K'UDIRINA

266 16 1
                                    

*K'UDIRINA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Dedicated to Maryamerh Abdulrahman* (Kwaiseh)

    
              *20*

  Farkawa yayi ya ganta zaune idonta na kanshi. K'ok'arin mik'ewa yake, da sauri ta mik'e ta rik'eshi tana fad'in.

"Kabi a hankali Yaya ba k'arfi a jikinka."

D'an yamutsa fuskarshi yayi yana kallonta. Yanayinshi zaisa ka gane yana jin zafin jikinshi.

Cikin damuwa da tausayi Islam tace.

"Sannu Yaya."

"Yauwa Islam! Ina makarantar baki tafi ba?"

"Yaya taya zan iya tafiya in barka, alhalin tun jiya kake kwance kana barci ba tare daka farka ba, ka san ba zan iya zuwa ba."

Cikin kulawa ya dubeta da k'yar.

"Kada ki damu na warke ki tafi ko."

Cikin kuka tace.

"Dan Allah ka k'yaleni ba zan iya tafiya ba, lafiyarka ya fiye min bak'in cikin C/O d'in da zan samu dan haka ka k'yaleni."

Yanayin yanda kanshi ke ciwo yasa yayi shiru, dan baya so ya cika magana. Runtse idonshi yayi, ba yanda zai yi haka ya hak'ura ya k'yaleta.

zama tayi tana jinyarshi, misalin k'arfe goma Doctor ya shigo ya dubashi. Sosai yanzu yake jin damar jikinshi, dama buguwar da yayi ne.

Wanda ya bigeshi ne ya k'ara dawowa dan dubanshi. Sosai yaji dad'in samunshi zaune, alamu ya nuna ya samu sauk'i.

Cikin farin-ciki yake cewa.

"Masha Allah! Jiki yayi sauk'i."

"Sosai kuwa dan kad'an nake jin ciwon jikin, kan ma da yake min ciwo ya sauka. Allah ma ya tak'aita wahala."

"Gaskiya kam, Allah ya k'ara tsarewa."

"Ameen."

Shirin tafiya yayi. Hannu yasa a aljihu ya ciro dubu biyar.

"Gashi kuyi hak'uri da wannan ko da zaku buk'aci wani abin."

Godiya Yaya Muhammad ya mashi. Sannan ya tafi.

Bashir yazo dubashi, ganinshi zaune yasa shi murna. Mik'a ma Islam abincin daya kawo masu yayi, tasa ma Yaya Muhammad. Sai da taga yaci sannan ta damu damar ci itama.

*** ***
Zaune yake kan kujerarshi yana rubuce rubuce. Shigowa suka yi suna gaidashi cikin girmamawa a matsayinshi na malaminsu.

Kallo ya bisu dashi d'aya bayan d'aya fuskarshi a d'aure.

"Kada Wanda ya bani kud'i ko wani abu da sunan cin hanci, dan ni bana taimakon students. Idan mutum zai dage yayi karatu ya dage abinda kuka rubuta shi zaku gani."
Ya maida kanshi jikin kujera ya rufe idonshi.

Wucewa sukayi ba tare da sun furta wata magana ba, dan duk wani d'alibi dake cikin makarantar ya san waye S Fulani baya amsar komai a hannun d'alibi sai dai k'ok'arinka ya k'waceka a hannunshi, dan baya son ganin d'alibi na wasa, idan har aka ga ya bada C/O, to tabbas ka fad'i ne.

Tun fitarsu idonshi yake a rufe, zuciyarshi ce ta fara tambayarshi.

"Ina take? Mai ya hanata zuwa bayan ta san abinda suke? Ya Allah kasa lafiya take. Mai zai dameka da halin da take ciki tunda ta san exams suke ta kasa zuwa?"

Dogon ajiyar zuciya ya sauke. Wanda har yanzu idonshi yana a rufe, ji yayi gaba d'aya ya damu da rashin zuwanta tayi exams d'in subject nashi a yau.

***
Waye S Fulani? Kun san asalin sunanshi Salim Ahmad d'anfulani. Ya samo asalin sunan S Fulani ne a wurin abokanshi, wanda sunan ya bishi. Asalinsu 'yan garin Yola ne aiki ne ya zaunar da mahaifinshi garin Kano, su biyar iyayansu suka haifa Aunty Salaha itace babba, sai Salim Munnir da Naseem wanda suka zamo tamkar 'yan biyu sai autarsu Safeenat. Sun taso cikin jin dad'i da kulawar iyaye, wanda suke nuna masu k'auna k'arara. Suna da ilimin addini dai-dai gwargwado, wanda kuma Salim ya dokesu dan ya tsaya tsayin daka ya nemi ilimin addini. Wanda har yanzu da girmanshi yana kan nema, tunda ba a girma da neman ilimi.

Suna da natsuwa da hankali, sai dai kuma sun taso sun d'auki ak'idar iyayansu na k'in talaka. Sai dai Salim ya ciri tuta a cikinsu, ya fidda zakka, ya kasance yana ganin darajar d'an Adam a duk yanda yake. Bayi da k'yamar mutum, kowa nashi ne, tun yana k'arami baida abokai sai 'ya'yan talakawa, iyayanshi su buga amma baya ji, komi ya samu su zai kai mawa. Duk inda yaji ana naiman taimako, sai ya nemo ya basu, koda shi kad'ai ne a hannunshi zai mik'a, tun bai mallaki hankalinshi ba. Zama yake cikin talakawa yana ganin yanda suke tafiyar da lamuransu wanda zaisa yayi iya bakin k'ok'arinshi na ganin ya tallafa masu, duk wani kud'i da zai samu kansu zai k'arar dasu.

Tun tasowarshi ya tashi cikin   natsuwa, bai damu da hayaniya ba, ba ruwanshi da hidimar kowa nashi kawai yasa a gaba. Tun yana yaro bai yarda abinda zaiyi yasa mai aiki ta mashi ba, zai iya shiga yayi abinda yake so da kanshi ba tare daya k'untuka ma wani ba a cikin ma'aikatan gidansu. Haka dai-dai da driver na gidan bai 'bata lokacinshi a kan sai ya kaishi wani wuri, idan har fita dashi za ayi ya gwammace ya kaisu da kanshi ba tare da sun nemi driver ba. Iyayanshi sun rasa yanda zasu yi dashi akan ya rabu da wad'anda yake tare dasu ba sa'o'inshi bane. Amma ya toshe kunnanshi sabgarshi yake shi d'aya ba tare da ya nemi shawararsu ba.

Idan ka cireshi a gidan gaba d'ayansu halayansu d'aya. Ya rasa ta yanda zai fahimtar dasu su gane mahimmanci da darajar da mutum yake dashi a duk yanda yake. Wannan shine tak'aitaccen tarihin Salim S Fulani.

*** ***
"Islam yanzu kina ji kina gani kinyi asarar exams d'inki na yau, banji dad'i ba."

"Kada ka damu guda d'aya ne kawai mukayi shiyasa ban wani damu ba sosai."

Girgiza kai kawai yayi. Dole tasa ya rok'i Doctor ya sallameshi dan ya san idan har bai koma gida ba tana ganinshi kwance ba zata school ba. Haka suka dawo gida jikinshi Alhamadulillah.

Bashir ne ya shigo gidan da sallamanshi. Amsawa su kayi.

"Kai shine ka gudo gida ba tare da ka bari kaga yanayin jikinka ba?"

"Kai dai bari wannan dawowar na dole ne, ka san rigimar wannan 'yar k'anwar tawa."

D'an murmushi yayi yace.

"Ai kai da Islam sai Allah. Allah dai ya mana tsawon rai."

"Ameen Ya rabbi."

Dubu uku ya ciro cikin kud'in da mutumin nan ya bashi, ya mik'a ma Bashir kud'in.

"Gashi waya nake so ka duba ma Islam 'yar Nokia haka ta d'an rik'e."

Waro idanu tayi. "Yaya muna cikin wannan halin yaushe zan bari ka saya min waya."

"To ai yaci ki rik'e waya, kin zama 'yan mata ai."

Dariya tayi cikin jin dad'i tace.

"Na gode Allah ya bud'a maka."

"Ga wani Sim d'ina da bana amfani dashi idan kina so in d'auko maki."

"Ina so mana."

Bashir mik'ewa yayi ya fita dan siyo mata waya.

Sosai taji dad'i da wayar da za a siya mata. Dan tana so itama taga ta rik'e 'yar wayan nan da kowa ke rik'ewa har da wad'ada basu kaita ba.

Suna nan Bashir ya dawo da waya a hannunshi, mik'a ma Yaya Muhammad ya fara yi. Gani yayi fuskarshi d'auke da murmushi ya mik'a mata.
"Sai ki samu kisa charging wayan."

Tasa hannu biyu ta amsa cikin murna.

Tana mai k'ara gode mashi.

Bata tashi damuwa ba sai da dare yayi ta tuna da exams d'insu, tuna S Fulani yasa hankalinta ya tashi, tabbas ta san tana cikin yanayin tashin hankali. Rok'on Allah take ya d'aurata a kanshi su rabu lafiya dashi.

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now