'KUDIRINA Page 44

89 9 0
                                    

'KUDIRINA*

       ®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

       ©
*EASHA MD*

*Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)

     *44*

  *Wattpad:Ayshatmadu*

Tama kasa ce masu komai, sai kanta data du'kar 'kasa hawaye na sauko mata. Bata san sadda kuka ya 'kwace mata ba.

Baba Salisu yace.

"Ki gama kuka dole ne ki bamu dukiyar yaro mu ri'ke mashi, dan ba zamu bar maki ma'kudan dukiyar da bamu san yawanshi ba a hannunki.."

Juyawa yayi ya kalli Barrister Isma'il dake zaune yaci gaba da magana.

"Barrister kaine duk wasu shaida ta dukiyar Faruku ke hannunka, muna da bu'katansu."

D'an gyaran murya yayi gami da gyara zamanshi yace.

"Da kunbi ta maganar Hajiya Amina a bari ta haihu sai a raba gadon, sai inga hakan zaifi saboda wannan dukiya ta marayu ce."

Baba Sani yace.

"In banda abinka Barrister, ai da kai da kaya duk mallakan wuya ne. Dan haka ka dun'kula mana dukiyar marayu shine magana."

Baba Salisu yace.

"Ai badawa ma ya zama dole, saboda mu keda iko akan komi na Faruku."

Goggo ta d'aura da cewar.

"Wai da kake maganar dukiyar marayu, dukiyar marayu. Lokacin da muka yi d'awainiya da Faruku baka san munyi ba, Faruku jininmu ne shi muna da ikon da zamu ri'ke dukiyarshi ba tare da mun barshi hannun wani ba."

Barrister ya d'anyi jim kad'an, kana yace.

"Naji duk abinda kuka ce, amma ina so ku d'an bani lokaci."

Baba Salisu yace.

"Wane lokaci zamu baka? Ai alfarma d'aya zamu maka, gobe muke bu'katar komai."

Mi'kewa yayi tare da cewa.

"Shikenan sai kun jini goben, ni zan wuce ina da aikin yi yanzu."

Tafiya ya fara yi had'i da masu sallama.

Dubanta Baba Salisu yayi tun daga sama har 'kasa yace.

"To mu zamu tafi, gobe muna nan dawowa sai ki shirya tarbar abinda zamu zo maki dashi."

Mi'kewa suka yi gaba d'aya suka fita a d'akin.

Had'a kai wuri guda suka yi ita da Muhammad, in banda kuka ba abinda suke yi.

              ***  ***
"Barrister muna bu'katar duk wasu kadara daka sani wanda Faruku yake dashi. Kai kanka Barrister na san ba zaka 'ki wasu kaso na arzi'ki daya bari ba, kaima dole ka yagi rabonka, ka san fa dukiya ba abin gudu bace, kai da kanka nan gaba zaka yi alfahari dashi."

Shiru Barrister Isma'il yayi yana nazari ba tare daya iya furta komai ba.

Dafashi Baba Salisu yayi tare da cewa.

"Ko ya ka gani? Zan baka kaso mai tsoka a ciki, dan ina mai tabbatar maka da dukiyar Faruku Allah ya riga daya sa mata albarka, kullum hauhawa take, kuma na tabbata zata ci gaba da hawa ba tare data gurguce ba, tunda ci gaba da juyashi zamuyi ba tare da mun aje muna ci ba, bare ya 'kare mu talauce."

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kana yace.

"Alhaji ba wai bana so bane, Amma ina jin tsoron abinda zaije ya dawo ne."

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now