*K'UDIRINA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Dedicated to Maryamerh Abdulrahman* (Kwaiseh)
*41*
Mintuna kad'an sai gasu sun shigo d'akin, da fara'a ya tarbesu.
Yayin da nasu fara'ar ta dole ce, ba yabo ba fallasa.
"Yaya kune da yamma haka?"
"Baka so ganinmu ba ko a irin wannan yanayin?"
Yaya Salisu ya bashi amsa yana mai binshi da wani kallo da bai san na miye ba.
"Haba Yaya ina da kamarku ne a duniyar nan? Bana so kuna fad'in irin wannan maganar."
Yaya Salisu ya dubeshi tare da cewa.
"To mu ba wannan ya kawomu ba, ka san dai mu ba ilimin boko muka yi ba. Dan haka kud'in da kake bamu baya isarmu, yanzu muna bu'katar kud'i naira na gugan naira har miliyan biyar saboda mu zauna da 'kafafuwanmu ba sai munzo muna maula a wurinka ba kana jin haushinmu. Gara ka sallamemu gaba d'aya mu 'kyaleka."
Dafe kai Farouk yayi tare da fad'in.
"Inna lillahi wa Inna ilaihir-raji'un! Yaya har miliyan biyar? Wai mai kuka d'aukeni ne haka? Injin buga kud'i da kun nema kuzo ku bud'e ku d'iba?"
Dogon ajiyar zuciya ya sauke. Yayin da su kuma suka saki baki suna kallonshi cikin mamaki.
Baba Salisu ya dubeshi tare da cewa.
"Faruku ni na san za a rina, na tabbata akwai ranar da zaka nuna gajiyawarka a kanmu. To bari kaji in fad'a maka kud'i ya zama dole ka bamu, ba shawara muke baka ba ko muke lallashinka, umurni muke baka ka bamu miliyan biyar. Ni a ganina ai mun nemi kud'i kad'an shine har zaka tada hankalinka."
Dafe kanshi yayi da hannunshi wanda yake mashi ciwo a lokaci guda.
Amina ce ta shigo ri'ke da tray a hannunta wanda ta d'aura had'ad'd'an zo'bon data had'a, sai snacks wanda bata tsaya jiran masu aiki suyi ba, dan duk da kud'in da suke dashi bata zama ta lan'kwashe 'kafa tace komai sai an mata. Ta dire a gabansu tare da kallon Farouk tace.
"Habibty ka basu kud'in ba wani abu bane, idan suna so kawai ka rin'ka mi'ka masu ka huta."
Cikin daka tsawa Baba Salisu ya nuna mata yatsa tare da cewa.
"Ke bada ke muke magana ba da zaki saka mana baki, ke zaki bashi umurnin ya mana ko mu zamu bashi umurnin ya mana? To bari kiji in fad'a maki, dukiyar Faruku tamkar namu ne, shi yayi wahalar tarashi amma mu zamu mora baku ba, dan sai yanda muka yi dashi."
Kallonsu take mai cike da takaici, wai mai suka d'auki kansu haka ne? Duka rayuwar rayuwar duniyar nawa take?
Faruku ne ya dafe 'kirjinshi tare da fad'owa 'kasa daga kan kujera.
Da sauri Amina tayi kanshi tana kuka tare da girgizashi tana fad'in.
"Habibty ka tashi, mai ya sameka haka?"
Wani irin nishi yake sai kace ranshi zai fita. Su kam tsaye suka yi suna kallon ikon Allah ba tare da sunce komai ba.
Baba Salisu da zuciyarshi tafi 'ke'kashewa ya kasa 'boye murnarshi na ganin halin da yake ciki, dan sai da ya nuna murnarshi a fili.
Ganin yanayin da yake ciki, yasa ta fita waje da gudu tana kuka cikin tashin hankali take kiran su Mallam Musa, da sauri suka 'karaso inda take cikin tashin hankali.
Cikin rud'u take magana.
"Dan Allah ku taimaka min Daddy'n Muhammad ne ya fad'i."
Tayi hanyar ciki, da sauri suka bi bayanta, duk ma'aikatan gidan suka shigo ciki suna mai jimamin halin da suka ganshi.
Da taimakon Mallam Musa suka sa Farouk a mota suka yi asibiti dashi.
Suna isa da sauri aka shiga dashi emergency, likitoci ne suka tsaya a kanshi dan ceto rayuwarshi.
Har a lokacin in banda kuka ba abinda Amina take yi, har yanzu
Cikin tashin hankali take, ita kanta in banda d'aci ba abinda zuciyarta take mata.Had'a kanta tayi da gwiwa, in banda hawaye ba abinda take zubarwa.
"Mai yasa wad'annan mutanan suke son ruguza mana rayuwarmu mai cike da jin dad'i? Idan har wani abu ya samu mijina ba zan ta'ba yafe maku ba."
Magana take tamkar zautacciya. Wata nurse ce ta iso wurinta tare da cewa.
"Hajia kizo Doctor na son ganinki."
Da sauri ta mi'ke dan binta, dai-dai lokacin da su Baba Salisu suka iso asibitin.
Ko kallon inda suke bata yi ba tabi bayan nurse d'in.
Suna shiga tun kafin ya bata umurnin zama ta nemi kujerar dake fuskantarshi ta zauna fuskarta a kumbure saboda kuka.
Aje rubutun da yake yayi ya maida hankalinshi kanta tare da cewa.
"Hajiya Amina a iya binciken da muka ma Alhaji Farouk mun gano yana d'auke da ciwon zuciya, wanda ciwon ya d'an jima a jikin saboda tashin hankalin da yake yawan fuskanta. Ina so ku rin'ka kula da abinda yake so, ku kiyaye tashin hankalinshi da 'bata mashi rai, idan ba haka ba zuciyarshi zata iya bugawa wanda zai iya rasa rayuwarshi."
"Na shiga uku! Wayyo Allah na.!"
Ta fad'a cikin tashin hankali.
"Kada ki damu, ba abin tashin hankali bane, kawai dai ku kiyaye abinda na fad'a maku shike nan."
Ya fad'a mata cikin magana mai kwantar da hankali.
Share hawayen daya zubo mata tayi, mi'ka mata wata takadda yayi tare da cewa.
"Ga wannan magungunan da zaku siya mashi ne."
Amsa tayi ta mi'ke dan zuwa siyan maganin.
Tana fita suka tareta. Baba Nasiru ne yayi magana.
"Mai likitan yace?"
Cikin zubda hawaye tace.
"ciwon zuciya ke damunshi wanda likitan ya tabbatar da idan har ba a daina tada mashi hankali ba, zuciyarshi zata iya bugawa."
"Haka yace kuma?"
"Eh! Ina mai ro'konku da Allah da ku rin'ka binshi a hankali, zai rin'ka maku duk abinda kuke so."
Ba tare data tsaya jin abinda zasu ce ba ta bar wurin ta tafi dan tafiya siyo maganin.
Baba Salisu ya dubi 'yanuwanshi da murna yace.
"Shikenan abu yazo da sau'ki, idasashi da zamuyi mai sau'ki ne ba tare da munsha wahala ba."
"Sosai kuwa Yaya Salisu."
Cewar Baba Sani dake dariya.
"Ai ba zai ta'ba rayuwa da dukiyarshi ba, dan mu ya tara mawa bashi da iyalanshi ba. Ka saurari mutuwarka yau ko gobe."
Tofa! Kamar ku keda rayuwarshi, ai rayuwarshi ba hannunku yake ba.
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.