*K'UDIRINA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Dedicated to Maryamerh Abdulrahman* (Kwaiseh)
*40*
Mommy Amina ta samu ciki, Farouk ba k'aramin dad'i yaji da haka ba.
Gaba d'aya sun d'auki buri sun d'aura akan cikinta.
Ko Muhammad fita yayi ya dawn, hankalinshi na kan 'kanwata.
Tun cikin na wata biyar suka tafi siyayyan kayan haihuwa.
Ta dage sai jidan kayan mata take, kallonta yayi cikin kulawa da soyayyarta tace.
"Wai ya naga kina ta jidan kayan mata ne?"
Dubanshi tayi da murmushi tare da furta.
"Ina ji a jikina d'iya mace zan aura."
"To Allah ya kawo mana ita ya raya mana ita, mu rayu tare da junanmu."
"Amin ya rabbi.!"
Ta fad'a cikin kashe mashi ido d'aya tare da murmushi.
Kayan sosai suka siya, haka ta d'iban ma Muhammad nashi kayan shima.
Sun koma gida duk a gajiye, samu tayi ta shirya Muhammad dan tafiya Islamiyyar hadda da yake yi.
Duban Amina yayi tare da furta.
"Mommy bana son zuwa islamiyya yau, saboda na gaji da yawa."
Dubanshi tayi cikin kulawa tare da dafa mashi kafad'a tare da furta.
"Haba Muhammad! Idan ka zauna a gida mai zaka yi? So Kake haddar da kake ta zube ne? Baka san irinku suna da 'karanci ba, duka shekarunka nawa amma gashi saura wata biyu kayi hadda. Ko baka so ayi haddar da kai ne?"
Da sauri ya girgiza kai tare da cewa.
"A'a Mommy ina so."
"To maza ka wuce driver na jiranka ya kaika, Allah ya bada sa'a."
Da kanta ta had'a mashi d'an abin ciye-ciye, tasa mashi a jakarshi. Sai da ta rakashi 'kofar fita d'aki sannan ta dawo ciki.
*** ***
"Assalamu alaikum! Assalamu alaikum!!..""Wai masu gidan basu nan ne sai faman sallama nake amma shiru?"
"A'a Goggo muna ciki ne."
Amina ta fad'a dai-dai lokacin da take saukowa daga saman bene.
"Damar fitowa ne baku yi ba kenan dan baku d'aukeni mahaifiya ba ko? Dan na tabbata inda uwar data haifeshi ne da baku yi banza da ita ba Ko? Shiyasa har masu aikin gidan na rasa wanda zai amsa min sallamata saboda banda muhimmanci a idonku."
"A'a ba haka bane."
Ta fad'a tana mai du'kawa dan ta gaidata.
Ba tare data jira ta 'kara magana ba tace.
"Ina Muhammad d'in?"
"Yana ciki yana barci."
"Zaki iya shiga ki tado min shi, dan ina son yin magana dashi."
Ta fad'a tana mai kallonta, kallo mai cike da nuna tsantsar 'kiyayya.
Mi'kewa tayi jiki a sanyaye ta haye sama dan kira mata Farouk d'in.
Zama tayi bakin gado kusa da inda yake kwance ta dafa kanshi, dan a tsarintsu ba kai tsaye suke tada junansu daga barci ba, wanda zai iya haifar ma mutum da ciwon kai.
Shiru tayi tana mai kallonshi. Hura mashi iska ta fara yi dai-dai fuskarshi yanayin yanda yake jin iskar na kad'ashi yasa ya fara bud'e idonshi a hankali, har ya gama bud'esu yayin daya saukesu a kan fuskarta.
Murmushi ya sakar mata, inda ta maida mashi da martani.
Cikin kulawa yace.
"Ya a kayi? Mai kike so?"
"Dama Goggo ce tazo take son ganinka."
D'an 'bata rai yayi tare da cewa.
"Mai kuma zan mata? Ni ta fara takura min."
"Kada ka fad'i haka.! Kai da kanka kake fad'in tamkar uwa take a gareka. So kada ka 'kara fad'in haka, tashi muje kada tace an shanyata ya zama laifi kuma."
Mi'kewa yayi ya sauko yana mai mutsitstsike idanunshi, a tare suka sauko 'kasa.
Du'kawa yayi har 'kasa ya gaidata ta amsa cikin sakin fuska.
"Kana barci nasa an tadoka. Da yake sauri nake ma sai ka koma ka kwanta, dama kud'i nake so ka bani zanyi bikin jikar 'kawata."
"Kamar nawa kike so?"
"Dubu d'ari saboda kaga ta sani a 'kirjin biki bai kamata in bata kunya ba. Kaga dole in mata abinda zata ji dad'i."
Dafe kanshi yayi yana mai tunanin yanda suke d'auko hidima mai girma suna d'aura mashi. Cikin girmamawa yace.
"Goggo idan ba damuwa da sai in baki dubu hamsin, saboda akwai hidindimun dake gabana da zanyi, gana walimar Muhammad ga kuma company na saida motoci da zan bud'e kwanan nan, abubuwan da yawa."
"Akwai damuwa! Dubu hamsin ya min kad'an, ai sai a min dariya. Kawai ka shiga ka fito da kud'i ka bani ba ka zauna kana cikani da surutu ba, dan ka bani wannan kud'in ba abinda zai ragu daga cikin dukiyarka."
D'agowa yayi ya had'a ido da Amina wanda ta d'aga mashi kai alamun ka bata.
Mi'kewa yayi ya shiga ciki, ba jimawa ya fito da kud'i a hannunshi. Du'kawa yayi ya mi'ka mata, hannu tasa ta amsa ba tare daya samu arzi'kin godiya ba.
Mi'kewa yayi tare da furta.
"To ni zan wuce, sai ka rin'ka ha'kuri damu tunda kai d'aya Allah ya za'ba a cikinmu ya maka arzi'ki."
"Goggo ba komai ai, sai anjima."
Tasa kai ta fita daga d'akin.
Dogon ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon Amina yace.
"Na rasa yanda zanyi da wad'an nan mutanan. Gaba d'aya dukiyata suke so bani ba, idan har zan basu shikenan na gama masu komai, basu damu da komi nawa ba."
Cikin kulawa ta furta.
"Kaita ha'kuri wata rana sai labari, sai kaga kamar ba ayi ba."
"Hakane bari na shiga ciki na watsa ruwa."
Tafiya ya fara yi, ta bishi da kallo tana mai jin tausayin mijin nata.
*** ***
Bayan wata biyu, gagarumin walima ake na haddar Muhammad, sosai makarantar suka yi alfahari dashi, dan shi kad'ai ne mai 'karancin shekaru a cikin mahaddatan. Sosai ya samu kyaututtuka.Abubuwa kala kala aka buga dan rabawa al'umma, hidima sosai aka yi, wanda Goggo sai fad'a take tana ganin almubazzaranci ne kawai wannan.
"Haba Faruku! Wannan uban kud'i da ka kashe haka akan d'an tatsitsin yaron nan. Abin yayi yawa fa."
D'an murmushi yayi, kana yace.
"Haba Goggo ba wani abu bane fa, hakan da nayi shi zai 'kara bashi 'kwarin gwiwa kan duk abinda zai sa gaba. Yanzu haka kinga jss 1 zaije, kuma kinga yana daga cikin 'kwarin gwiwan da nake bashi."
"To Allah ya taimaka ya bada sa'a."
"Yauwa Goggo abinda ya kamata ki fad'a kenan."
Har dare gida cike yake da abokan arzi'ki hatta wad'anda ba a gayyata ba, nan suka shigo suka cika cikinsu a gidan har suka tafi dashi.
*** ***
Zaune suke a palour suna fira cikin nishad'i.Mallam Musa ya shigo cikin girmamawa yace.
"Alhaji dama su Alh Salisu ne suka zo, suka ce na duba ka ko kana ciki."
Nan take gabanshi ya fad'i wanda bai san dalilin hakan ba. Cikin yanayin damuwa yace.
"Kace masu su shigo ina ciki."
"To ranka ya dad'e."
Yasa kai ya fita dan shaida masu sa'kon uban gidanshi.
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.