Follow me on ArewaBooks
https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e
Follow me on Wattpad
@Nazeefah38112
✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽
Tunda ya fara maganar tayi k'asa da kanta sai da taji yayi maganar neman iso wajen Iyayenta sannan ta d'ago tana masa wani irin duba
A tsorace take kallonsa, kasantuwar ba'a tab'a tareta da magana kwatankwacin wannan ba.
Taji zuciyarta na wani irin bugu kamar yarda dai hakan take faruwa ga tarin y'an mata, a karo na farko da saurayi ya taresu da kalmar Na gani Ina so."Kin amince min?" Ta jiyo maganarsa daga sama tamkar dirar mikiya. Da sauri ta d'aga kai, don bata da zab'in da ya zarta hakan, Wa take da shi bayan shi? Da zata ce bata amince masa ba?
Ta tabbata Allah ne ya kawo mata mafita a lokacin da ta kai kukanta garesa cikin sakankancewa da cewa Jallan ya amsa mata. Sai ga shi a cikin lokacin da bai gaza kwana biyu ba kacal Allah ya aiko mata da Zunnurain ya aureta, ashe dai ba zata bawa Yaya Hammad kunya ba, kamar yarda yace ya bata kwana bakwai, zata je masa da labari mai dad'i Samun Miji a gab'ar data dace.
"Kisa min digit d'inki" Ta sake jiyo maganarsa wannan karan ma a bazata. Da sauri ta kalli wayar hannunsa tana girgiza kai tare da cewa "Bani da waya." Ya kuwa dad'e da ido a bud'e bisa ga dukkan alamu tarin mamakinta ne yake nema ya karshi, a zamanin nan da waya ta zama ruwan dare ace zabgegegiyar budurwa kamarta da ta fito daga zabgegen gida bata da waya? Abin a jinjinawa lamarinta ne don kuwa yayi girman da ya kamata ya girgiza zuk'ata.
"Wasa kike amma?" Ya sake jefo mata tambayar, ta girgiza kai tana turo baki kafin tace "Da gaske bani da ita, bata yarda za'a yi had'uwar farko na jaka da wasa alhali ba ban san ko kai waye ba."
Ya jinjina kai had'e da sakin murmushi, "Shikkenan, na yarda dama kamila kamarki bai kamata aji zance akasin gaskiya a bakinta ba, zan dawo jibi da misalin takwas na dare, insha Allah zan taho miki da waya."Tamkar tace masa Ya barshi, sai dai ita kanta tana buk'atar rik'e wayar, kamar yarda taga k'awayenta na rik'ewa, Abbu ya tab'a siyo mata amma Ammi na kyalla ido ta k'wace ta, taji ciwon hakan a ranta, sai dai bata damu sosai ba, saboda ta san hakan ce take faruwa a duk sa'ilin da Ammin taga abu mai mahimmanci da zai sata nishad'i a rayuwa, sai ta san hanyar da tayi ta k'wace.
"Ki shiga gida beauty, naga a gajiye kike sai Allah ya dawo dani."
Murmushi ta d'an sakar masa kafin ta tura wangamemen gate d'in gidan nasu, ta d'aga masa hannu kamar yarda shima yayi waving d'inta.
Da shigarta Kamla da suke wasa a harabar gidan ta taho ta d'aneta da gudu, haka kawai jininsu yazo d'aya da yarinyar, kai gaba d'aya d'iyoyin Hammad ma suna sonta tamkar yarda take sonsu cikin tata zuciyar.
Peck ta bata a kumatu, a kunne kuma ta rad'a mata "My Kamlulu, dirar yaushe? Yaushe kuka dawo daga gidan Granny?" Kamla ta d'an cono baki had'e da cewa "Ni nafi son nan gidan, can ba dad'i shine Mom tace a dawo damu ita sai jibi zata dawo." Hamda taja hancinta had'e da cewa to Parrot wa ya tambayeki, ina Khairi? Da Abul khair? Tayi mata pointing b'angaren Didi da hannu, "Suna can suna cin wani abu wai zogale, nifa na kasa ci amma Sis Khairi tana taci wai dad'i ita da Dad nifa idan naci am sure I will vomit it." Ta fad'a tana kakarin amai "Please Anty Hamda will you cook noodles for me?" Hamda ta gyad'a mata kai, dai-dai lokacin da take tura k'ofar parlourn Didi.A baje ta gansu duka akan carpet sun yi Baja-baja da tarkacen b'awon gyad'a ga kwanon da suka ci zogale, shi kuma yana saman three seater yana danna waya.
Sallamar da tayi cikin sanyin murya yasa shi d'ago kai, idanunsa akansu ita da Kamla, sai ya sake ganin zahirin kamanninsa ashe da ba abinda ya gani.
Bayan ta gaida Didi ta gaisheshi, suma su Khairi suka gaisheta, ta amsa musu cike da kulawa, ta fara harhad'a plates d'in wajen, Khairi ta sa hannu tana tayata. Didi sai mita take "Baiwar Allah daga zuwanki zaki fara gyara waje, ai wallahi wanda ya aureki ya more mace, ba dai tsafta ba abinci kuwa idan aka ci naki kamar kunne zai tsinke, to ba dole na soki a
Cikin jikokina ba, mai kula da kai ai
Shine abin martabawa, ba wanda ya mayar da kai d'an iska ba, yanzu tunda nayiwa Hammad magana akan matarsa da taje ta rashe gindi ta zauna gidan iyayenta yake zaune nan yake ta cin magani ina ji ma har zagina yayi a zuciyarsa.."
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.