*K'UDIRINA*®
*NAGARTA WRITER'S
ASSOCIATION*
©
EASHA MD*Dedicated to Maryamerh Abdulrahman (kwaiseh)
. *39*
"Goggo inafa ta shirin tafiya jigawa zuwa jibi."
"Au har tafiyar ta tashi kenan? Ya maganar zuwa nijar d'in?"
Ta fad'a tana mai kallonshi dan jin amsar da zai bata.
Cikin du'kar da kai ya furta.
"Yanzu dai ba maganar zuwa nijar a cikin tsarina sai dai ko nan gaba."
"Haba saboda mai kuma zaka ce ka fasa zuwa"
"Nima dai ban san dalili ba, na dai ji tafiyar ta fita a raina ba yanzu zani ba."
Cikin farin ciki da jin maganarshi tace.
"To ai shikenan, dama kaine ka nace sai kaje, wad'annan mutanan ba sonka suke ba, tunda kake rayuwarka basu ta'ba zuwa inda kake ba."
Ba tare daya bata amsar maganarta ba ya furta.
"Ni zan koma akwai abinda zanyi a wani."
"To shikenan Allah ya taimaka yayi albarka."
Cikin mamaki da addu'ar da bata ta'ba mashi ba tunda yake a rayuwarsa ya furta.
"Amin Goggo."
Tare dasa kai ya fita.
Wani shu'umin murmushi ta furta lokacin daya fita daga gidan, tare da furta.
"Haba yaro! Dani kake magana, ai ba zan ta'ba barinka ka ziyarci dangin uwarka ba. Muna nan tare da kai dukiyarka tamu ce."
Dariya ta saki ta koma cikin gidan ranta fes take ji dan jin maganin data mashi ya kamashi.
Kamar yanda ya fad'a yaje garin jigawa duk ya zaga danginshi tare da cikasu da abin arzi'ki.
Zama suke cikin kwanciyar hankali, idan kaga yanayin damuwarsu suna tare dasu Goggo.
A haka suka je garin cairo dan gaidasu, sunji dad'in ganin d'iyar tasu cikin kwanciyar hankali, sun rasa inda zasu sasu dan murna.
Muhammad ganin inda ake sonshi yasa ya saki jikinshi cikinsu.
Satinsu d'aya a can suka dawo 'kasa nigeria tare da kewar danginta.
Tunda ta dawo ganin yanda ta rabu dasu lafiya yasa kullum cikin waya take dasu suna mai gaisawa.
Cikin hukuncin Allah arzi'kin Farouk sai 'kara bun'kasa yake, ya zama babban mutum, taimako bai fasa yi ba, kullum cikin taimaka ma mabu'kata yake wanda suke cikin farin ciki. Duk iya dukiyar da zai bada bai jin komai a ranshi sai farin ciki.
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.