K'UDIRINA page 63

308 22 6
                                    

*K'UDIRINA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)

      *63*

*Wattpad: Ayshatmadu*

Zaune suke a harabar gidan suna fira cikin annashuwa.

Dubanta yayi kana yace.

"Islam ya ake ciki ne kin san ni ba yaro bane da zanzo aita soyayya a waje, magana d'aya nazo muyi ina son ayi maganar aure."

Du'kar da kanta tayi tana sauraranshi.

"Kinyi shiru ko ba zaki aureni ba?"

Cikin sanyin magana tace.

"A'a in dai ka shirya d'in ka turo zan fad'a ma Yayana."

Cikin farin ciki yace.

"Insha Allah zaki jini cikin satin nan."

Sun dad'e suna fira sannan ya tafi cikin farin ciki da jin dad'i yana mai ro'kon Allah daya cika mashi burinshi na mallaka mashi Islam.

*** ***
Salim ne zaune gaban Dad in banda fad'a ba abinda yake mashi, ya shiga ta nan ya fita ta can.

"Salim ka bani mamaki, wai mai ka d'aukeni ne da baka d'aukana da muhimmanci? Aure dai ni zani nema ko to ba zani ba, ba hannuna a cikin maganar neman aurenka."

Duk'awa yayi kan k'afafunshi biyu ba tare daya ankare ba yaji saukan hawaye. Cikin rawar murya kamar mai kuka yace.

"Dad kada ka cutar dani zan iya rasa rayuwata idan har ban auri Islam ba, ina sonta da yawa."

Cikin tashin hankali da tafa hannu Mommy tace.

"Innalillahi! Shikenan ta asirceka wanda har baka ganin kowa sai ita, yanzu zaka iya rasa rayuwarka a kan mace?"

"Mommy ku taimaka min, yanzu maganar da nake daku tana so in tura shima Yayanta haka."

Shiru suka yi suna k'are mashi kallo. Dad ya dubi Mommy yace.

"Yanzu miye abin yi? Dan bana k'aunar yarinyar nan, hakanan naji bata min ba."

Mommy tace.

"Bashi yaji ya gani ba, mu barshi ya aureta d'in duniya ta hukuntashi da kanta, mai zaka yi yarinyar da ba k'aruwa zaka yi da ita ba sai dai ita ta k'aru da kai?"

Cikin nuna damuwa yace.

"Mommy bana son kina irin maganar nan, ni dai amincewarku da albarkarku nake nema."

Tsura masu idanu yayi dan jin mai zasu ce.

Gyara zama Daddy yayi had'i da cewa.

"Shikenan za aje nema maka auranta, amma ka sani bana son in rin'ka ganin yarinyar kaje can ka k'arata kai da ita."

Hakan ba k'aramin dad'i yayi mashi ba.

Da sauri Mommy tace.

"Ban yarda ba.."

Cikin sauri ya dubeta.

"Ban yarda ba, yanzu ma da muke tare dashi ta asirceshi ina kuma da mun bar mata shi gaba d'aya. A nan gidan nake so ta zauna in rin'ka kula da duk wani motsinsu."

"To amma kuma Mommy gidana dana gina inyi yaya dashi?"

"Ka barshi yayi ta zama a haka har sai sanda na mula na k'yaleka ka zauna can, ko kuma idan ka auri wadda muke so."

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now