K'UDIRINA page 62

136 12 2
                                    

*K'UDIRINA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)

      *62*

*Wattpad: Ayshatmadu*

Salim ne ya shigo ya tadda Mom da Dad a palour zaune suna fira, samun wuri yayi ya zauna tare da yi masu sannu da gida. Shiru ne ya biyo baya, du'kar da kanshi k'asa yayi yana son yayi magana amma ya kasa. Dad ya kalleshi cikin kulawa yace.

"Salim ya akayi ne naji kayi shiru kamar akwai abinda kake son furtawa."

Cikin hard'ewar murya yace.

"Dad da..dama gi..gidan da nake neman aure ne suka ce in tsaya cikin shiri zasu iya nemana akan sa ranar aure."

Kallo Dad ya bishi dashi cikin tamke fuska had'i da cewa.

"Salim ina d'aukarka mai hankali ashe baka da hankali, ina d'aukarka mai natsuwa ashe baka dashi, ina d'aukarka mai jin maganar iyayenshi ashe ba haka bane. Wai mai ka d'auki kanka ne?"

Mom itama ta d'aura da nata.

"Haba Salim na d'auka yaran nan su Nasim zaka ga suna haka ka tsawata masu ba kai ba. A dage ayi ta abu guda ina dalilin haka, gaskiya ka canza halinka tun wuri."

Cikin damuwa yace.

"Haba Mom wai ya kuke so inyi da rayuwata ne? Nifa namiji ne ba mace ba da za a tilasta min auran da bashi nake so ba, ko mace ma ai bai dace ba bare ni. Na san inda ke min ciwo na san wacce ta dace da rayuwata."

"Oh kana nufin ita Farida da ake son had'aku bata dace da kai ba kenan?"

Mom ta fad'a ranta a 'bace tare da binshi da harara.

"Mom tabbas Farida bata dace dani ba kuma kun sani kun dai take ne kawai. Kun san bata da tarbiya kawai saboda wani dalili naku ne kuke son had'a auran nan. Dad kun sanni ba tun yau ba ban son mace mara kamun kai kuma bana son auran d'iyar mai kud'i sangartacciya."

"Wai kai wane irin mutumin banza ne? Wato ka had'a kayi mana kud'in goro kenan? Idan baka son 'ya'yan masu kud'i ka kashesu ka huta."

Dad ne yake maganar cikin 'bacin rai yana jin kamar ya tashi ya kai mashi duka.

Mom tace.

"Ka barni dashi muyi magana ka san halinshi d'an a lalla'bashi ne."

"Ba zan lalla'bashi ba, nace ba zan lalla'baka ba, kai ka haifeni ko ni na haifeka?"

Mom ce ta mi'ke cikin kulawa ta dubi Salim da yake zaune shima ranshi a 'bace tace.

"Biyoni d'akina."

Mi'kewa yayi ya bita ba tare da musawa ba har suka isa d'akin nata.

"Haba Salim meyasa kake haka? Mufa muka haifeka ya kamata ace kana bamu girmanmu. Sai a maka magana ka nuna kai sai abinda kake so shi zaka yi, miye dan ka auri Farida tana sonka duk abinda kake so tayi zata yi."

"Amma Mom kin san ina girmamaku iya girmamawa ina maku abinda kuke so, wannan ne kawai ba zan amince ba."

Cikin tausasa murya tace.

"Haba Salim kada ka manta mu iyayenka ne da kullum muke son farin cikinka, mahaifinka shi ya d'auki nauyin komai naka har ka kawo yanzu da kake alfahari da kanka, yaso ka zauna company nashi a matsayinka na babba dan ka kulan mashi da komai amma kasa k'afanka ka ture. Baiyi k'asa a gwiwa ba ya barka kayi ra'ayinka kana yasa kaje ka k'ara yin wani degree d'in a fannin Business dan dai ko ra'ayinka zai karkato ga kan company amma kasa k'afa ka ture. Yanzu kuma ya bijiro maka da maganar aure ka nuna bai isa ba, mai kake tsinta a aikin da kake yi?"

Dafe kanshi yayi da yaji ya sara mashi, tare da k'ara tamke fuska kamar zaiyi kuka. Dubanshi taci gaba dayi.

"Ya kamata kaje ka natsu kayi tunani, zaka iya tafiya."

Mi'kewa yayi ya fice, kamar zai koma d'akinshi ya fasa dan jin yayi gaba d'aya koda ya zauna a gidan ba zaiji dad'in zama ba. Mota ya shiga ya tada ya fita gidan, tunanin inda zuciyarshi ta raya mashi yaje yayi, juya akalar motar yayi zuwa gidansu Farida.

Yana isa ya lalubo wayarshi ya kirata, kwance take tana kallo, ganin mai kiranta yasa ta mi'ke zaune da sauri tana murza idanunta. D'auka tayi cikin yanga tana fari da inanunta.

"Ki fito gani a k'ofar gidanku."

Amsa ta bashi da.

"Meyasa ba zaka shigo ciki ba?"

"Sauri nake idan kika tsaya 'bata min lokaci zan tafi..."

Da sauri ta katseshi da fad'in.

"Dan Allah kada ka tafi gani nan zuwa."

Mi'kewa tayi cikin sauri ta gyara fuskarta gami da fesa turare ta suri gyalenta har tana had'awa da gudu ta fice ba tare da Ammi ta sani ba.

Samunshi tayi zaune yana wasa da key d'in mota hannu, da fara'arta ta isa sai yanga take tana taunar chewingum sai fari take da ido tace.

"Hala 'batan hanya kayi na ganka a nan?"

D'an murmushi yayi yace.

"Ba 'batan hanya da nayi zuwan naki ne, kuma ina so ki natsu ki saurareni."

"To ai da kazo mun shiga ciki ko, naga ko harabar gidan ma baka shiga ba ka tsaya k'ofar gidan."

"Kada ki damu nan ya isheni. Farida miye ginshik'in aure?"

D'an jim tayi tana tunani, ta rasa me zata ce.

"Baki sani ba ko? Ina tunanin ginshik'in aure soyayya ce, to kinga ba maganar soyayya a tsakanina da ke had'in iyaye ne ba namu ba, dan haka ina so ki cire tunanin auran da ake so a had'a ki rungumi masu sonki."

Tuni ta jik'e sharkaf da hawaye, cikin hawaye da damuwa tace.

"Kada ka min haka, duk duniya babu wanda nake so kamar kai, idan har kak'i amincewa dani ban san ya zanyi da rayuwata ba."

"Farida kisa ma ranki ha'kuri, ina da wadda nake so zan aura yanzu ma gaf ake da maganar aure, kinga kada kice na yaudareki tunda tuntuni na fad'a maki bani da ra'ayi a kanki."

"Salim dama soyayyar tana iya zama k'iyayya? Soyayyata ta gaskiya ce ba ta k'arya ba."

"Na riga da na gama magana zan wuce."

Rugawa tayi da gudu ta shige cikin gida, fad'awa tayi kan gado ta saki kuka. Ammi da ta fito ta fara jin sheshshe'kar kuka. Da sauri tayi wurin d'akin Farida ta tura k'ofar ta shiga, saurin rik'ota tayi tana tambayarta.

"Farida meke damunki? Mai aka maki?"

Cikin kuka ta kwanta jikin Ammi tare da cewa.

"Ammi ya zanyi da rayuwata ina zansa kaina?"

K'ara fashewa tayi da kuka. Cikin kulawa tace.

"Kwantar da hankalinki kiyi mani bayani meya faru dake?"

"Ammi Salim ba zai ta'ba sona ba, har gida yazo yaci min mutunci wai yana fad'a min in k'yaleshi ya samu matar aure."

Binta Ammi tayi da kallo tana mai jin tausayin 'yar tata a cikin ranta tace.

"Kiyi ha'kuri ni zan san abin yi a kanshi, dan ba zan jure kallonki cikin yanayin damuwa ba."

D'ago da kanta tayi tana duban Ammi tare da cewa.

"Ammi mai zaki min da zan sameshi?"

"Kede kawai kisa min ido zaki ga abinda zanyi, baki da miji sai Salim. Share hawayenki kije ki gyara fuskarki zaki ga abin mamaki."

Mi'kewa tayi cikin jin dad'i ta wuce d'akinta tana mai cike dafarin ciki sai kace ba ita bace ta gama kuka yanzu har da shashshek'a.

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now