*K'UDIRINA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)
*61*
*Wattpad: Ayshatmadu*
Su Ayshat sun gama hutunsu sun fara shirin tafiya. Ranar da zasu tafi har airport suka rakasu, sai da suka yi kukan rabuwa dan ba k'aramin sabawa suka yi.
Kafin su wuce sai da Dad d'in Ayshat ya bata kud'i tare da ce mata.
"Islam idan har kina da bu'katar wani abu, kar kiji komai ki kira ki fad'a min domin yanzu na riga da na zame maki mahaifi."
"Insha Allah Daddy, Allah ya saukeku lafiya."
Gaba d'aya suka amsa da "Amin."
Haka suka rabu cikin kewar juna, suka dawo gida. Islam ji take ina ma basu tafi ba.
*** ***
Bayan wasu watanni. Islam taci gaba da hidimarta, yau ma kamar kullum tayi shirin tafiya school cikin wata had'ad'd'iyar jallabiyar da Ayshat ta bata, ta d'auki gyalen tayi rolling nashi.Fitowa tayi dan yin sallama ta tafi.
Had'ewa suka yi da Maryam k'awarta a bakin gate, tare suka jera har ciki suna tafe suna fira.
*** ***
Sun fito daga lectures shi ya bata damar fita dan ta samu abinda zata ci. Ji tayi ana ambatan sunanta, tsayawa cak tayi ba tare data waigo ba.K'arasowa wurinta yayi, kallo d'aya ta mashi taga yanda ya fita hayyacinshi, duk ya rame yayi wani iri kamar ba Abdallah d'an gayun nan da ta sani ba.
"Islam na kasa cireki a raina, na rasa yanda zanyi da rayuwata. Ina sonki da yawa ki taimaka min ki amince dani. Baki ce komai ba, kiyi magana."
K'ara tamke fuska tayi tare da juyar da kanta.
"Islam dama so yana zama k'iyayya ban sani ba?"
Cikin tsiwa tace.
"Yau gashi ka sani. Abdallah ina rok'onka da Allah da ka k'yaleni bana sonka, ai na zata ko dan abinda nama iyayenka zaka tsaneni a cikin a ranka."
Cikin marairecewa yace.
"Ni dai fatana ki yarda ki amince dani, duk wannan abin da kika yi ba shine damuwata ba, amincewarki nake nema."
"Aiko ya kamata ka damu da abinda nayi, ka ganni nan duk wanda ya ta'ba iyayena ban jin zan k'yaleshi. Dan haka na rok'eka daka k'yaleni."
Tana gama maganar ta juya ta fara tafiya. Ji tayi an fincikota an juyo da ita tare da fad'in.
"Dole ki aureni dan baki da miji sai ni..."
Kafin ya idasa maganar cikin 'bacin rai ta d'aukeshi da mari.
Dafe wurin yayi yana kallonta cikin ido.
"Abdallah ka rabu dani bana bu'katar ganinka a cikin rayuwata, ban jin zan ta'ba k'aunarka, idan kana tak'amar kayanka dake wurina, bani nace ka barsu ba dan haka kazo ka amshi kayanka. Kada ka k'ara biyoni wurin karatuna kaji na fad'a maka."
Wucewa tayi ba tare data k'ara bi ta kanshi ba.
Haka ta wuni ranta a 'bace har aka tashi, ba inda ta wuce sai gidansu Abdallah.
Tunda ta shiga gabanta ke fad'uwa da tsoro, haka ta rin'ka kutsawa tana jin kamar ta juya ta koma, amma haka tayi k'arfin halin k'arasawa ciki.
Zaune ta gansu a palour, samun wuri tayi ta zauna.
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.