*K'UDIRINA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)
*54*
*Wattpad: Ayshatmadu*
***
Zaune yake bakin gado ya kasa ko runtsawa, tunani barkatai ke yawo cikin zuciyarshi, taya zai yi ya ganar da Islam ne ta cire son Abdallah a zuciyarta?Taya za tayi ta gane rabata dashi da yake son yi ba dan bai 'kaunarta bane sai dan abinda zata je ta tadda a cikin family nasu?
Dafe kanshi yayi da yake sara mashi, mi'kewa yayi yaci gaba da zagaye d'akin yana jin takaicin abinda Islam ta mashi.
Komawa yayi ya zauna yana share hawayen daya zubo mashi.
Fatima ce ta farka ta ganshi zaune ya rafka tagumi. Mi'kewa tayi ta zauna tana kallonshi, ji tayi gaba d'aya tausayinshi ya kamata ganin halin da yake ciki, ta san soyayyar dake tsakaninshi da 'yaruwarshi, kullum son faranta mata yake.
Juyo da fuskarshi tayi gareta suna fuskantar juna, hannunta tasa tana goge mashi hawayen daya wanke mashi fuska tace.
"Haba sweetheart mai nake gani a idonka? Kuka bai kamaceka ba, Islam tamkar uba kake a gareta duk abinda ka umurceta a kai zata aikata ba zata ta'ba tsallake maganarka ba."
"Ta tsallake, ta tsallake fatima saboda har yanzu tana nan a kan bakanta na son auran Abdallah, Islam zata ga kamar bana 'kaunarta ne alhalin ba haka bane, ina guje mata ranar da zasu gane ko ita wacece domin kuwa duk sanda suka gane ba zasu barmu da ranmu ba bare har iyayenmu su samu addu'armu. Zasu sama ransu tunda mun girma zamu iya yin komai a kansu."
Fatima tace.
"Maganar da kayi gaskiya ce, amma ka zauna da ita kuyi maganar fahimta da ita ko Allah zaisa ta gane."
Furzar da iska yayi daga bakinshi yace.
"Kina jin abinda Doctor Hamisu yace fa dole mu guji 'bacin ranta taya zanyi magana da ita wanda zai sa ta fahimta alhalin da an mata magana sai ta zube ta fad'i 'kasa sumamma."
Ya idasa maganar da kuka. Jawoshi tayi jikinta tana lallashinshi kamar 'karamin yaro.
"Calm down my dear! Haba akan mai zaka zauna kana damun kanka? Islam ta tsani 'bacin ranka da damuwarka dan haka Insha Allah komai zai zo da sau'ki, yanzu ka koma ka kwanta kayi barci."
"Ba zan iya barci ba a halin yanzu." Mi'kewa yayi ya fad'a toilet ya d'auro alwala ya fito ya fara doka sallah yana mai ro'kon Allah.
***
Washegari ta tashi idonta yayi luhu-luhu saboda kukan da taci cikin dare, lokaci guda duk ta fita daga hayyacinta ta rame. Mi'kewa tayi ta zauna tsakiyar gadon ba tare data yi yun'kurin saukowa ba.
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.