K'UDIRINA Page 49

103 19 4
                                    

*KUDIRINA*

       ®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

       ©
*EASHA MD*

*Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)

         *49*

     *Wattpad: Ayshatmadu*

Lokaci ne keta tafiya, yayin da al'amuran Inna suka canza, a kullum gani take Muhammad ya sangarta Islam.

Inda ita kuma taji gaba d'aya sun fita a ranta, duk da 'kan'kantar Islam hakan bai sa ta kasa wahalar da ita ba, koda kuka take nan zata tsallake ta barta ba tare da tabi ta kanta ba, hatta wanka sai idan ya dawo sannan ya mata, ko in Allah yasa Naja'atu na gidan ta kan d'an kula da ita.

Kamar yanda yanzu Inna ta saba da rashin kula da Islam, yau ma haka ta kasance.

Tunda ta tashi yau da zawo ta tashi, da 'kyar Mallam Musa ya lalla'ba Muhammad ya yarda ya tafi makaranta saboda suna exams.

Zaune take duk jikinta ba 'kwari wani kashin ya kufce mata a nan.

Inna ta taho da sauri had'i da murd'e kunnan Islam tace.

"Yanzu dan tsabaragen wula'kanci da kika iya, kina jin kashi ba zaki iya mi'kewa ki nemi wurin da ake yi ba, ni ba ruwana da 'kan'kantarki zaneki zanyi, dan ba zan d'auki iskancin kashi a jiki ba. Kika wani kafeni da ido kina kallona."

Ta idasa maganar tare da kai mata ran'kwashi a kai. Islam ta tsanyare da kuka.

"Zaki rufe min baki ko kuwa sai na zaneki a wurin? Sai dai ki jira d'anuwanki har sai ya dawo ya wanke maki, haka kawai muna fama da kanmu Mallam yaje ya jajibo mana wasu."

Sai faman fad'a take ita kad'ai, Islam kuwa in banda kuka ba abinda take yi, tunda ba a bigeka ba a hanaka kuka. Ga 'kudaje sai faman binta suke.

A haka har Muhammad ya taso ya taddata a haka, da sauri ya 'karaso wurinta ba tare daya damu da abinda ke jikinta ba, ya d'auketa ya rungume a jikinshi yana tambayarta.

"Islam meke faruwa aka barki haka a waje?"

"Nice nan na barta a wurin dan na isa, kaga tunda ka dawo sai ka tsaftace mata jiki dan ni ba zan iya ba."

Cewar Inna data fito cikin fad'a.

Kallonta yake cikin 'bacin rai yace.

"Amma Inna kashi tayi bai kamata a barta a haka ba."

"Eh ai kace haka tunda gani baiwarku ko? Nifa na gaji da ganinku a gidan nan, haka kawai muma muji da kanmu mana. Ko yanzu ka barta a gidan ta 'kara kashi haka zan barta dashi a jikinta koda ko kwana zata yi dashi. Nifa gaba d'aya kun takura min kun isheni."

Muhammad gaba d'aya ya gama zuciya, ji yayi gidan da wad'anda ke gidan sun fita a ranshi.

Ji yayi jikinshi yayi sanyi zuciyarshi na tafasa, zuwa yayi ya aje Islam ya d'ibi ruwan zafi wanda tana fad'an kada ya d'iba hakan baisa ya saurareta ba, dan a zuciye yake.

Wanka ya mata sosai ya samu zani ya goyata, kana ya dawo ya wanke duka kayan data 'bata dana jikinshi.

Shanyasu yayi ya koma d'aki ya shiryata ta fito tsaf-tsaf da ita, kayansu ya jawo ya fara had'awa, wayar Mommy ya fiddo ya dawo dashi saman kayan, saida ya gama tsaf ya fito dasu tsakar gida, hali na iska kuma kayan daya shanya ba masu nauyi bane, sai gashi har sun sha iska, d'aukosu yayi ya linke ya tura cikin kayansu.

Fitowa yayi ya tadda Inna zaune, kallo ya bita dashi kana yace.

"Inna zamu bar maki gidanki, ban san muna takura maki ba, da bamu zauna a nan ba, 'kaddara ce ta rabamu da iyayenmu, da ace anyi shawara damu ba zamu yarda a rabamu dasu ba. Koda kika yi haka ban ji haushinki ba, saboda dangin mahaifinmu su suka fara gudunmu, kinga dan wani ya gujemu ba zamu ji haushi ba."

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now