K'UDIRINA page 38

109 15 0
                                    

  *K'UDIRINA*

                  ®    
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

                  ©
        *EASHA MD*

        *Dedicated to Maryamerh Abdulrahman* (Kwaiseh)

                   *38*

*salam masoya littafin k'udirina Madu tambayar lfy shiru,wayana ne ya Samu Matsala shiyasa Kuka Jini shiru, amma insha Allahu bayan sallah zaku ci gaba da jina da zarar na maida wayar, yanzu dai ga Kad'an kuyi maneji*

Muhammad 'bata rai yayi sosai tare da zum'buro bakinshi. Mommy Amina ce ta dubeshi cikin kulawa tare da furta.

"Mai ya sameka lokaci guda ka canza?"

Cikin damuwa kamar zai yi kuka yace.

"Mommy bana son gidan nan."

Dafa mashi kai tayi cikin kulawa ta furta.

"Kada in sake jin ka fad'i haka, 'yan uwanka ne baka da tamkarsu a fad'in duniyar nan ka jini ko?"

D'aga mata kai yayi.

Farouk ya dubeshi tare da cewa.

"Ai zaneshi zanyi. Ku fito mu shiga ciki."

Fitowa suka yi jikin Muhammad sanyaye suka shiga cikin gidan da sallama.

Cikin girmamwa suka du'ka dan gaisheta. Da 'kyar ta amsa sai kace dole.

Mutanan gidan ne suka fito daga d'akunansu dan gaisawa dasu.

"Goggo naga gida yayi kyau sosai."
Farouk ya fad'a yana mai dubanta da fara'a d'auke a fuskarshi.

"Eh gida yayi kyau ba kamar naka ba, ka d'auko bare ta fiye maka mu, ita ka maka mata babban gida haka. Amma mu ka sakemu a nan ba."

Dafe kanshi yayi da hannayenshi biyu, yana mai tunanin irin halinsu dako mai zai masu basu ta'ba gani.

Muhammad ganin yanayin babanshi ya canza yasa ya mi'ke da sauri ya bar wurin. Wurin hayaniyar yaran gidan ya isa da suke gefe suna wasa. Wanda tun isowarsu gidan yaran basu zo sun gaidasu ba, in banda wasa ba abinda suke yi.

Mommy Amina da take zaune ne tabi d'an nata da ido wanda dai-dai lokacin daya isa wurinsu Abdallah yasa mashi 'kafa ya fad'i kan hannunshi wanda ya bugu sosai.

Kuka ya fashe dashi! Wanda Mommy Amina ta kasa jurewa, da sauri ta mi'ke ta isa inda yake ta d'aukeshi jikinta tana mai lallashinshi tare da ri'ke hannun daya bugu a kai tana mai danna mashi.

Duban Abdallah tayi wanda ya kauda kai, sai kace bashi ya aikata ba tace.

"Haba Abdallah! D'an uwanka ne fa, mai yasa zaka mashi haka?"

"Kai Amina haka kike baki da kawaici a kan yara?"

Cewar Safiya maman Abdallah dake zaune.

Goggo tayi caraf da fad'in.

"Ke kuwa ina zata yi kawaici an ta'ba d'an gwal."

Farouk ne yayi magana cikin dariya.

"Haba Goggo ba haka bane. Tunda abinda yayi Muhammad ai shi yayi Abdallah, ni a ganina ai duk d'aya ne."

"A'a! Ba d'aya bane akwai banbanci."

Dai-dai lokacin Mommy Amina ta iso, yasa hannunshi ya amsheshi yana mai girgiza kai tare da cewa.

"Goggo cikin satin nan zamu wuce umara gaba d'ayanmu harda Muhammad."

Kallo ta bishi cike da mamaki ba tare data iya furta kalma d'aya ba. Sai tafa hannayenta da takeyi.  D'an nisawa tayi sannan ta furta.

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now