K'IDIRINA Page 51

114 13 2
                                    

*K'UDIRINA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)

*51*

*Wattpad: Ayshatmadu*

Tuna wannan rayuwar shi ya sashi kuka sosai harda shashshe'ka, cikin d'akin ba wanda bai fidda hawaye.

Nisawa yayi yace.

"Islam idan har na isa dake, idan kuma zaki duba abinda iyayenshi suka mana ina so ki rabu dashi. Islam na sadau'kar da farin cikina dan ke ki samu, baki ta'ba neman abu ban maki ba, Islam ina umurtarki da ki rabu da Abdallah, gidansu ba gidan zama bane."

Fashewa yayi da kuka yace.

"Islam sune suka kashe mana mahaifinmu da hannunsu, a dalilin haka itama mahaifiyarku ta rasa rayuwarta. A sanadinsu muka shiga 'kuncin rayuwa bayan sune sanadin rasa iyayanmu suka rabamu da dukiyoyinmu suka kasa ri'kemu, shine zaki yi tunanin zama dashi, Islam ina mai shawartarki daki rabu da Abdallah."

'Kwallara 'kara tayi ta zube 'kasa sumammiya. Da gudu suka yi kanta, Muhammad jijjigata yake yana ambaton sunanta cikin tashin hankali.

D'aukarta yayi kacokan yayi waje, duk ya gama rud'ewa, ambaton sunanta kawai yake yana jijjigata.

Hajiya ce ta tsaidashi tana fad'in.

"Muhammad kabi komai a hankali, tsaya mana."

Ina hankalinshi ya tafi keke napep ya tsaida da sauri ya shiga yace.

"Kayi sauri ka kaimu asibiti, ka anzarta kada na rasa amanata."

Wani 'karamin asibiti dake kusa dasu ya idasa dasu, ganin halin da take ciki basu wani tsaya 'bata lokaci ba suka yi emergency da ita.

Hajiya da Aunty Fati ne suka biyoshi a baya, ganin har yanzu hankalinshi a tashe yake, sai faman safa da marwa yake. Hajiya ta ri'koshi ta zaunar dashi.

'Ko'karin ceto rayuwarta suka fara yi, amma har yanzu bata farka ba.

'Ko'karin ceto rayuwarta suka fara yi, amma har yanzu bata farka ba

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Addu'a yake ta faman yi, Allah ya tadata. Tambayar kanshi yake.

"Shin mai ya sata ta suma ne? Mai na fad'a mata da bai mata dad'i ba har ya kaita da shiga wannan yanayin?"

Rasa takamaiman amsa ne ya bashi damar yin shiru, in banda addu'a ba abinda yake yi.

Sai can ta farka tana sambatu, allura aka mata na barci, kana aka sa mata drip.

Doctor d'in ne ya fito ya dubesu suna tsaye curko-curko yace.

"Alhamdulillah! Mun samu ta farfad'o."

Cikin damuwa Muhammad yace.

"Amma Doctor meke damunta haka?"

Ya bashi amsa da cewar.

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now