'KUDIRINA Page 47

107 11 2
                                    

*KUDIRINA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)

*47*

*Wattpad: Ayshatmadu*

Yarinyar kamar ta san halin da take ciki, har yanzu sai barcinta take duk wannan hayaniya ta Muhammad da yake yi baisa ta tashi ba.

Har yamma ana zaman makoki wasu kuma na zuwa dan yi masu gaisuwa.

Nan Muhammad ya 'kara rikice masu shifa bai son zaman makokin nan da za ayi, kowa ya tafi. Mallam Musa ne ya fara lalla'bashi yace.

"Zaman makokin nan ne kawai damuwarka?"

Cikin kuka yace.

"Eh bana son ganin kowa a gidan."

Cikin 'bacin rai Baba Salisu ya fara mashi fad'a.

"Mai ka d'auki mutane ne? Yanzu baka da gatan da zaka yi abinda ranka ke so, domin kuwa yanzu kai maraya ne. Amma tunda haka ka za'ba munji yanzu kowa zai kama gabanshi, dama muna da abin yi."

Haka ya fita gaba d'aya ya sallami kowa dake 'kofar gidan, sannan ya dawo ciki ya sallami matan dake ciki.

Kallonshi ne ya koma kan Muhammad.

"To yanzu haka ya maka ko? Mu zamu wuce Allah ya baka ha'kurin rashinsu, ai nayi mamakinki Goggo kina wurin nan yaron nan keta tsula tsiyarshi baki d'ad'd'aura mashi mari ba."

Cikin ta'be baki tace.

"Niko mai zance mashi bare yaji dad'in maido min magana, tunda tun bai kai haka ba ba tsorona yake ji ba."

"To Mallam Musa mu zamu wuce."

"To Alhaji mun gode."

Haka kowa ya tafi ya barsu su kad'ai. Mallam Musa yafi 'karfin awa d'aya yana lallashinshi, kana yace ma matarshi tazo su tafi gida tunda ga Karime zata kula da yarinyar.

Mi'kewa yayi tare da cema Karime

"Bari inje in siyo ma yarinyar nan madara kada ta tashi ba abinda zata ci."

Hannu ta mi'ka mashi gami da cewa.

"To mi'kota kaje ka dawo."

"A'a ba zan baki ita ba, ita amana ce a gareni, kamar Mommy ta san zata rasu, a kullum tana fad'a min idan na haihu ka kula da 'kanwarka. Kullum firarta kenan a 'yan cikin kwanakin nan, jiya ma firar da tayi ta min kenan."

Ya idasa maganar yana mai share hawayen daya zubo mashi da duka hannayenshi biyu.

Ya idasa maganar yana mai share hawayen daya zubo mashi da duka hannayenshi biyu

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Ita kanta Karime hawayen take yi. Drower ya bud'e ya ciro kud'i suka fita, da 'kyar ta samu ya bata yarinyar ta goyata.

"Kiga Karime kamar ta san zata rasu, jiya tasa aka ciro mata ragowan kud'in dake account d'inta, tace min idan ta haihu sai ta saida gidan nan mu samu kud'in komawa 'kasarsu, gashi yanzu iyayanta basu san ta rasu ba, na gama lura dasu tunda ta dawo Nigeria basu damu da ita ba. Wallahi suma na tsanesu ba zan ta'ba nemansu ba."

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now