KUDIRINA

807 31 5
                                    

*K'UDIRINA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Dedicated to Maryamerh Abdulrahman* (Kwaiseh)

           *19*

Tana shiga gida ba dad'ewa, Bashir ya shigo gidan cikin yanayin damuwa. Duban Islam yayi cikin natsuwa ya fara mata magana.

"Islam dama ba wani abu bane, Muhammad ne ya d'an samu accidents."

Cikin rud'ewa take tambayarshi.

"To yanzu ina Yayan yake?"
Kafin kace mai, har ta wanke fuskanta da hawaye.

"Ki natsu Islam ai yana asibiti, jikin nashi da sauk'i."

"Muje ka kaini in ganshi."

Gaba d'aya duk ta gama rud'ewa.

Tare suka fita, sun isa asibitin, tafe yake tana biye dashi, ji take inama ta san d'akin da yake ciki da yanzu ta manta ta isa wurinshi. Suna shiga da sauri ta isa gadon da yake kwance. Dubanshi tayi taga yanda yake a kwance idonshi a rufe sai maida numfashi yake.  Kifa kanta tayi  a jikinshi tana kuka.  yanayin kukan da take cike da tashin hankali.

"Yaya ka tashi! Yaya kada ka tafi ka barni, zan shiga wani hali. Yaya kai kad'ai gareni. Ban san kowa ba, kaine komai nawa Yaya. Allah ka dubeni ka tausaya min kaba ma Yayana lafiya."

K'ara fashewa tayi da kuka mai ratsa zuciya.

Cikin tausayinta Bashir yace.

"Islam kiyi hak'uri zai tashi, ki daina kukan haka ya isa."

"Yaya Bashir dole nayi kuka, Yaya Muhammad ne kad'ai komai nawa bani da kowa. Dashi nake rayuwa, idona bai saba ganin kowa ba sai shi."

Tausayinta ne ya k'ara ratsashi. Kallonta kawai yake ya rasa mai zai ce mata.

Doctor ne ya shigo. Duba Yaya Muhammad yayi, kana ya juyo ya dubi Bashir dake tsaye.

"Yana buk'atar jini saboda ya zubar da jini a raunin da yaji, zamu so a k'ara mashi koda Leda d'aya ne."

"Doctor ba damuwa, a d'ibi nawa idan har zai yi dai-dai da nashi."

Gaba d'aya suka fita, Islam sai faman share hawaye take.

An gwada jinin Bashir bai yi dai-dai da nashi ba. Tunani Bashir yayi ta inda za a samu jinin da za a sa mashi.

"Yanzu Islam ya zamuyi? Jinina baiyi dai-dai da nashi ba."

"A duba nawa idan zaiyi a sa mashi."

"Haba Islam kina mace k'warin mai gareki da za a d'ibi jininki?"

Cikin damuwa, ga hawaye dake zubar mata a ido tace.

"Idan har jinina zai mashi na yarda a d'iba a sa mashi, mata nawa ne aka d'ibi jininsu? Jinina nefa shi. Dan Allah Ku duba idan zaiyi Ku saka mashi koda leda biyar yake da buk'ata a d'iba asa mashi."

Bashir ya fara magana cikin kulawa.

"Islam ki bari in dubo wasu abokanmu suzo a gwada aga ko zaiyi."

"A'a! Kawai Ku duba nawa, kwance fa yake yana buk'atan taimako,  yaushe za a zauna ana 'bata lokaci."

Kuka ta saka masu. Dole aka duba nata, cikin hukuncin Allah sai gashi yayi dai-dai da nashi. Haka tasa aka d'ibi jininta. Saida taga ansa mashi sannan hankalinta ya kwanta.

Ranar Islam tak'i matsawa ko ina tana tare dashi, sallah kad'ai ya tadata a wurin, koda Bashir yaga goman dare yayi ba yanda baiyi da ita ba akan ta koma gida amma tak'i tafiya. Dole tasa ya hak'ura ya tafi ya barta a nan ta kwana dashi. Tana nan zaune wanda ya kad'e Yaya Muhammad ya shigo. Gaidashi tayi ya tambayeta.

"Ya mai jikin?"
Ta bashi amsa cikin dasashshiyar muryarta daya disashe saboda kuka.
"Da sauk'i har yanzu barci yake yi."

"Kiyi hak'uri kukan ya isa hakanan. Nima ba a son raina na bigeshi ba. Ban san da shigowarshi ba."

"Kada ka damu tsautsayi ne ai, haka Allah ya hukunta."

Bai jima ba ya mata sallama ya tafi.

Tunda Islam ta zauna nan idonta ke kanshi, dan ta kasa rufe idon nata bare har tayi barci. Burinta kawai taga ya farka. Gashi sun mashi allura ne na barci, yanda zai samu hutu sosai.

*** *** *** *** *** *** *** ***
Naseem ne ya shigo d'akin Salim dake zaune yana karatun Qur'ani. Cikin girmamawa yace mashi.

"Yaya Salim kazo Dad na kiranka."

Ba tare da ya d'ago ya kalleshi ba ya bashi amsa.

"Gani nan zuwa."

Fita yayi dan fad'a ma Dad sak'onshi.

Mik'ewa yayi ya tafi kiran da Dad yake mashi.

Har k'asa ya duk'a cikin girmamawa yace.

"Gani Dad."

Gyara zamanshi Dad yayi ya dubeshi.

"Salim ya maganarka ne da Farida 'yar wajan Alh Isma'il?"

"Dad bata cikin tsarin rayuwata, shiyasa ma Bambi ta kanta ba."

"Ni kake fad'a ma haka? Ina umurtarka da kaje Ku sasanta da ita. Dan naga ya kamata a maka aure ko zaka yi hankali."

"Haba Dad ka ta'ba ganin a za'ba ma namiji wacce zai aura? Ko  kuma an tirsasashi akan auran dole? Ai an wuce wannan zamanin. A barni in nemo kalar tsarina da kaina."

Cikin 'bacin rai da fad'a Dad yake duban Salim.

"Yanzu Salim har ka kai matsayin da zan fad'a maka magana ba zaka ji ba?"

"No Dad! Ba haka bane. Kawai so nake ka fahimta ba kowace mace take birgeni ba, sai na duba wadda tsarina da nata ya zama d'aya. Wannan da kake maganar ku had'ani da ita, yaushe tarbiya ta shigeta? Wanda k'arya da son a san su waye ya Riga ya shigesu. Ku barni na za'bi macen aure da kaina."

Saboda takaici Dad ya rasa mai zaice mashi.

Mom ce ta dubi Dad tare da cewa.

"Ka barni dashi zamuyi magana. Tashi ka tafi ka bamu wuri."

Ta bishi da harara. Mik'ewa yayi ya bar d'akin, garden ya wuce ya zauna iskar wurin na hurashi. Damuwa ta mashi yawa. Yana so yaga iyayanshi sun canza akan tafarkin da suke kai. Meyasa suke nema su rink'a shiga cikin rayuwarshi ne haka? Mai yasa suke d'aukana k'aramin yaro? Shiru kawai yayi yana tunanin rayuwa.

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now