*KUDIRINA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)
*46*
*Wattpad: Ayshatmadu*
*** ***
Haka suka ci gaba da rayuwarsu cikin gidan nan, duk da Karime na gidan tana d'ebe mata kewa, hakan bai hanata tunani ba. Tunani ya riga ya mata yawa, wanda a kullum idan tana zaune cikin kuka take.Muhammad shima yaci gaba da zuwa makaranta bashi da lokacin kanshi.
*** ***
Kallonta yake a tsanake da nuna tausayawa. Dogon ajiyar zuciya ya sauke kana yace."Haba Hajiya sau nawa zan fad'a maki ki daina wannan tunanin, ba a son tunani ga mai ciki. Kina gani fa jininki ya hau sosai, ki duba kiga yanda kika kumbura kuma ako yaushe zaki iya haihuwa, kina so kema ki rasa rayuwarki ne d'anki ya shiga gararin rayuwa?"
Hawaye ne ya zubo mata, yayin data sa hannu ta share hawayen tana mai girgiza mashi kai.
"To kiyi ha'kuri ki rungumi 'kaddara, na san d'acin mutuwa sosai, amma ba yanda zaka yi da hukuncin Allah duk yanda ya tsara maka haka zaka amsheshi hannu bibbiyi. Idan har kika ci gaba da sama ranki damuwa akwai matsala, saboda ina tausayin d'anki."
Cikin damuwa tace.
"Insha Allah Doctor zan kiyaye."
Nan ya rubuta mata wasu magunguna, saida ta siya sannan ta wuce gida.
*** ***
Cikin haka ko ta fara na'kuda cikin dare, wanda kafin suje asibiti duk ta gama galabaita.Gaba d'aya Karime duk ta gama rud'ewa.
Shi kanshi Muhammad ya kasa barci, yana tsaye kan mahaifiyarshi. Waya Karime ta d'auka ta kira Mallam Musa cikin rud'ewa take fad'a mashi halin da Mommy Amina take ciki.
Ai neman barcin yayi ya rasa, haka ya fito cikin dare ya buga ma wani ma'kwabcinshi mai napep, yana fitowa yace.
"Mallam Musa lafiya na ganka cikin dare?"
"Taimaka min zaka yi matar marigayi mai gidana ne take na'kuda, gashi tana cikin mawuyacin hali."
"Allah sarki! Bari na shiga na fito."
Haka ya shiga ya fito suka tafi, suna isa fito da ita kawai suka yi suka wuce asibiti, dama tuni Karime ta had'a kayan haihuwan.
Suna isa nurses suka amsheta suka shiga da ita ciki, na'kudar take amma haihuwa ta'ki zuwa, duk ta gama galabaita, dole suka lalubo Doctor Idris, haka ya fito cikin dare ya taho dan tunda aka fad'a mashi mai na'kudar ya san tana da bu'katar taimako.
Shi kanshi ganin halin daya taddata ba 'karamin tashin hankali ya shiga ba.
Ganin har safiya tana abu d'aya ya yanke hukuncin yi mata C.S.
Gashi kuma ya gwadata yaga har yanzu jininta bai sauka ba, gaba d'aya ya shiga rud'ani ya rasa mai ke mashi dad'i, duk dauriya irin tashi saida ya zubda hawaye, tsaye kawai yake a kanta yasa ma sarautar Allah ido.
Salati yaji ta fara tare da yin wani nishi mai 'karfi, sai ga 'ya ta fad'o. Yayin da ita kuma rai yayi halinsa.
Bakinshi ne yaci gaba da ambaton.
"Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un! Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un!!"
Rungume yarinyar yayi cikin jini, yana 'kara ambaton Allah.
Fashewa yayi da kuka yama kasa yin komai.
D'aya daga cikin nurses d'in ne tayi 'karfin halin amsar yarinyar daga hannunshi dan su kimtsata.
Su kansu cikin tashin hankali suke ciki.
Samu yayi ya fita cikin tashin hankali ya sanar dasu rasuwar Mommy Amina.
Sallallami suka fara jerowa, yayin da Muhammad ya saki kuka yana ambaton Mamanshi.
Ganin yanda yake kuka ba wanda bai tausaya mashi ba a asibitin.
Fito da jaririyar akayi aka mi'ka masu, Muhammad amsarta yayi ya 'kura mata ido, sai kuma ya rungumeta ya fashe da kuka.
Kowa na wurin idan ya kalli halin da Muhammad yake ciki sai ya tausaya mashi.
Doctor Idris da kanshi yasa motar asibiti ta d'auki gawar Mommy Amina ta kai gida, su kuma suka tafi a motarshi.
Mallam Musa da kanshi yaje har gidansu Baba Salisu ya sanar dasu rasuwar Mommy Amina.
Haka suka d'ungumo cikin shiga ta alfarma suka iso gidan. Wanda tuni har an gama shiryata dan kaita gidanta na gaskiya.
Nan kuma Muhammad ya 'kara rud'ewa da kuka, kukanshi shike sa wasu kasa jurewa har sai sun zubar da hawaye, Karime ce ta ri'koshi tana lallashinshi.
Ga yarinya ya ri'keta a hannunshi, daya rungumeta sai ya 'kara fashewa da kuka.
Ya rasa a yanzu mecece makomarshi shida 'kanwarshi da suka rasa iyaye a lokacin da suke da bu'katarsu.
Haka yana ji yana gani aka d'auki mahaifiyarshi aka tafi da ita gidanta na gaskiya, ji yayi duniyar ta mashi zafi, ji yake baya bu'katar ganin 'yanuwan mahaifinshi.
Kuka sosai yake wanda duk mai imani sai ya tausaya mashi.
Ba yanda Karime bata yi ba dan ya bata yarinyar amma ya'ki bata, duk wanda yazo dan ya amsheta ya'ki ya bada.
Har aka dawo kai mahaifiyarshi yana nan zaune kamar zautacce.
Mallam Musa ne yazo ya du'ka kusa dashi yace.
"Muhammad kawota ka samu kaci abinci ka huta, kaga tunda aka haifeta take hannunka."
Cikin kuka yana girgiza kanshi yace.
"A'a ba zan bama kowa ita ba, bana so na rasata kamar yanda na rasa iyayena, ina so na rayu da ita. Mallam Musa na rasa iyayena har abada so kake itama inyi sakaci da rayuwarta?"
'kara fashewa yayi da kuka. Yana murgina kanshi jikin 'yar jaririyar.
Mallam Musa cikin zubda hawaye yake ambaton.
"Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un!"
Yaro 'karami ji yanda yake zaro magana.
Baba Salisu da suke tsaye kanshi yace.
"Wai kai Muhammad ba magana ake maka ba?"
Cikin kuka ya d'ago idanunshi da duk sun gama kumbura yace.
"Ba wanda zan bama ita, bana so na rasata, na fad'a maku bana so na rasata."
Ya idasa maganar cikin d'aga murya.
Kukan ya 'kara fashewa dashi, wanda yafi wanda yake yi, magana ya fara cikin kuka.
"Mallam Musa ka taimaka min kace ma kowa ya tafi tunda an kai Mommy na, bana son ganin kowa a gidan nan, bana so su tafi kowa ya tafi.
'kara fashewa yayi da kuka mai tsuma zuciyar mai saurare.
Dogon ajiyar zuciya ya sauke. Kana yace.
"To naji Muhammad kowa zai tafi ka daina kukan haka."
"Mallam Musa jiya i yanzu ina tare da Mommy tare muka ci abinci muna fira."
Kwantar da kanshi yayi jikin Mallam Musa yana share hawayenshi.
'Kara rungumeshi Mallam Musa yayi a jikinshi yace.
"Kayi ha'kuri Muhammad lokacinta ne yayi ba zata tsallake ba sai ta tafi, kaide kawai kaci gaba da binsu da addu'a."
Sawa yayi Karime ta had'a mashi tea mai kauri ta kawo mashi tare da dankali da wata ma'kwabciyarsu ta kawo yanzu. Ajewa yayi yace.
"Mallam Musa baby bata ci komi ba, wadda zata bata nono ta sha ta rasu. Nima ba zan iya cin komai ba ita bata ci ba."
"Haba ka daure kaci, ai kaga tana barci ne data tashi za a bata nata."
Da 'kyar aka lalla'bashi ya d'an sha tea da dankalin kad'an.
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.