K'UDIRINA page 37

109 7 0
                                    

*K'UDIRINA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Dedicated to Maryamerh Abdulrahman* (Kwaiseh)

*37*

*Wattpad@ayshatmadu*

Kamar yanda Farouk yace, kwana biyu da zuwansu ya nemi ma'aikata suka fara gyara masu gida, nan gidanshi suka dawo, duk tsiyan da suke Amina bata ta'ba d'aga kai ta kallesu, ba wahalar da Muhammad baya sha a wurin Abdallah. Amma Amina bata ta'ba cewa dan me ba.

Cikin haka aka sama ma Muhammad makaranta ya fara zuwa, baya dawowa gidan sai yamma.

Duk da k'ank'anta irin na Muhammad, yanda yaga Abdallah na takura mashi, yasa shima yaji ya fita a ranshi, dan a kullum Abdallah bashi da magana sai na baya k'aunar Muhammad da iyayenshi.

Cikin hukuncin Allah aka gama gyaran gidansu, yanayi na girman gidan yasa har aka k'ara d'aki na masauk'in bak'i. Gini mai kyau aka masu sosai. Ga kayan d'aki duk yasa masu wasu. Tsayawa fad'in murnar da suka yi na ganin gidan 'bata lokaci ne.

Sun koma sunci gaba da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali, sai dai fa har a lokacin k'iyayyar Farouk tana nan a cikin zuciyoyinsu.

*** ***
"To yanzu Habibty kinga na gama da wannan matsalar tasu, sai kuma sun samo wani sabon."

Gyara zamanta tayi tare da maida hankalinta kanshi tace.

"Nifa idan naga yanda suke nuna maka k'iyayya a fili har mamaki suke bani. Tun a zamansu gidan nan na k'ara fahimtarsu sosai, basa son ci gabanka, a kullum suna so su ganka cikin k'unci. Sai dai basu sani ba mijina ya san yanda zai iya zama dasu."

"Sosai kuwa Habibty! Tuntuni na san su mamugunta ne, na rasa mai na masu suka tsaneni haka, jibi wannan yaron Abdallah yanda yake gana ma Muhammad azaba, yake kuma nuna mana k'iyayya k'arara d'an yaro dashi."

Amina tace.

"Uhm! Kai dai raba kanka da d'an yau, ba abinda yaga iyayanshi nayi ba kenan. Allah dai yasa mu dace."

"To Amin! Nafa gama shirina dan tafiya Cairo, kin san zanje su sallameni aikina ya dawo nan gaba d'aya d'in."

"Kada fa kana zuwa suce ba zasu k'yaleka ba."

D'an dariya yayi tare da cewa.

"Haba wane su, ai tun kafin mu taho sun san da maganar, duk da dai ransu bai so ba. Nima ai kinga gara nazo na inganta k'asata ko?"

"Hakane kam. Kwana nawa zaka yi?"

"Sai dai kin gani.."

Ya fad'a yana mai kallon yanayin fuskarta daya canza. Dariya ya fara mata yaci gaba da magana.

"Kada ki damu ba dad'ewa zanyi ba ko dan company na robobi da nake so in bud'e, kuma tun a waya na fara magana dasu, tafiyar ba zata d'auki wani lokaci ba."

"Shikenan! Allah ya dawo min da kai lafiya."

"Amin Habibty."

*** ***
Ya gama shirinshi na tafiya, har airport suka rakashi suka dawo, ji take duk gidan baya mata dad'i.

Amma ya zata yi tunda dama haka zaman auran ya gada, yanayinta na mai son jama'a ko ya suke yasa ta shige cikin su Iya, tare take komai dasu, dan jinsu take tamkar 'yanuwanta.

Suma ba k'aramin jin dad'in zama da ita suke ba, suna jin dad'in yanda take shigewa cikin su tayi fira dasu suyi aiki tare. Ga abinta bai rufe mata ido ba, basu san da abu ba zata d'auko ta basu.

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now