'KUDIRINA Page 45

80 10 0
                                    

*KUDIRINA*

       ®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

       ©
*EASHA MD*

*Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)

      *45*

  *Wattpad: Ayshatmadu*

'Kwala ma Karime kira tayi tare da umurtarta data kira duka ma'aikatan gidan. Fita tayi dan zuwa kiransu

Muhammad kam gaba d'aya ya gama tsorata dasu, du'kun'kune kanshi yayi cikin pillow dake kan kujera.

Le'kensu kawai yake dan baya son ya had'a ido dasu.

Gaba d'aya sai gasu sun shigo, samun wuri suka yi suka zauna cikin girmamawa

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Gaba d'aya sai gasu sun shigo, samun wuri suka yi suka zauna cikin girmamawa.

Magana ta fara yi cikin damuwa.

"Yau zaku bar gidan nan, saboda masu wurin suna da bu'katar wurin, ku tashi kuje ku had'a duk wani abu da kuka san naku ne, nima yau zan bar gidan."

Dukansu ba 'karamin tashin hankali suka shiga ba daji bayanin Mommy Amina.

Suna mai mamakin wad'annan wane irin mutane ne haka?

Cikin alhini da jimami suka amsa mata tare da mi'kewa jiki ba 'kwari suka fita d'akin dan sun kasa magana ma.

Itama mi'kewa tayi dan shiga ciki, da sauri Muhammad yabi bayanta ri'ke da ita suka 'karasa d'akin.

Had'a masu kayansu ta fara yi cikin akwatuna.

Saida ta gama tsaf kana ta fito dasu palour, duk da kayan data siya na baby ta had'o ta fito dasu, sai 'yankunnayenta da kud'ad'en da yake aje mata a gida, duk ta zuba su cikin wani jakar.

Baba Salisu yace.

"Iya abinda muke bu'katar ki fita dasu a cikin gidannan. Komi da kika sani yanzu ya zama namu dan bamu yarda ko mota ki tafi dashi ba."

Dur'kushewa tayi a nan ta fashe da kuka mai tsima zuciya.

Dur'kushewa tayi a nan ta fashe da kuka mai tsima zuciya

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Magana ya 'kara yi.

"Au kuka ma kike? To ko kukan jini zaki yi ko na mutuwa kada kiyi tunanin zamu tausaya maki. Dole ne ki bar gidan nan."

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now