*K'UDIRINA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)
*59*
*Wattpad: Ayshatmadu*
Ganin tana ta kira bai d'auka ba yasa tayi tunanin ko ya bar wayarshi a gida ne? Tunanin hakan shi ya bata damar ta suri gyalenta don zuwa ta sameshi a wajen ayi wacce za ayi.
Fita tayi ba tare data damu da cincirindon mutanan dake wajan ba. Dai-dai lokacin da aka gayyato waliyan ma'auaratan dai-dai lokacin da ta isa wurin.
Hangan Yaya Muhammad tayi fuskarshi a sake yana ta dariya, sai dai zuciyarta ya bata wannan dariyar ta dole ce.
Hangota yayi tana nufoshi, da sauri ya baro wurin abokanshi ya taho, yana isowa ya fara tambayarta.
"Islam mai ya fito dake a dai-dai wannan lokacin?"
Hawaye ne ya gangaro mata ta kasa magana.
Rik'eta yayi yana mai k'ara tambayarta.
"Yaya so nake a fasa auran nan."
Runts idanunshi yayi kana ya bud'e su yana kallonta tare da cewa.
"Kinko san abinda kike cewa kuwa? Islam ba na riga da na yarda auranki ba, ya kuma zaki yi haka bayan an tara jama'a don nuna shaidar auranki?"
"Yaya da gaske nake bana son auran nan, ba abinda zanyi dashi bana sonshi."
Cikin tashin hankali yace.
"Islam anya kina cikin hankalinshi kuwa?"
Cikin kuka da nuna tsantsar k'iyayyar auran tace.
"Yaya ina cikin hankalina, a cikin hankali nake maganata ina so a dakatar da d'aurin auran nan tun kafin ka rasani gaba d'aya."
"Islam wani abu ne ya faru? Taya zan iya zuwa in tunkari bainar jama'an nan ince a dakatar da d'aurin auran nan?"
"Yaya farin cikin wa kafi so tsakanina da mutanan da aka tara?"
Shiru yayi yana kallonta. Ganin bai ce komai ba shi ya bata damar ci gaba da maganarta.
"To idan har kafi son farin cikina akan na kowa ina so kaje kasa a dakatar da d'aurin auran nan."
"Islam ba zan iya ba, ba zan iya ba yamin nauyi a baki."
Kallonshi tayi tare da cewa.
"Ni zan iya domin ranar nan dama nake jira."
Kafin ya ankara ta wuceshi ta kutsa cikin mutanan dake wurin, cikin nazari take tafiya dan ganin ta isa wurin.
Harda gudu ta had'a dan gani take kafin ta isa wurin an d'aura auran. Kowa dake wurin mamakin yanda take kutsa kai yake, wad'anda kuwa suka san ita ce amarya tambayar junansu suke mai ya kawota wurin nan.
Tana isa cikin haki saboda sauri da gudun da take yi yasa ta fara magana sama sama.
"Kada a d'aura auran nan a dakata. Nice amaryar da zan auri Abdallah, amma a yau na canza na fasa auranshi saboda bai dace dani ba."
Kowa dake wurin binta yayi da kallon mamaki. Daddy'n Ayshat ne ya taso ya iso wurinta yace.
"Islam mai yayi zafi haka?"
"Daddy bana sonshi idan aka kuskura aka d'aura aurena dashi tabbas za a kwashi gawata."
Ta idasa maganar cikin saukowar wasu zafafan hawaye.
YOU ARE READING
K'UDIRINA
Fiksi PenggemarLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.