*K'UDIRINA*
®
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION©
EASHA MDDedicated to Maryamerh Abdulrahman (kwaiseh)
*25*
Wattpad@ayshatmadu
Dole ne na mik'a gajsuwata ga nagartatun cikin nagarta wanda yawansu ba zai dameni ba wurin ambatonsu espicially
*Maryamerh Abdul kwaiseh, sosai kika taka muhimmiyar rawa jinjinar ban girma, tare da Hauwa Jabo, Fiddausi Sodangi, Benazir, Ashnur kina raina kece sanadin shogowata nagarta tare da had'in kan M Jabo ina yinku, princess Amrah, Khadija candy, Safiyya galadanci, oum Samhat, lubabatu maitafsir, sady jegal, Jidda Aliyu, Bilkisu Bilyaminu, Asiya b Aliyu, meesherh lurv, mjay, Naseeba, Fiddausi SA, mrs omar, Rabi'atu sk msh, nooriya noor, beeboh Hafsat mai Sharif, seemby luff, Ayeesh A sadiq, Ayshat one, Hanifa usman, official- sahaf, Binta Bashir, futa lurv, deejah Abdul, stylish, munaiyshat, Hauwa H Nayaya, Maman jafar, queen mamue, feedo, BEBE'ARTH, Na'ila Aahmila. Allah ya bar k'auna tare da had'a kanmu ya had'a a gidan Aljanna. Sosai nake jinku a raina 'yanuwa rabin jiki, ina alfahari daku. Masu kamshin alkhairi.
Dubanshi take mai cike da takaici zuciyarta na k'una.
"Ban ta'ba ganin d'a mai irin halinka ba, a zauna aita fama da kai kan abu d'aya Salim. Ko Safeenat bana tunanin zata iya yin abinda kake yi. Ban ta'ba ganin d'a mai nuna rashin ci gaban mahaifinsa ba sai kai.
D'auraka ake akan hanya amma kak'i kabi. Mai kake so mu maka? A iya sanina Farida bata da makusan da za ace ba za a aureta ba. Ita ba muni ba.""Akwai makusa Mom! Akwai sosai. Farida idan har kin santa kin san bata da kamun kai, ina so na auri wadda zata ga girmana ta bama 'ya'yana tarbiya, uwa ita ke rayuwa da 'ya'ya a cikin gida. To bata natsu ba bare yaran da aka bar mata su natsu. Dan haka Mom ina so ki aje maganar auran Farida a gefe, ina mai neman afuwanku. Ba zan iya auranta ba shine kawai."
"Mom cikin mamaki take tafa hannayenta tare da cewa.
"Yau naga ikon Allah wurin Salim! Kana ganin yaron nan ko? Yau Salim daba mu muka haifeka ba zaka iya mana abinda yafi haka. Mu haifeka ka kasa bin umurninmu. Kana ko so ka gama da duniya lafiya?"
Cikin takaici Dad ya d'aura daga inda Mom ta sauke.
"Bari in fad'a maka..." Ya nunashi da yatsa.
"Baka isa ka sa company na yayi asara ba, dole ka auri wannan yarinyar Farida ko kana so ko baka so. Ko aya take ban damu ba, ci gabana nake so. Akan me? Baka isa ba wallahi Salim ina son kud'i fiye da yanda kake tunani, dan haka dole ne kabi umurnina."
Sai yanzu Salim ya d'ago da rinannun idanunshi, magana ya fara cikin raunanniyar murya.
Please Dad don't do this to me! Zan cutu rayuwata zata shiga garari. Ka san waye ni, ka san halina ka san ra'ayina. Kada son abin duniyarka yaja ka 'bata min komai."
Dad ne ya d'auki wayarshi dake aje kan kujera kusa dashi. Dealing number yayi, ba a jima ba can 'bangaran ya d'auka.
Gaisawa suka yi cikin girmama juna. Sannan Dad ya d'auko wata maganar kamar haka.
"Ina Farida tana gida ne? Salim ke son zuwa su d'an tattauna."
Can ya bashi amsa cikin sakin fuska.
"Eh tana gida. Mu fara shiri kenan muna da babban bak'o."
Dariya yayi irin tasu ta manya ya bashi amsa.
"Sosai kuwa. Ina dai mai k'ara baka hak'uri kan abinda ya faru tsakaninta da yayanta."
"Haba kada ka damu! Ai ya riga daya wuce."
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.