K'UDIRINA page 27

117 10 0
                                    

  *K'UDIRINA*

      ®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

       ©
*EASHA MD*

*Dedicated to Maryamerh Abdulrahman* (Kwaiseh)

              *27*

Ta dawo gida bayan ta huta, ji tayi wayanta ya fara k'ara, inda tazo d'auka dan ganin mai kiranta. Dubawa tayi taga bata san number d'in da aka kirata ba. D'auka tayi da sallama, ya amsa cikin jin dad'i.

Tambayarta yayi.

"Kinko gane mai magana?"

Girgiza kai tayi kamar yana kallonta, ta furta.

"A'a"

"To wanda muka had'u ne d'azun. Ina fatan zan samu gurbi a zuciyarki. Dan ina ganinki na kamu da sonki, naga na riga dana samu matar aure."

Rufe idonta tayi alamun jin nauyin kalmar so daya furta mata.

"Ya naji kinyi shiru?"

"A'a ina jinka."

Kode ban maki bane? Bana so ki fad'a min haka dan ba zan iya jurewa da rashinki ba a tare dani."

D'an ajiyar zuciya ta sauke had'i da cewa.

"Idan ba damuwa ka bari zuwa anjima sai muyi waya."

"OK! Ba damuwa Allah ya kaimu anjiman."

Ya katse wayar. Tunda suka gama wayar, maganar da suka yi yake ta dawo mata a rai.

Tana cikin tunani, sai ga Zarah ta kirata, tana d'agawa ta fara tambayarta.

"Ya ake ciki ya kiraki kuwa?"

"Eh ya kirani wai yana sona."

Ta fad'a mata.

"To ke kuma sai kika ce masa mai?"

"Kai wannan irin tambaya haka? To ce mashi nayi bana ra'ayinshi.

"Kai dan Allah kada ki mana haka mana. Dan Allah ya kuka yi dashi?"

"Ce mashi nayi sai zuwa anjima zan fad'a mashi."

"To kawai kice mashi kin amince musha biki."

"Kede ake ji, duk kinbi kin dameni."

Cewar Islam.

"Islam kin gane ki cire maganar wasa, ki tsaya ki natsu ki gane mai sonki kiyi aure. Kinga ke marainiya ce baki da iyaye, daga ke sai Yaya Muhammad, gara kema ki samu d'akin kanki sai kinfi jinki dai-dai akan zaman da zaki tayi tare da matar yayanki, ba fata ake ba, wataran zata iya nuna ta gaji da zama dake. Ki zauna kiyi tunani ki gani."

Dogon ajiyar zuciya Islam ta sauke, had'i da cewa.

"Zarah naji dad'i da shawarar da kika bani, zan k'ok'arta inga na d'auka, amma a son raina naso sai na cika k'udirin dake raina sannan zanyi aure."

"Ko a gidanki ne zaki iya yi tare ma da taimakon mijinki."

Sun dad'e suna tattaunawa sannan suka yi sallama. Islam sai juya maganganun da suka yi da Zarah take.

Kamar yanda suka yi kuwa, sai gashi da daddare ya kirata, lokacin har tayi shirin barci. D'auka tayi da sallama, suka gaisa. Magana yayi.

"To ya muke ciki in san matsayina?"

D'an murmushi tayi.

"Ki fad'a min kada kiji komai, ina sauraranki."

"Ba damuwa na amince."

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now