K'UDIRINA page 31

131 11 0
                                    

K'UDIRINA

        ®
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

        ©
EASHA MD

Dedicated to Maryamerh Abdulrahman (Kwaiseh)

          30

Wattpad@ayshatmadu

K'arasowa inda yake zaune tayi tana mai mashi wani irin kallo na rashin kyauta abinda ya mata.

"Haba Salim haka muka yi da kai? Mai yasa kamin abinda ka san ba zan iya jurewa ba? Har alk'awari kamin na zaka zo gida ka sameni, yau kwana nawa kenan da yin maganar?"

"Amma ai da kin k'ara hak'uri ba sai kinzo ba, zanzo ne aiyuka sun min yawa, yanzu haka zaman nan da kika ga nayi aikin Dad nake. Bana so kina biyoni gida."

Yayi maganar ne yana dafe da kanshi, dan yana ganin Farida takura ce a rayuwarshi.

"Salim dole ne na biyoka, tun d'azun nake kiranka wanda ban san iya adadin kiran da na maka ba, amma kak'i d'auka a k'arshe ma kashe wayan kayi gaba d'aya, tunda na damu da in ganka ai dole in zo."

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana mai furta.

"Farida ya kike so inyi? Kinga zauna muyi magana ta fahimta, na tabbata zaki fahimceni."

Samun wuri tayi ta zauna tana mai kallonshi tare da sauraran abinda zai fad'a mata.

"Farida..!" Ya ambaci sunanta idonshi na kanta, itama haka k'ura mashi ido tayi, wanda ya bashi damar ci gaba da maganar da zaiyi.

"Ba zan aureki ba, ina so ki zauna a gida ki natsu har ranar da Allah zai kawo maki miji na gari. Ina da wadda nake so na aura, a tsarin rayuwata bani da burin aje mata biyu ko sama da haka, d'aya ta isheni. Dan haka kisa ma zuciyarki salama ki natsu duk ki aje abubuwan da kike ko zaki samu miji na gari, dan bana tunanin cikin wad'anda kike mu'amala dasu zasu aureki. To sai ni ki takura ma rayuwata a kan sai na aureki? ban ta'ba 'bata 'yar kowa ba, ban zama fasik'i mazinaci ba, dan haka ba zan auri wadda na san mazinaciya bace. Dan haka tashi ki fitar min a d'aki kada in sake ganin k'afarki ta tunkaro inda nake."

Kallo take mashi mai cike da mamaki, wanda tuni hawaye ya wanke mata fuska, ji take zuciyarta tayi mata nauyi, in banda bugawa ba abinda zuciyarta take, da k'yar ta iya bud'e bakinta ta saita yanayinta ta fara magana.

"Salim dama akwai ranar da zaka iya jifana da irin wannan bak'k'en kalaman nan marasa dad'in ji? Tunda har ka san haka halayena suke ba masu kyau ba, mai yasa ba zaka bini da addu'a akan Allah ya shiryeni ba, sai dai ka bini da bak'ak'en maganganu. Kaima baka wuce Allah ya d'aura maka ba, ni kaina ba a son raina nake aikata haka ba, kada ka manta kana da k'anwa idan Allah ya jarabceta da halin dana tsinci kaina ya zaka yi da ita?"

"To bari kaji in fad'a maka Salim. Ko ta halin k'ak'a sai na mallakeka, sai dai kayi duk abinda zaka yi. Wadda make ikirarin kana so, dole ka rabu da ita."

Mik'ewa yayi cikin zafin nama ya finciketa yayi waje da ita tare da maida k'ofar ya rufe yana mai sa key a jiki, komawa yayi ya zauna had'i da dafe kanshi da yaji a lokaci guda ya sara mashi. In banda zafi ba abinda zuciyarshi take, ji yayi ranshi ya 'baci.

"Ya zama dole na d'auki mataki a kanki."

Kukanta ya fara ji a jikin k'ofar tare da maganarta.

"Dan Allah Salim ka bud'e min, kayi hak'uri ka taimaka min, son da nake maka zai iya illatani, nafi sonka fiye da raina Salim. Kada ka kujeni, kai ne rayuwata, gujemin tamkar rabuwa da numfashina ne."

Fashewa tayi da kuka mai tsuma zuciyar mai saurare. Mik'ewa yayi ya fara taku a hankali yana mai jin zafin kukan da take. Bud'e k'ofar yayi wanda ya bata damar d'agowa da idanunta da suka yi ja saboda kuka.

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now