*K'UDIRINA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Dedicated to Maryamerh Abdulrahman* (Kwaiseh)
*36*
*Wattpad@ayshatmadu*
Cikin takaici farouk ya furta.
"Haba Yaya duk abinda nake maku baku gani? Idan har zan biye abinda kuke min, da ban maku komai ba ku 'yan uwana ne, kune dolena banda kowa sai ku. Ku d'aukeni yanda na d'aukeku mana, maganar gida kuma ku bani nan da kwana biyu za a maku abinda kuke so tunda na gane abinda kuke fi so a tare dani."
Yaya Salisu yace.
"Dan zaka mana abu shine zaka zauna kana jero mana maganganu?"
Cikin washe baki Goggo ta furta.
"Kai Salisu manta da sannan maganar. Yanzu naji magana, amma kawai da ka barmu cikin bak'in gida, kai kana k'aton gida haka."
"Yanzu kuma Goggo ai magana ta wuce tunda za a maku gini mai kyau."
Cewar farouk tare da dafe kanshi.
Goggo Suwaiba ce ta dubeshi tana mai cewa.
"Ni kuma ya maganar jali? Saboda wancan daka bani ya karye."
Duban Amina yayi da take tsaye tana kallon ikon Allah yace.
"Habibty shiga ciki ki d'auko mata dubu hamsin ki bata. Ya kamata mu koma ciki tunda kun gama ganin wuri."
Tafiya shima ya fara suka bi bayanshi, yayin da Goggo Suwaiba ta fara magana.
"Haba Faruku! Yaushe dubu hamsin zai isheni? Wai mai yasa yanzu ka koyi mak'o ne dan da ba haka kake ba?"
"Kiyi hak'uri da wannan, nan gaba sai in k'ara maki, kinga ga gini an tak'alo min kin san zai ci kud'i."
Dai-dai lokacin Amina ta fito da kud'in a hannunta, ta mik'a ma Goggo Suwaiba. Amsa tayi tana mai hararar Amina.
"Amma ai naga gidan da za a gyara ba dani za a zauna a ciki ba."
Goggo tace.
"Gidan ma da tun kafin a gyara an fara mana gori. Kunga ku tashi mu tafi tunda wuri."
Mik'ewa tayi suma duk suka mik'e gaba d'aya.
Cikin damuwa ya dubeta tare da cewa.
"Haba Goggo ai abin bai kai haka ba, gida ni nasa kaina kuma za a gyara maku d'in. Kina cewa ku tashi ku tafi tun yanzu gashi idan za ayi gyaran gidan nan zaku dawo."
"To ai mun gama abinda zamu yi ba sai mu tafi ba."
"To shikenan bari mu rakaku waje."
Tafiya suka fara ta dubeshi tace.
"Au muzo gidan naka haka zaka barmu mu tafi bakomi a hannunmu?"
"Amina d'ibo min wasu kud'in."
Ya fad'a idonshi na kanta.
"Kamar nawa zan d'auko?"
"Duk yanda kika ga ya dace ki d'ibo kawai."
Da sauri ta shiga ciki ta bud'e drower d'in da kud'in ke ciki, d'aukowa kawai tayi ba tare data tsaya ko rafa nawa ta d'auko ba, ta fito dan ita kanta ta k'osa su tafi. Mik'a mashi kud'in tayi tana mai d'an russunawa.
"Au iye matarka ma fa naga alama ta fimu muhimmanci a wurinka."
Goggo ta fad'a tana mai ta'be baki.
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.