*K'UDIRINA*®
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION©
EASHA MDDedicated to Maryamerh Abdulrahman (Kwaiseh)
21Tun daga ranar Islam ta dage har suka gama exams d'insu lafiya. Sai fatan samun sakamako mai kyau. Fatanta taga sun rabu da S Fulani lafiya.
*** ***
Yaya Muhammad yaje ya samu Baban Bashir da maganar auran da yake so yayi. Cikin jin dad'i yace."Kai amma naji dad'i sosai. Allah ya sanya alkhairi a cikin wannan aure naka. Yanzu zan samu Mallam Ali sai muje muji magana."
"To Baba na gode sosai."
"Kada ka damu Muhammad. Kaima tamkar d'ana kake, ka d'auka kai da Bashir duk d'aya kuke, duk wani abu daya shafeka kasa a ranka kana da uba mai tsaya maka, Insha Allahu zanga nayi bakin k'ok'arina akan lamuranka. Zan shige maka gaba akan auran."
Sosai Yaya Muhammad ya nuna jin dad'inshi da wannan magana da Baban Bashir yayi.
Yanda Baban Bashir ya fad'a ma Yaya Muhammad zai samu Mallam Ali suje nema mashi aure. Haka ko akayi sun shirya dan zuwa jin maganar. Da kanshi Baban Fatima yazo suka shiga ya kaisu d'akin saukar bak'i. Gaisawa suka yi cikin mutunta juna.
Mallam Abdullahi ne Baban Bashir ya fara magana cikin natsuwa.
"Dama munzo ne kan maganar d'iyarka Fatima da d'an wajanmu ke nemanta. Muna fatan ka san da maganar zuwanmu?"
Gyara zama yayi yana dubansu a tsanake.
"Eh na san da zuwanku. Sai dai kuma ina da labarin shi yaron da take so ana rad'e rad'in bashi da asali. Kuma kun san iyaye ba zasu so su d'auki 'ya'yansu su bama wanda basu san asalinshi ba. Dan naji ance daga shi sai k'anwarshi suke rayuwa a cikin gidansu."
Cikin rashin jin dad'in maganar da Baban Fatima yayi, Mallam Abdullahi yace.
"Haba Alhaji dan kaji labarinsu a haka, ba wai yana nufin basu da asali bane. Yanzu muna cikin zamani ne da son zuciya ya mana yawa. Amma Muhammad yana da asali wanda zaiyi alfahari dashi. Kowa ya san ba tsintattu bane su, suna da gatansu yanayin halin rayuwa ne da kuma Allah daya so ya jarabcesu a haka."
"Ina so ku fahimceni, su kad'ai fa suke rayuwarsu wanda ba wani da zai nuna mutum d'aya yace d'an'uwansu ne. Kun san da haka kuma."
Idanunshi ya tsaida a Kansu dan jin maganar da zasu yi.
"Alhaji naji maganarka Muhammad bashi da asali. Amma inaso ka dubi halinshi na gari da yake dashi, ai dama burin iyaye ako yaushe suga 'ya'yansu sun samu abokan zama na gari. Na tabbata inada yak'ini na kowace mace tana so ta samu Muhammadu a matsayin miji. Dan haka ina mai shawartarka daka barsu su auri junansu. Saboda rashin barin masoya su auri junansu shi ke k'ara kawo mana gur'bacewar tarbiyarsu, sai kaga sun aikata abinda aka guda. Amma idan aka barsu suka yi auran sai kaga an samu salama."
Ajiyar zuciya ya sauke.
"Shikenan zan duba inga yanda za ayi. Idan ba damuwa sai ku dawo nan da sati d'aya."
Mallam Abdullahi yace.
"Amma Alhaji daka duba mana anyi komai yau."
Sai yanzu Mallam Ali ya tanka gami da cewa.
"A'a Mallam Abdullahi muyi mashi uzurin, Allah ya kaimu nan da sati d'aya d'in."
Gaba d'ayansu suka had'a baki gami da cewa.
"Amin ya Rabbi."
Tafiya suka yi. Bayan sun isa gida. Mallam Abdullahi ya kira Muhammad domin ya fad'a masa yanda suka yi. Zuwa yayi da sauri dan yaji.
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.