'KUDIRINA Page 43

100 7 2
                                    

*'KUDIRINA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)

*43*

"Amina mai ya faru haka aketa kuka a cikin gida?"

D'agowa tayi da hawaye cike a fuskarta tace.

"Allah ne ya amshi ran bawansa cikin hukuncinsa, dan lokacinshi ne dama yayi."

Gaba d'aya juyawa suka yi suna kallon juna sai kace wad'anda basu san abinda ya faru ba.

Cikin rud'ewa Baba Salisu ya fara tafiya dan zuwa d'akin Daddy Farouk, binshi suma suka yi a baya.

Bayan sun shiga d'akin suka 'kara tabbatar da tabbas ya rasu. 'ko'karin sauko dashi 'kasa suka fara yi, Mommy Amina ce ta shigo d'akin dan ganin mai zasu 'kara shiryawa.

Juyowa Baba Nasiru yayi cikin damuwa yace.

"'Kasa zamu saukeshi."

Binsu dai tayi da kallo ba tare da tace masu komai ba.

Baba Sani yace.

"Dama mai za a tsaya jira tunda jin dad'in duniya ta 'kare mashi."

"Sai kuma na lahira da zaije ya tadda ba wadda tafi ta duniya jin dad'i, su wad'anda suka za'beta sai su zauna suyi gadinta."

Mommy ta basu amsa cikin tsantsar tsanarsu.

Kallon juna suka hau yi cikin nuna zargin kota gano komai ne.

Baba Salisu yace.

"Wannan haka yake, ku kira gida ku fad'a masu da sauri a samu a shiryashi a kaishi gidanshi na gaskiya."

Umurninshi suka bi.

Kafin kace mai gida ya cika ma'kil da 'yanuwa da abokan arzi'ki, sanin shi babban mutum ne yasa aka jinkirta kaishi aka bari sai washegari.

Iyayanta ta kira ta fad'a masu rasuwar Daddy Farouk, Ammi mata gaisuwa tare da cewa.

"Idan kin haihu sai ki taho ko?"

Cikin kuka da damuwa tace.

"Ammi ba zaku zo bane? Mijina ne fa ya rasu."

"Kiyi ha'kuri Amina ba zamu samu zuwa ba, kinga tunda kin kusa haihuwa sai ki taho gaba d'aya. Duk zasu kiraki su maki gaisuwa."

Hawaye ne ya gangaro mata tace.

"Shikenan Ammi na gode."

Katse wayar tayi ta kifa kanta kan cinyarta, wani irin kuka ta fashe dashi, wanda duk wanda ke wurin saida ya tausaya mata.

Samun wannan dama yasa Mommy Amina tasa aka ci gaba da sauke mashi Al'qur'ani, haka aka kwana ana saukar Qur'ani a gidan

Ganin ta kasa barci shi ya bata damar d'auro alwala tayi ta doka sallah tana mai ro'ka ma mijinta gafara da nema mashi rahama a wurin Allah.

*** ***
Washegari an gama shirya Daddy Farouk dan kaishi gidanshi na gaskiya, nan gida ya 'kara kaurewa da kuka. Hatta Muhammad yaro dashi haka ya kifa kanshi jikin mamanshi yana raska kuka.

Haka aka d'aukeshi aka fita dashi, duk wanda ke wurin kuka yake, sai 'kalilan wand'anda suke jiran hakan ta faru.

Su Mommy Amina kam kuka sosai take, yayin data rasa wanda zata jingina dashi daji d'uminshi. Sai ha'kuri ma'kwaftanta da wad'anda ke wurin suke bata. Gaba d'aya ji take duniyar ta mata zafi.

Da Ace yau 'yan uwanta sunzo data d'an ji sanyi a zuciyarta. To duk waigawan da zata yi ba wani dangi nata a wurin.

Abinci kanshi ta kasa ci, ba yanda ba ayi da ita taci abinci ba amma kwata-kwata bata son ganin abincin, kallo mutane d'aya bayan d'aya take tana ganin yanda suke ciye-ciyensu da firansu hankali kwance, yayin da ita kam duniyar ta mata zafi.

Lokaci zuwa lokaci hawaye ke sauka daga idanunta, wasu rayuwarsu take tunawa wanda shi ke sata hawaye ba tare data iya dakatar dasu ba.

Lokaci 'kan'kani duk ta fita a hayyacinta, shi kanshi Muhammad kallo d'aya zaka mashi ka tabbatar da yana cikin hali na damuwa da tausayawa.

Duk 'yanuwanta da mahaifinta sun kirata sun mata gaisuwa. Ba yanda ba tayi ba a kan suzo, amma fafur sun 'kiya, sun nuna mata ba zasu iya zuwa Nigeria ba. Sai dai sun nuna mata jimami da tausayawa na rashin mijinta.

*** ***
Haka aka ci gaba da zaman makoki, yau gashi har ya kwana uku da rasuwa. A yau kuma Mommy Amina tace tana so a gama zaman makoki ba sai an kai kwana bakwai ba.

Hakan yama su Baba Salisu dad'i dan dama sun 'kosa kowa ya kama gabanshi.

D'akin suka shigo gaba d'ayansu suka samu wuri suka zauna. D'aya bayan d'aya Baba Salisu ya rin'ka kallon wand'anda ke zaune cikin palour.

Gyaran murya yayi wanda yasa Muhammad ya 'kara ma'kalewa jikin mahaifiyarshi, dan sosai yake jin tsoronsu tun ba Baba Salisu ba.

"To kamar dai yanda kuka sani yau d'anuwanmu ya cika kwana uku da rasuwa, muna mai ro'kon Allah da yaji 'kansa da rahama, idan namu yazo yasa mu cika da imani."

Suka amsa da "Amin."

Yaci gaba da magana.

"Ke Amina Allah dai ya amshi ran mijinki, yanzu dai muna so ri'kon d'a ya dawo hannunmu tare da dukiyar da mahaifinshi ya bari, dan ba zai yuwu mu bar maki shi a hannunki ba."

D'agowa tayi ta kalleshi cikin ido tace.

"Gaskiya ba zan iya baku d'ana ba, ni zan ri'keshi da kaina."

Cikin fad'a Goggo tace.

"Yau ga ja'irar yarinya! Kin san dai mun fiki iko dashi koda kike ganin ke kika haifeshi dan haka.."

Baba Salisu ne ya katseta da cewar.

"Goggo ki barni da ita, dole ne ki bada yaron nan da dukiyarshi. Ni dama can na sani dukiyarshi kike so shiyasa kika aureshi, wama ya sani ko ke kika kashe mana d'anuwa munafu.."

"Ba ita ta kasheshi ba, kune kuka kasheshi."

Cewar Muhammad daya katse Baba Salisu.

Da sauri Mommy Amina ta rufe mashi baki tare da cewa.

"Kai Muhammad wannan wane irin magana kake haka?"

Baba Sani yace.

"Sharri zaka mana d'an yaro da kai?"

Amsa ya bashi yana mai kallonshi.

"Meyasa zaku ce Mommy ta kasheshi? Kuma sharri kuke so ku shirya mata.

Baba Salisu ne ya taso cikin zafin nama ya kai mashi duka, wanda zafin dukan yasa ya fashe da kuka tare da kwanciya jikin mamanshi wanda ita kanta bata san sanda hawaye ya zubo mata ba.

"Munafuka! Na tabbata ke zaki kitsa mashi wannan maganar, dan wannan d'an tatsitsin yaron ba zai iya furta wannan maganar ba. Dan haka ya zama dole ki bamu dukiyar yaro dashi kanshi mu ri'keshi."

Cikin kuka tace.

"Naji zan baku dukiyar nan ku ri'ke, amma ina so ku jira nan da wata biyu in haihu aga abinda na haifa, sai a kira malamin da zai raba gadon, saboda yau ma kwananshi uku da rasuwa amma kun fara maganar dukiyarshi."

Cikin jin zafi Baba Salisu yace.

"Ke ba wani jira da zamuyi, duk wani abu nashi mai muhimmanci da kika sani muna da bu'katarshi a yanzun nan."

Binshi tayi da kallo, kallo na tsana dan gaba d'aya bata son ganinsu a gabanta.

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now