14

590 14 3
                                    

Follow me on ArewaBooks

@nazeefah

https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e

On Wattpad
@Nazeefah381

14
____________________________________

✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽

Ido biyu suka yi da Mahmah da take shirin shiga duba Hammad d'in, suka shiga kallon-kallo kowa da abinda yake rayawa a ransa, musamman Mahmah da haka kawai gabanta ya yanke ya fad'i.
Ammi ta d'an saki yak'en murmushi don bata son Mahmahn ta zargi komai a ranta, duk da hakan ma bata tsira ba, don Sadiya Ta san tabbas ba wani dalili Sakina ba zata sakar mata murmushi ba, yarda ta tsaneta har kowa ya fuskanci hakan. Ga mamakinta sai ji tayi Sakinan ta ce "Ya kuma mai jiki? To Allah ya tsare ya sake kiyaye gaba, ai ma an auna arziki." Mahmah ta d'an yi murmushi kawai had'e da furta Ameen tana shigewa cikin sashennasa, haka kawai zuciyarta ta k'i yarda da lamarin Sakinan. Tana shigewa Sakina ta saki tsaki murya can k'asa ta ce "Algunguma, da ni kike zancen, shegiya bak'a kawai kin zo kin mamaye gida."
Wayarta da ta shigo ne yasa ta saurin shigewa b'angarenta, ganin Kady ke kiranta. "Sakna mu godewa Allah yara dai sun yi kasuwa, Senator Aruwa na son       Shi kuma D'an majalissar birni da kewaye yana son.               Wata irin shewa Sakna ta saka, don tsananin farin ciki bata san sanda ta dinga k'wala musu kira ba.

Su d'inma a sukwane suka fito samun labarin ya saka su rungumar juna suna shewa da gaske abin ya zo musu tamkar almara a lokacin da suka cire rai.
Ammi ta gargad'esu da jan bakinsu su tsuke gudun y'an hana ruwa gudu, ko zancen za suyi, sai dai suje gidan Kady, ta kalli Muneerah kafin ta ce "Saura kuma don ubanki na ji labarin ya fita, yanzu ke kika rage min na samo miki wani gwaskan d'an kasuwan ko b'arawon gwamnati, don ta waccan banzar bana tata kowa ma ya aureta ba matsala ta bace."
Turus y'an uwan suka yi, zuk'atansu cike da tambayoyi game da dalilin da yasa Ammin ta tsani y'ar uwarsu, kullum abin yana damunsu ganin dai Ammin bata son yawan zancen yasa suka tattara suka watsar da lamarin.

Wannan karan dai kam sai da Munira tayi k'uru ta ce "Wai Ammi me Hamda tayi miki kika tsaneta har haka? Alhali Ko mu da kike nunawa k'auna ba ma yi miki biyayyar da Hamda take yi miki."
Wani kallo Ammin ta jefeta da shi kafin ta ce "To uwata naji duka tukunna kafin na sanar miki, wallahi duk ranar da kika kuskura kika sake yi min makamanciyar wannan tambayar ranar na lahira ma sai ya fiki jin dad'i kinibabba kawai." Sunkuyar da kai Kawai Muneerat tayi kafin ta mik'e ta shige bedroom d'insu da sauri. Tayi alk'awarin sai ta binciko dalilin da yasa ake yiwa y'ar uwarta wannan tsana ta ba gaira ba sabar, sam bata yarda da dalilin wai don an haifeta a mace bane, akwai dai wani b'oyayyen lamarin da dole zata bincikoshi. Ammi ta bita da banzan kallo sai taji ma duk farin cikin da take ciki ya b'ace b'at, saboda wannan zancen da Munira ta tsillo mata na waccan bak'ar yarinyar mai kalar mutanen Habasha. Ta ja tsaki kawai had'e da mik'ewa.


____________________________________

Zunnuraini, bayan kwana hud'u da had'uwarsu ya zo, cikin shigarsa ta alfarma sai zabga k'amshin turaren Miyaki yake yana asalin.

Suna zaune gaba d'aya a parlourn Didi har da Nanna da Hammad da yaransu sai Hamda da take gefe take tsakurar tuwon kamar bata so, haka kawai yau ta tashi da yanayi na fad'uwar gaba da b'acin rai shi yasa take zaune a gefe, duk da surutun da Kamla take damunta da shi bai sa ta cire damuwar da take ranta ba.

Sallamar yaron da yake musu sharar harabar waje ne ya dawo da ita cikin duniyar tunanin da ya zurfafa jin yace "Wai ana sallama da Hamda."

Da sauri ta kai idonta wajen da Hammad yake, sai dai ko alamar yaji zancen bai yi ba, gaba d'aya hankalinsa yana kan Abulkhairi da suke buga TV game, a gark'amemiyar t.v d'in da take parlourn.

Didi tsaki ta ja tana zabga mata harara ta ce "Ji min y'ar banza, shin baki ji ana sallama da ke bane?" Jikinta a salub'e ta mik'e ra shige d'aki, Kamla na binta a baya, sai yanzu ta gane dalilin b'acin ranta, da fad'uwar gaba, duk sabida a karo na farko saurayi yazo zance wajenta. Ba abinda ta saka a fuskarta sai ma zumbulelen Hijabin da ta saka da ya kai mata har idon sawu, sannan ta rik'e hannun Kamla suka fice, ta k'asan Ido Hammad yake kallonta, ya saki ajiyar zuciya, a ransa yana mata fatan dacewa da abokin zama Na gari don shine kad'ai abinda Zai saka ta samu peace of mind Ta huta da gallababbiyar Uwarta.

A can bakin gate ta tarar da shi saman bonnet d'in motarsa yana danna waya hasken farin wata ya haske kyakkyawar madaidaiciyar fuskarsa, har a zuciyarta take jin Zunnuraini ya kwanta mata kuma zata iya zaman aure da shi. Don ita dai bata hango makusa tattare da zubin halittarsa ba.

Cikin nutsuwa take takun, hannunta rik'e dana Kamla har suka isa inda yake. Ya d'ago fuskarsa cikin murmushi yana tsareta da idanunsa gaba d'aya yarinyat ta gama tafiya da imaninsa tun ranar da yayi tozali da ita duk da bai ga zubin halittarta ba ta fuska kam tayi masa hundred percent irin matar da yake so, mai matsakaicin kyau ba mai manyan kyau ba.

Tsawon lokaci suka d'auka suna hira kafin ya sake sanar da ita ainahin wanene shi da sunan mahaifinsa da komai, sai dai gabanta ya fad'i jin cewa yana da mata har da yara biyu. Ganin ta firgita ya saki murmushi kafin ya ce "Kada fa ki damu, matata bata da matsala kuma ba gida d'aya zan had'aku ba." Murmushi ta d'anyi lokaci guda kuma yana sake burgeta ganin ba halinsu d'aya da sauran maza ba masu kushe matansu na gida a yayin da suke neman aure madadin haka ma shi yabon tashi matar yake, nan take zuciyarta ta sake amincewa da shi hundred percent.

Da zai tafi ya mik'a mata sabuwar waya dal a hannunta, ganin ta k'i karb'a sai ya mik'awa Kamla had'e da fad'in ya sunan k'anwar tamu don da gani babu tambaya k'anwarmu ce ga kama nan b'aro-b'aro. Hamda murmushi ta saki kafin tace Baka canka daidai ba, Niece d'ina ce ba k'anwa ba." cikin mamaki ya ce "Ai kuwa wannan ko y'ar waye tabbas mu ya haifawa y'a don kamar babu banbanci. Masha Allah, Idan kin gama shawarar please ki fad'a a gida Zan turo magabatana so samu ne ma ki azimi a gida na, amma na san yayi wuri don haka zan barshi Immediately after Sallah Insha Allah." Da sauri ta shige Gida cikin matsananciyar kunya.

Da murna Didi ta karb'i kwalin wayar tana cewa "Masha Allah, haka muke so kab'akin arziki, kice saurayin naki mai d'an maik'o ne? Har da dalleliyar waya haka, gaya min waye ubansa anan garin? Burina ki auri wanda uwarki zuciyarta zata kusa bugawa ta mutu kowa ma ya huta, Allah yasa dai Ubansa yafi d'angote kud'i."

Wani tsaki Hammad ya ja kafin ya ce "Ai duk halinku d'aya da Ammin shegen son abin duniya, madadin kiyi mata fatan samun mutumin k'warai sai ki wani ce Allah yasa Ubansa yafi d'angote kud'i, mhmn don dai baki san arzikin d'angoten bane, ke kuma shashasha ki tsaya daka tatata kada ki samo mutumin arziki ki tsaya neman mai dukiya
Ba mai zuciya ba."

Sak'ek'e Didi tayi tana kallonsa baki a mele kafin tace "Kaji min mutum banda kai d'in wanta ne da sai nace bak'in ciki da hassada kake mata, waye yak'i dad'i a duniya inace ko kai yanzu d'iyar d'angote Ta ce zata aureka murna zaka yi."
Bai bi ta kanta ba ya fice don ma ya cusa mata takaici har da jan hannun Nanna kamar zai mayar da ita ciki, duk da Nannan na turjewa Didi ta ce "Jarababbe, jarabar ta motsa ai ni yanzu lamarinku tsoro yake bani, mata ki bi ki nanik'ewa miji, Allah dai ya kyauta." Dariya kawai suka fita suna yi. Hamda ma dariyar take kafin ta shige d'aki tana dafe da k'irjinta saboda tsananin bugun da yake mata.


__________________________

Ciwon cikin da ya murd'awa Muneerah cikin dare da misalin Sha biyun dare ne ya sata fitowa daga bedroom d'insu don ta samo magani a first aid box da yake d'akin Amminsu.

Kasancewar dare ne kafin ta murd'a k'ofar d'akin ta ji sautin muryar Ammin da alama waya take jin tana kiran sunan Hamda yasa ta dakata da bud'e k'ofar ta kara kanta sosai a jikin k'ofar sai taji Ammin ta cigaba da cewa "Kin san sarai ta yarda aka samar da yarinyar nan? Ta yaya kike tunanin hankalina zai kwanta idan ban kawar da ita ba, duk ranar da Umar ya san maganar nan na ha'intarsa da nayi ha'inci mai muni ina tabbatar miki Mami ba zan kwana da igiyar aurensa ba, don Allah Mami ki nemar min mafita wallahi kaina ya k'ulle, na rasa yarda zan yi, don na lura yaron nan bai k'i ya fallasa sirrin nan ba ko da shi zai kwana a ciki, na tabbata akwai abinda Hammad ya taka shirunsa ba yana nufin ya hak'ura bane musamman da na san ya kwana da sanin cewa ni na turo mutanennan suka yi masa duka cikin dare.......

Wata irin hajijiyace ta fara d'iban Munirat ji da ganinta duk suka d'auke na wuncin gadi, a take ta kurma wani uban ihu........✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

Jikar Nashe//

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now