, ko sunansa cikakke ba 'a sani ba, yanzu duk duniya ta shaida ni ba jinin D'an Borno bace. Mahaifiyar da ta kawo ni duniya bata damu da ni ba, na tabbata kuma dangin ka yanzu ba za su dinga min kallon jininsu ba, tun daga yau an fara sanar da ni matsayina." Hannu yasa kawai yana share mata hawaye, don duk kalmomin bakinsa sun d'auke tsaf, tabbas abin da ciwo ace ba'a san asalin mahaifinka ba. Kunnenta kawai ya dinga hurawa kafin cikin rawar murya ya ce "Ni zan zame miki gatanki, zan zame miki uwa uba miji duka. Zan shayar da ke duka farin cikin duniya fiye da wanda yake da uwa da uba a kusa." Ta k'ank'ameshi murya na rawa ta ce "Me yasa Ammi ba zata karb'eni a matsayin y'a ba, alhali ita ta samar da ni ta hanyar son zuciyarta." Baki yasa ya rufe nata bakin ruf ya dad'e a haka kafin ya d'ago cikin yanayin canzawar ido ya ce "Zata amsheki, har ma ta yi alfahari da zamowarki y'arta insha Allah." Jajayen idanunta ta d'ago tana kallonsa kafin cikin hawaye ta ce "Kaima ai ba nawa bane, tunda ina ji ka gayawa jama'a ta hanyar aure kawai zaka iya tona asirin Ammina, ka ga hakan yana nuni da cewa ba so na kake ba, ka aure ni ne don waccan hujjar kawai. Na tabbata tunda ka gama amfani da ni, ta hanyar tonuwar sirrin Ammina yanzu zaka sakeni, bak'in ciki na d'aya ka riga ka kusanceni, ka d'auke min martabata ta y'a mace, ga shi aurenmu ba matabbaci ba ne.." Da sauri ya katse mata sauran furucinta ta hanyar zuba mata nagartattun idanunwansa da suka rine suka zama ja lokaci guda, mafi munin furuci a kunnuwansa ya ji ta ce wai za su rabu, lamarin sai kace almara, a da tabbas soyayyarta ba ta game masa zuciya ba, amma tun bayan da ya d'ora idanunsa a kanta zuwansa Nigeria, ya tabbatar itace macen da yake muradi, itace macen da yake k'awata ta a zuciyarsa sai ga shi ta bayyanar masa a zahiri. A lokacin da ya kusanceta kuwa ya tabbatar ita ce mahad'in da gangar jikinsa ya dad'e yana nema, ta ko ina ta yi masa. Ita ce a koda yaushe yake jin sha'awarta tana game duka sassan jikinsa. So yake mata mara gauraye ko kad'an zallar so ne mai k'unshe da wata irin k'auna, mai yiwuwar fasaltuwa. Ya jata jikinsa ya rik'e gam, tamkar dai rabuwar ta su ce ta zo da gaske. Knocking d'in da ake bai saka ya saketa ba, saboda zallar samun nutsuwa da yake da d'umin da yake cikin fatarta mai d'auke da zafin zazzab'i kad'an.
Da kyar ya janye jikinsa yana manna mata kiss a kumatu sannan ya mik'e don bud'e k'ofar. Yana bud'ewa idanunsa suka fad'a cikin na Mahmah, da Nanna. Cikin tsananin takaici Sadiyan take wurginsa da wani irin kallo, kafin ta cije leb'en k'asan bakinta d'aya, ta mayar da kallonta a kan gadon da Hamda take, ta gefensa ta bi ta wuce ba tare da ta amsa Sannu da zuwan da yake mata ba, burinta ta je ta isar da sak'on da ta nad'o a ranta, da gaske ba zata amince Hammad ya cigaba da zama da Hamda a matsayin matarsa, ko da hakan na nufin rasa ta ta igiyar auren. Nanna kuwa na tsaye tana jifansa da murmushin mugunta, itama a shirye take da cusguna masa ta kowane fanni matuk'ar zai cigaba da zama da Hamda, yarinyar da take jin tsananin kishinta tun tana matsayin y'ar mijinta balle yanzu da ta zama kishiyarta, idan kuwa ya k'i tabbas zata fallasa sirrin da ya zama na sa shi da ita.. to wannan hanyar kawai take tunanin samun galaba a kansa, ya amince ya datse igiyoyin auren da suke tsakaninsu da Hamda!Jikar Nashe ce✍🏽
❤️❤️❤️❤️❤️🙏
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.