*K'UDIRINA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)
*50*
*Wattpad: Ayshatmadu*
"Ganin ba inda zai bar Islam, haka yake tafiya da ita wurin sana'arshi. Duk rana zafi da sanyi kansu yake 'karewa.
Al'amarin dake dagula mashi lissafi da damuwa a koyaushe karatunshi, ya kasance yana da son karatu, a kullum ya kan zama yayi ta rusa kuka. Islam baiwar Allah sai dai ta bishi da kallo, idan ta kasa jurewa itama ta saki kukan.
Da yaga tana yi zaiyi 'ko'karin ganin ya danne nashi, daga baya daina kukan yake a gabanta, dan ya tsani d'igon hawaye a tare da ita.
D'igon hawayenta d'aya yana sashi shiga damuwa sosai, yarinya ce wadda ta taso ta bud'e idonta dashi, wanda shine ya zame mata iyayen data rasa, wadda a kullum take kiranshi da Babana.
Ganin ba zai iya jure zama ba karatun boko ba, yana zaune ya yanke ma kanshi hukuncin yanda zaiyi da Islam.
Da haka ya bar abin a zuciyarshi, sai dai fa daya tuna inda yake tunanin kaita, gaba d'aya sai yaji hankalinshi ya tashi, sai dai yayi ta girgiza kai shi kad'ai.
Ji yake ba zai iya yin abinda yake tunanin zai aikata ba, ba yanda zaiyi haka yaci gaba da rainonta suna fita tare d'in, sai dai fa daya tuna karatunshi sai yaji hankalinshi ya tashi, ya zaiyi da amanarshi? Dole ya zauna yaci gaba da rainonta a haka.
Cikin hukuncin Allah, sana'arshi tana kar'buwa, . yayin da yake samun cinikin sosai, baya damuwa da d'ari biyar d'in da a kullum yake cirewa yana adanawa, tunda dama ba duka kud'in yasa ba a jalin nashi, dan 'ko'karinshi ya samu da shekara tayi ya biya masu kud'in haya.
Haka kullum yake samu yana aje kud'in.
Ya kuma je ya samu mai gidan akan yana son ya rage mashi kud'in haya, saboda baida 'karfin biya, duk bai 'boye mashi komai nasu ba.
Ba 'karamin tausaya mashi yayi ba yace.
"Muhammad na tausaya maku halin da kuka shiga, daga ganin yanayin jikinka da suturarka, shi zai tabbatar da kai daga gidan manya ka fito. Dan haka na rage maka dubu goma."
Sosai Muhammad ya nuna farin cikinshi, ya mashi godiya sosai.
In dai dama ka tsaya ma Allah, to tabbas shima zai tsaya maka.
*** ***
Bayan shekara biyu Muhammad ya kasa jure rashin zuwanshi makaranta, wannan tunanin ita ta 'kara dawo mashi, duban Islam yayi da take ta wasa tana surutanta yace."Islam! Ina so na kaiki wani wuri da zaki samu gata da ilimi a can. Kuma ba zaki rin'ka zama da yunwa ba."
Zum'buro baki tayi tace.
"Yaya ba inda zani in barka."
Sai ga hawaye ya gangaro mata, da sauri ya jawota ya fara share mata hawayen dake zuba a idanunta yace.
"Shikenan ya isa ba sai kinyi kuka ba, ina nan tare dake har 'karshen rayuwata."
Saida ya tabbatar data yi shiru kana ya 'kyaleta taci gaba da wasanta.
Ciki ya shige ya kasa jurewa, ina zai kai Islam ya samu yayi karatunshi? Kuka ya saki mai 'karfi, kuka yake sosai harda shashshe'ka.
Shigowa tayi ta sameshi yana kuka, jawo hannunshi tayi, tasa hannunta tana share mashi hawayen tace.
"Waye ya bigeka? Ka fad'a min waye ya bigeka?"
Murmushi ya sakan mata kana yace.
"Islam ke amanata ce, iyayenmu sun mutu sun bar min ke, bana so inga wani abu ya sameki, Islam na san ba fahimtata kike sosai ba, baki da wayan da zaki fahimci abinda nake nufi. Islam ina so in koma makaranta amma ban san inda zan ajeki ba, shine na yanke shawarar in kaiki gidan marayu ki zauna na d'an wani lokaci, da zarar na gama secondary ko kafin in gama zanje in d'aukoki."
YOU ARE READING
K'UDIRINA
أدب الهواةLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.