28

321 3 0
                                    

Cikin takaicin lamarin ta juya da sauri ta rurrufe ko ina na gidan sannan ta kashe kayan wuta. Tana tsaki ta ja trolley d'inta ta fice daga gidan.

Tun daga nesa Nanna take jifanta da wani irin kallo gabanta yana dukan tara-tara ganin yarda Hamdan ta fito ta yi wani azababben kyau fatar jikinta ta murje sosai asalin natural skin d'inta ta sake bayyana zallan kyanta game da laushi da santsin fata. Ta amince Hamdan number one ce a wajen kyan fata, don ko farin mutum ba zai gaya mata d'aukar ido ba. Sanin cewa tare yake da matarsa ya sa ta had'e fuskarta tamau tamkar bata tab'a dariya ba. Da kansa ya fita ya bud'e mata boot d'in motar ta cilla trolley d'inta a ciki. Idanu take so su had'a kawai amma ya fuske ya d'auke kansa don ya san muddin zai had'a ido da ita to komaima zai iya canjawa. Takaici ya sake kumeta wato sabida yana tare da matarsa yana tsoron b'acin ranta shi yasa ko kallon arziki ba zata samu daga gareshi ba? Ta ji kamar ta zunduma ihu ganin har ya shiga motar ya tayar bai damu da ya ce mata ta shiga ba. A zuciyarta ta ayyana tabbas auren mijin wata masifa ne. Ji yarda ya banzagatar da lamarinta da su kad'ai ne ta tabbata yarda yau ba sa azimin nan saboda tafiya sai ya kusanceta kafin su taho amma saboda munafunci jibi yarda ya yi shakulatun b'angaro da ita. Jikinta a sanyaye duk da fuskarta bata nuna karaya ba ta bud'e bayan motar ta shiga. Tana gyara Glass d'in da yake fuskarta. Idanunta cikin na Nanna da ta lura tana yi mata kallon mamaki. Ba k'aramin dauriya ta yi ba ta angije abinda yake ranta murya a cunkushe ta ce "Ina kwana Maman Kamla?" Nanna ta saki hucin b'acin rai kamar ba zata amsa ba sai kuma itama ta mayar mata a cunkushen "k'alau." Daga haka ta ja baki ta tsuke itama Hamdan gefen window ta mayar da kanta tana kallon kyau da tsarin garin Birmingham d'in. Shi kuwa ta cikin black glasses d'in da yake idanunsa yake k'arewa Hamda kallo shi kansa yana mamakin yarda jikinta ya sake murjewa ya yi kyau. Shi kad'ai yake murmushin ganin yarda take cika tana batsewa shi kansa ya yi mamakin yarda har ya iya basar da ita haka? Tabbas nan gaba akwai darun rigimar da zata sassauke masa idan suka kad'aita. K'okari yake kawai su had'a ido sai dai ta basar da lamarinsa, ko kallon inda yake bata sake yi ba ta ba banza ajiyarsa.

Har suka isa Airport d'in ba mai magana a cikjnsu kowa da tunanin da yake a zuciyarsa. Nanna kam kasa daurewa ta yi kafin su fita daga motar su je airport d'in ta ce "Ke kuma ina mijinki ya barki kika taho ko rakiya babu?" Da kyar Hamda ta had'iye abinda ya tsaya mata a wuya ta fice daga motar kawai ba tare da ta bawa Nanna amsa ba. Gaba d'aya ma haushin Hammad take ji idan banda munafunci me yasa har a lokacin ya kasa sanar da matar tasa ya aureta? Kada fa ya cuceta ya kaita y baro. Tunanin da ya sark'eta kenan ta shiga taune lips d'inta ba tare da ta shirya ba.

Ganin bata san yarda zata nufa ba, yasa dole ta ja tunga ta tsaya tana kallo sanda suka taho sai ta ga tamkar da gayya ma Nanna take sake shigewa jikinsa tana nannarkewa tsaki ta ja a fili har tana zabga musu harara ta cikin glass d'in da yake idonta. Har suka zo ta gefenta suka wuce Hammad ya sauke idanunta a kansa yana sakar mata murmushi kad'an. Ta kau da kanta ita kuma tana jifansa da harara.


_______________

Gaba d'aya Mahmah (Sadiya) cikin farin ciki take na dawowar Hammad ya warware bak'in k'ullin da waccan makirar matar ta k'ulla.

Lokacin ma tana aikin shirya musu abinci a kitchen.Umma Asma'u ta shigo fuskarta fal fara'a don yanzu sam bata da buri irin na tozartar Sakina. Musamman ganin yarda take k'ok'arin lalle sai ta had'a ta fad'a da d'an uwanta. Abinda ta yi mata ranar ba k'aramin tsaya mata ya yi a rai ba daga ita har Didi da kyar suka runtsa a daren ranar Didi juyi kad'an sai ta ce "Iyye Ba takka lamalin Umaru ya girgimama. To ba dani da a yi wannan itkantin ba babu matal da zata zo ta laba min kanku. A to Takina dai te dai ta ci kanta."

Asma'u ta dafa kafad'ar Sadiyan ta ce "Hope dai ko Abbu baki sanar da shi dawowar ta su ba, don haka waccan makirar matar zata iya wargaza shirinmu. Ko ba haka bama na fi son yarda ta sakankance d'in nan ta gansu bagatatan lamarin zai fi jirkita tunaninta." Sadiya ta saki murmushi kawai had'e da gigiza kai a fili ta ce "Allah yasa shi uban gayyar Abbun ya yarda, don jiya ban da na kai zuciya nesa tabbas da na bar gidannan. Daga fa ba masa nasiha akan duk abinda ta kawo masa dangane da maganar mutane ya fara tsananta bincike tukun kafin zartar da hukunci." Shikkenan ya dinga sakar min bak'ak'en maganganu har da min gorin da ma ai tunda ni zab'in Didi ce dole ta fi so na, shi yasa kuma kuka fi so na aka saka masa mata a gaba to shi haka yake son matarsa duk da munin halinta da muke gani shi baya gani ciki da banta kawai kyanta yake gani. Bai tab'a sakar min bak'aken maganganu ba kamar jiyan nan." Ta fad'a tana runtse idanunta har tana shirin yankar kanta da wuk'ar da take hannunta da sauri Asma'u ta rik'e hannunta "Me ye haka kike yi Sadiya, sai kin jiwa kan ki ciwo a banza a wofi? Ina hak'urin da kika had'iya na shekara da shekaru sai yanzu da komai yazo gangara zaki zubar da ladanki. Ki jure kwana kad'an ya rage ko nace awoyi kad'an." Sadiya ta share k'wallar da ta sake kwaranyo mata tana sakin murmushin dole. Ita kanta ta san hak'kkinta kad'ai ba zai bar Sakina ta zauna lafiya ba don ta d'au tsawon shekaru tana cuta ta zahiri da ta bad'ini. Asma'u ta cigaba da kwantar mata da hankali har sai da ta tabbatar ta samu nutsuwa tukun na ta fita daga sasan nata.


Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now