34

289 6 0
                                    

Cikin Tsoron lamarin na dinga girgiza kaina kafin na mik'e idanuna cikin na Kady da take min kallon shashasha "Ai shikkenan ki je idan kin yi shawara zaki nemo ni da kanki. Kawo wayarki na saka miki numberta" na mik'a mata wayar kasancewar lokacin wayar hannu ta d'an fara zaga gari. Ta daddanna ta saka min numberrta sannan ta rungumeni kad'an ta ce "Allah ya raba lafiya, ni fa farkon ganina da ke na zata ba kya jin hausa wallahi. Sam ba ki yi kama da y'an k'asata ba." Na jijjiga kai "kin canka daidai ba ni da kowa a Nigerian nan duk dangi suna jordan aure ne ya kawo ni nan." Ta ce "Ayya insha Allah yanzu kuwa Zan zame miki y'ar uwa in dai kin karbeni da mutunci." D'aga mata kai na yi kafin nace "Why not? Ina maraba da ke, ni ko sunanki ma ban sani ba muna ta surutu." Ta girgiza kai "Muna magana mai amfani zaki ce ba surutu ba, sunana Kadija amma an fi kira na da Kady." Na fad'a mata sunana nima ina tafiya ta rakani har bakin mota in da driver yake jirana.

Tun daga lokacin muka d'inke da Kady ta zame min abokiyar shawara, na ji dad'in had'uwa da ita k'warai da gaske. A hankali ta dinga tunzira zuciyata har na amince da abinda ta ce, muka fara shirin yarda za mu farwa Gadanga da zarar na haifi cikin jikina na yi arba'in zamu fara saka shi a tarko.
Duk da zuciyata tana rawa da tsoro akan amincewar ko rashinta. Tabbas na san ba namijin da zai k'i ya kusanceni a yarda Allah ya kyautata min halittata. Amma ina tsoron bayyana hakan da Gadanga mutumin da ya zamo daga cikin jinsin mutane miskilallu, ta ya zan janyo hankalinsa? Kada na je ya tona min asiri don haka na k'udundune shawarar Kady na saka ta a gefe na shiga neman mafita da kaina. Ba k'ok'arin da ba tayi ba akan na amince da batunta sai dai na ce mata wallahi ina tsoro. Ta gaji ta k'yaleni had'e da cewa idan kin shirya d'aukan cikin namijin ki sanar da ni." Na d'aga mata kai kawai.


__________

A duk shekara na kan zauna na yi kwalemar kayan bayarwa a d'akina, na kwashi kayan yara da yawa buhu guda da k'atuwar ghana must go, kuma duk sanda na tashi bayarwa masu yi mana hidimar gida nake bawa. Su yi ta godiya suna min addu'oi.

Wannan karon san da na had'a kayan sai na ji zuciyata tana son na bawa Buzu sabon mai gadin da aka kawo gidanmu. Shekararsa guda kenan kuma muna d'an d'asawa da shi saboda yawan kyauta da nake masa. Da na gama tattara kayan sai na sanya Najwa ta kirashi ya d'au kayan gaba d'aya idan ya tashi tafiya garinsu sai ya tafi musu da shi.

Da kirarin da ya saba min ya shigo falon. Cikin harahensu na buzanci "Idan ka ji Kiran Uwar larabawa alheri ne, wannan yaran da izinin ubangiji sai sun zame miki abin alfahari, farar mace mai farar zuciya. Na saki murmushi ina wasa da gashin Munira da take cinyata na ce "Buzu ka bari ka iya hausar kafin ka dinga Yi, ni wani abin ma idan ka fad'a bana ganeshi, tunda nima hausar ba wai ta isheni ba ne." Ya yi dariya kawai yana kallon kayan da suke zube a gabana. Na ce "Buzu kayana ne da na yara na had'a na ji kace kana aike garinku sai ka aika musu da shi." Bakinsa ya washe kafin ya ce "Kash ina ma Allah d'iyoyi mata ya bani da sun mori kaya, to tsiyar abin sai dai mutanen gari su mora. Yara na goma sha biyar daga iyayensu mata biyu amma kaf ba wacce ta tab'a haifa min mace duk da so na da haihuwar y'ar d'iya." Sak na yi ina kallonsa jin furucinsa kafin na ce "Kana nufin kaf zuri'arka maza ne?" Ya d'aga min kansa cike da tabbatarwa "Wallahi Hajjaju nake gaya miki kaf d'insu maza ne guda sha biyar da su masha Allah, haka zuri'ar mu take da wuya ki ga an haifi mace daga yayyena maza har mata kuwa, ina ga d'iyoyi biyu ne mata a cikinsu, shima daga tsatson wata k'anwata, San da aka haifesu ba kiga irin murnar da ahalinmu suka shiga ba. Da zarar kin je Habasha kika ce kina neman gidan Abu rijalun to za'a kai ki gidanmu. Tunda ba b'oyayyu ba ne mu muna da sarauta a garin." Na tsaya ina kallonsa baki na sake zuciyata da tunani iri-iri a cikinta. Ciki kuwa har da tunanin Allah ne ya kawo min buzu mai gadi don na samu d'a namiji daga tsatsonsa. Idan haka ne kuwa ya zama dole na yi wani abu kafin lokaci ya k'ure min. Na sallameshi ina masa godiya zuciyata cike da farin ciki. Shima ya fice cike da farin ciki.

Tun daga lokacin na gadarwa kaina zama na zurfafe bincike akan yarda zan samu Buzu mai gadi ya amince da buk'atata. Duk da ina k'yank'ayamin kasancewa da shi. Hankalina duk ya tafi akan tunanin yarda zan samu d'a namiji. Musamman ganin yarda Hammad ya girma kuma Komai Umar sai yace sai shi shine babba. Idan na kawo masa maganar Najwa ce babba sai yace ai Hammad shine namiji nan gaba ita kanta Najwan wa zai zame mata ba k'ani ba, musamman tazarar ta su ba yawa ba ce da ita." Ban yarda da shi ba gani nake son kansa ne kawai idan ya ga na yi fushi da shi sai ya tattara dukkan nutsuwarsa a kaina ya shiga k'okarin lallai sai ya fahimtar da ni su yara mata da kike gani da zarar ka aurar da su, sun bar k'ark'ashinka kenan sun koma k'ark'ashin kulawar mijinsa ta ya zan bawa Najwa damar kula da dukiyata idan ta saba da kud'i kuma ta k'i aure fa. San da suka gama secondary school ba yarda ban yi ba ya tura Najwa K'asar England karatu amma ya k'i bud'ar bakinsa sai ce min yayi dama Namji ce amma ba Zan tura mace wata k'asa karatu ba. Wannan kalami nasa yasa na yarda na amince ita mace bata da wani value a idon iyayenta maza. Ba su d'auketa komai ba. Hakan yasa na k'udirce a raina ko ta wace hanya sai nima na haifi namiji.

Kady ta fad'o min a rai don haka na shirya tsaf na ce Umar zan je gidan Kady. Yana kallona ransa a b'ace ya ce "Har ga Allah Sakna bana son huld'ar ki da Kady don dai ba yarda zan yi dake ne, ke ban isa na hanaki ba dama Sadiya ce na san ina ce mata ta daina kaza zata daina."
Murya a cunkushe ina jan tsaki na ce "Sadiya ka ce ita taga zata iya rayuwar gidadanci, ni rayuwa mai y'anci zan yi irin yarda na ga yarda ake yi a gidanmu, bata yarda zan zamewa miji kamar baiwa." Girgiza kai kawai ya yi duk da alamunsa sun nuna ya ji haushi amma ya shanye b'acin ransa, sau tari hakan ce take kasancewa bai isa ya ce min ga abinda yake so ba na bi, kullum ra'ayi na nake bi fiye da nasa. Na fice ina jinsa Yana cewa "Allah ya shirya min ke Sakna, son ki ne ya yi min yawa shi yasa nake kasa d'aukan mataki a kanki." Ni kad'ai na saki murmushi ni da kaina na San da damar son da yake min nake zabga masa rashin kirki shi kuma yake kasa hukunta ni ba irin Sadiya ba da take karb'ar hukuncinsa a koda yaushe.

Kady da murmushi ta tarbeni tana fad'in "Mhmd Mhmnn manyan mata ka ga ta Umar ba da kanki a sare. Mai tsoron cin amanar Umar." Murmushi na saki kawai ina zama na ce "Biko na zo kwana biyu na ga ba na ganinki." Kady ta girgiza kai "Ina kuwa za ki ganni a gidanki in je mijinki yana min wani gani-gani shi yasa na janye jikina da ke." Na gyara zama ina tab'e baki "Ni ba wannan ya kawoni ba, zuwa na yi akan zancenmu na kwanaki." Dariyar shak'iyanci ta yi sosai kafin tace "Kin ga uwar bari kenan wa ya gaya miki Borno gabas take ina jinki ya ake ciki?" fuska a had'e na ce "Ba fa waccan maganar ta kawo ni ba,
sam ba zan iya wannan kwamacalar ba, Buzu mai gadin mu na hango a yanzu shine nake ganin kamar zai cika min burina." Tsawon lokaci tana min wani irin bahagon kallo kafin ta ja ajiyar numfashi ta ce "Allah ya kyauta, amma wannan tunanin naki kamar ya gurb'ata ta ya zaki iya had'a jiki da mai gadi?" Na runtse ido jina jijjiaga kaina "Dole na kawar da maganr duk wata k'azanta kady, in dai burina zai cika. Haihuwar d'a namiji shine cika makin farin cikin rayuwata." Baki sake take kallona kafin tace "Mhmn, to yanzu ta ina ki ke tunanin za'a fara?"
Na gyara zama kafin na ce "Sai na gyarashi tukun, ya zama mai tsafta na kuma jik'ashi da Naira kafin na bijiromasa da buk'atata, amma fa ta hanyar aure ba zina ba..... sak'ek'e take kallona kafin ta ce "Aure kuma? Kamar yaya?" Na saki murmushi kafin na ce auren dai da kika sani mai suna aure." Tsaki ta ja ta ce "Shi kuma auren Umar d'in ki kaishi ina?"

Jikar Nashe

❤️❤️❤️❤️❤️🙏

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now