K'UDIRINA page 35

154 11 1
                                    

*K'UDIRINA*

        ®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

        ©
*EASHA MD*

*Dedicated to Maryamerh Abdulrahman* (Kwaiseh)

           *35*

*Wattpad@ayshatmadu*

Washegari kuwa tunda wuri suka fara shirin tarbar bak'i.

Abinci aka zauna yi masu kala-kala.

Abokinnshi ne Isma'il yazo, falon saukan bak'i ya shigo dashi.

Sun zauna tare da k'ara gaisawa.

" Barister Isma'il muna shirin zuwa sai gashi ka rigamu."

"Aikuwa na rigaku, kan school d'in da za a sa Muhammad ne naga ya dace muyi magana."

"An samu ne?"

Magana ya fara yana mai gyara zamanshi.

"Eh! Naga inda d'iyata take yi yana da kyau gaskiya suna samun karatu, mai zai hana a sashi a nan."

"Tunda har ka yarda da tsarin makarantar, ba damuwa za a iya sashi. Sai mu bari zuwa Monday kenan ko? Na gode sosai da hidimar da kamin."

"Haba kai ba wani abu, ai mun zama d'aya, bari na wuce ina da wani aiki da zanyi yanzu."

"To shikenan  Barrister! Zaka iya ganinmu da daddare, nafa gode sosai."

Mik'ewa suka yi a tare suna mai k'ara mik'a ma junansu hannu, har bakin mota ya rakashi sannan ya dawo.

K'arasawa wurin Garba yayi tare da cewa.

"Mallam Garba yaya ake ciki ne? Ina so yanzu kaje gidanmu ka taho min dasu."

"To Alh bari na tafi."

"Yauwa Garba."

Ya wuce ciki ya bashi nan.

Mallam Musa ka san halin Alh yana birgeni, bai da k'yaman talaka duka kwananshi d'aya da dawowa gidan nan, amma jibi yanda ya saba damu ya d'aukemu tamkar 'yanuwanshi."

Mallam Musa yace.

"Tabbas Alh daban yake, fari ne mai farar aniya, ka duba kaga yanda yake son 'yanuwanshi."

Cikin d'an duk'o da kanshi kusa da Mallam Musa tare da furta magana can k'asa-k'asa.

"Kuma ka san 'yanuwan nashi su basa sonshi."

"Kai dan Allah.!"

"Wallahi kuwa nake fad'a maka wannan zancan, duk kyautata masu da yake basa gani. Basu k'i su bud'e ido suga baya doran k'asa."

"Lallai sun cika butulu, muda bamu had'a komai dashi ba, ya mana munji dad'i amma su suka sa jin dad'i. Kowa da irin halinshi."

"Kai dai bari kawai, bari naje na d'aukosu. Yawa garesu sai dai a d'auki motar can, ita kad'ai zata kwasosu."

Zuwa yayi ya shiga mota Mallam Musa ya bud'e mashi gate ya fita.

Shigewa yayi ya tadda duk sun gama shirya komai a kan dining.

D'akin Mommy Amina ya shiga ya taddata gaban mirrow tana kwalliya, jingina yayi jikin k'ofa ya hard'e hannu ya k'ura mata ido yana kallonta d'auke da murmushi a fuskarshi.

Juyowa tayi ta kalleshi itama da murmushin tana mai juya idanunta tare da furta.

"Wannan kallo haka?"

D'an murmusawa yayi tare da k'arasowa kusa da ita yana mai cewa.

"Duk sanda naga kinyi irin shigar nan tamu sai inga kin k'ara min kyau da kwarjini, sai inji bana gajiya da kallonki, baki ga yanda atamfar ta hau jikinki ba?"

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now