K'UDIRINA page 57

92 12 1
                                    

*K'UDIRINA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)

      *57*

*Wattpad: Ayshatmadu*

***
Ana gobe biki aka kawo lefen Islam, akwati set uku kowanne dank'are da kaya na nuna ma tsara.

Kallo kawai take abin na bata mamaki irin wannan kashe kud'i haka kamar ba a tunanin lahira.

"Zarah ta dubi Islam tace.

"Lallai kud'i sun sha kashi a wurin nan yanda ka san ba a san zafin nemanshi ba."

Islam tayi murmushi mai kama da takaici tace.

"Ina fa zasu san zafin nemanshi tunda a sama suka sameshi ba tare da sun sha wuya ba."

Gyara zama Ayshat tayi tare da d'aura k'afa d'aya kan d'aya tace.

"Au dama kin san da haka kuma kika kafe a kan sai kin aureshi? Ai ni kina bani mamaki da takaici. Ai wallahi idan nice ke ko kallo bai isheni ba."

Murmushi Islam tayi had'i da cewa.

"Hmm! Ba zaku gane bane shiyasa har kuke zama kuna irin wannan maganar."

"To ai da kin ganar damu tunda ke kin gane, ni idan kina wannnan murmushin ma baki san k'ara 'bata min rai kike ba."

Zarah tace.

"Kinga Ayshat musa mata idanu, mai d'aki shi ya san inda yake mashi zuba, sai dai tasa a ranta daga ranar da suka gano wacece ita to farin cikinta ya k'are. Sai kuma ki fara shirin irin zaman k'uncin da zaki yi kafin su shirya yanda zasu yi suga kin bar duniyar."

Gaba d'aya ranta ya gama 'baci, tana nuna su da yatsa tace.

"Tabbas yanzu na fara tabbatar da gaskiyar abinda ke ranku, yanzu fatan da kuke min kenan? Na gode sosai kunga na san irin zaman da zanyi daku."

Ayshat tace.

"Islam ko mai zaki ce kice, muna nan a kan bakanmu, na fad'a a gabanki ba zan ta'ba son Abdallah ba, na tsaneshi a rayuwata, ina so ki sani ba wai na tsaneshi haka kawai bane sai dan abinda iyayenshi suka ma iyayenku dashi shima kanshi. Dan haka idan kin d'aukemu a matsayin mak'iyanki ne da bama son ci gabanki to hakane."

Gaba d'aya ran Ayshat ya gama'baci, mi'kewa tayi ta bar d'akin cikin 'bacin rai.

Binta Islam tayi da kallo ba tare da ta iya tsaidata ba.

Komawa tayi ta kwanta tare da lumshe idanunta tana sauke numfashi da sauri da sauri.

Jin maganar Ayshat tayi ya daki kuna wadda magana ya ciwota ta k'ara dawowa d'akin.

"Ki sani Islam zaki auri Abdallah ne ba dan Yaya Muhammad na so ba, sai dan kina so ne yabi bayanki, amma ki sani har yanzu zuciyarshi na mashi d'aci da wannan auran da zaki yi dan ba yanda zaiyi ne. Ko hakan bai isa yasa ki ha'kura dashi ba ko min son da kike mashi, koda kuwa wani da ban ne ba Abdallah ba ai zaki iya ha'kura dashi ko dan farin cikin Yayanki da a kullum yake faranta maki."

Mi'kewa tayi zaune tana bin Ayshat da idanunta wanda tuni sun jik'e da hawaye. Tabbas Ayshat gaskiya ta fad'a sai dai ya za tayi? Gaba d'aya ta lula dogon tunani.

"Ga mai lalle nan a waje tazo."

Maganar Ayshat ya k'ara bugun dodon kunnanta.

"Kice mata ta shigo."

Fita tayi ba a jima ba mai lallan ta shigo. Ta gama had'a komai ta zauna zaman zana ma Islam lalle. Sai da aka gama mata Zarah ta mi'ke dan kiran Ayshat, da k'yar ta lalla'bata tazo dan tayi lallan.

Sai da ta masu harda Aunty Fatima sannan ta tafi.

Shirin biki aka ci gaba dayi gida ya cika mak'il da 'yan biki duk 'yan uwan Hajiya ne.

Gaba d'aya ranar Islam sukuku take zaune kawai take gabanta na fad'uwa. Ta rasa dalilin hakan, dan ta fara tsorata da abinda take shirin yi, yanzu ya zata yi? Wane abu zata fuskanta da haka? Ba haka taso auranta ya kasance ba ba tare data nuna farin ciki ba, bata so ace aure za tayi ba tare da bata gayyato kowa ba.

Mai zai faru da abinda take shirin yi? Ba zata samu matsala da hakan ba kuwa?

Hawaye ne ya zubo mata ya gama wanke mata fuska. Zarah ce ta shigo d'auke da kwalaye biyu a hannunta, ta dire gaban Islam da sauri tace.

"K'awata mai ya sameki haka ne kike kuka?"

D'an kwanciya tayi jikin Zarah cikin kuka tace.

"Zarah na fara sarewa da abinda nake shirin yi, ban san a ya zai zo min ba, mai yasa da na tashi yi nayi abina ni kad'ai ba tare dana saka wani a ciki dan neman shawara ba."

"Islam ban fahimceki ba mai kike nufi da wannan maganar?"

"Zarah ki samin ido kiga abinda na shirya wanda ban san a yanda zai zo min ba, fad'uwa ko nasara. Wallahi ina cikin matsala."

Fashewa ta k'ara yi da kuka yayin da Zarah taci gaba da lallashinta, tana tunanin mai Islam take nufi ita fa bata fahimceta ba.

"Islam har yanzu ban fahimci abinda kike nufi ba, saboda baki so in gane ba, amma ina baki shawara da kibi komai a hankali kisa ma ranki ha'kuri. Ga nawa gudunmuwana na kawo maki."

Dubawa islam tayi taga set d'in food flask ne masu kyau har guda biyu.

Cikin jin dad'i tayi ma Zarah godiya,sai dai har yanzu zuciyarta na mata zafi da tafarfasa.

Wayarta ne ke k'ara, ganin mai kiranta ba k'aramin razana tayi ba. Sai da ya kusa katsewa kana ta d'auka. Cikin sanyin murya tayi sallama, amsawa yayi cikin lumshe ido da jin dad'i.

Gaidashi tayi ya amsa tare da tambayarta.

"Mai ya hanaki zuwa School yau?"

Ji tayi gabanta ya fad'i, shiru tayi ta kasa bashi amsa.

K'ara jeho mata tambayar yayi.

Cikin inda inda tace.

"Da..dama ban..banda lafiya ne."

Cikin nuna damuwa yace.

"Meke damunki ne?"

"D'an zazza'bi ne ke damuna."

"Ayya sannu Allah ya baki lafiya, ko zan iya zuwa na dubaki?"

Da sauri tace.

"A'a kada kazo dan Allah."

"Meyasa haka naga duk kin razana dan nace zanzo?"

"A'a bakomai kawai dai."

Dogon ajiyar zuciya ya sauke yace.

"Shikenan ba damuwa Allah ya baki lafiya."

Datse wayar yayi, yayin da ita kuma tabi wayar da kallo, fashewa tayi da kuka wanda bata san dalilinshi ba.

Ayshat ta shigo ganin Islam na kuka bai sa ta tambayeta abinda ya sata kuka ba, wayarta ta bud'e tasa wak'a taci gaba dayi tana karkad'a kanta.

Mi'kewa Islam tayi ta d'auki abinda Zarah ta kawo mata ta fita dashi dan kai ma Aunty Fatima ta gani.

Godiya tayi sosai tare da d'auka ta kaima Hajiya itama dai godiyar tayi.

Ranar dai kowa na barci amma ya gagari Islam dan ta rasa meke mata dad'i a ranta, ta rasa mai zata yi zuciyarta tayi mata sanyi. Data tuna gobe ne sai taji hankalinta ya k'ara tashi, taji zuciyarta na bugawa da sauri da sauri.

Kome hakan ke nufi?

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now