*K'UDIRINA*®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Dedicated to Maryamerh Abdulrahman* (Kwaiseh)
*22*
"Haba Abba yaushe har za a biye mata a barta ta auri wannan yaron? Mai gareshi da zai rik'eta?"
Hafsat ce take magana cikin 'bacin rai.
"Wallahi sai yanzu na k'ara tabbatar da baki da hankali. Har yaushe zaki zauna da iliminki da hankalinki kamar wannan ya lalla'baki ki yarda da auranshi? Mai na sama yaci ballantana yaba ma na k'asa. Wai Abba kana fad'a kuwa akan wannan d'anyan aikin da take so tayi?"
Dariya yayi irin tasu ta manya kana yace.
"Haba Hafsat miye ban zauna na fad'a ma yarinyar nan game da wannan auran da take so tayi ba, amma tasa k'afa ta shure."
"To Fatima tunda haka kika ga ya dace da tsarin rayuwarki, zamu barki dashi, sai ya maki duk wani abu na jin dad'i ba tare da ko sisinmu ya shiga ba. Nan gaba kece zaki dawo abin tausayi a cikinmu."
Fatima dai zaune take duk maganar da suke bata tanka masu ba.
Umma ce ta k'araso wurin ranta a 'bace ta zauna tana mai cewa.
"Wai mai yasa kuke so kuga kun dagula mata lissafi? Insha Allahu ba zata zama abin tausayi ba.
Nifa bana ganin banbanci tsakanin talaka da mai kud'i, wannan yaron da kuke ta faman magana a kanshi ina da tabbaci da yak'ini zai rik'eta da kyau. Wai shin mai ake so a zamantakewar aure? Inace zaman lafiya da kula. To tabbas Fatima zata samu wannan abubuwan dan na tabbata Wanda kuke kira da talaka sai kunyi mamakin caring d'in da zata samu a wurinshi wanda Ku da kuke gidan masu kud'in baku samu ba. Har yaushe kuka samu kulawarsu wanda kullum suna can suna tunanin kud'in da zasu samu ba taku suke ba."
"A'a Umma. Aiko muna samun kulawar da kowace mace take samu a gidan mijinta."
"Uhm Hafsat kenan! Gaba d'aya kallonku nake."
Abba ne ya dubi Umma cikin takaici tare da cewa.
"Wai ke Haulatu yaushe zaki fahimci yanda duniya take ciki ne? Kinbi ki karanta ma yarinya karatun da ba zai amfaneta ba."
"To akan mai zaku tasa yarinya kuyi ta dagula mata lissafi."
"To ai magana ta wuce, mun barta da wanda take so, muna nan muna jiran zuwansu.
Abokan Abba ne suka iso Dan tarbar bak'in da zasu zo neman auran Fatima. Zaman jiransu suka tsaya.
Cikin hukuncin Allah sai gasu sun iso. Gaisawa suka yi cikin mutunta juna.
Mallam Abdullahi ne yayi magana.
"To gamu min iso yau d'in domin nema ma d'anmu aure."
Abba ne yayi magana.
"To Allah yasa kunzo da sadakin auran dan mu d'aura a yanzu."
"Yaushe har yaron ya shirya da za a d'aura aure yanzu. Ai aure yana son shiri. Kuma yaron nan ba k'arfi gareshi ba."
"Eh sanin da nayi baida shi shiyasa na nema mashi sauk'i, tunda ita taji ta gani take sonshi a haka, na san zata iya zama dashi ko ba lefe."
Cikin nuna jin dad'in maganar da yayi, Mallam Abdullahi yace.
"Haba Alh ai duk wannan bai taso ba. Harkar arzik'i ya kawomu bana tsiya ba."
Mallam Ali ne ya dubi abokan Alh Sharif.
"Yakamata kusa baki a wannan lamuran, ku rok'a mana akfarmar yasa mana rana."
Sai yanzu wani daga cikinsu yayi magana.
"Alhaji Saharif ina naima masu alfarma da asa masu rana koda na wata d'aya ne."
"To shikenan nasa maku wata d'aya."
Cikin nuna jin dad'i mallam Abdulla yace.
"Masha Allah! Mun gode sosai Allah yasa muna da rabon gani. Ga kud'in gaisuwa nan naira dubu ashirin, zamu kawo sadaki nan da sati d'aya da kayan sa rana." Ya mik'a mashi.
Amsa yayi cikin yamutsa fuska sai kace wanda yaga kashi.
Abinda zasu d'anci aka kawo masu. Basu wani ci sosai ba suka yi shirin tafiya.
A hanyarsu ta komawa gida ne Mallam Ali ya dubi Mallam Abdullahi ya fara magana.
"Wai baka lura da wannan bawan Allan bane? Kamar fa baya son bamu auran nan."
"Na lura dashi. So yayi ai a hau sama, wannan da kake ganinshi ya d'aura buri ne akan 'ya'yanshi, bai san bai isa ya hana hukuncin Allah ba."
"Sosai kuwa." Cewar Mallam Abdullahi.
Da haka har suka isa gida suna tattauna maganar.
Mallam Abdullahi ya kira Yaya Muhammad. Ba jimawa sai gasu sun iso shi da Bashir.
Duban Yaya Muhammad yayi a tsanake.
"Alhamdulillah! Min dai je an tsaida magana. Sun sa ranar biki wata d'aya."
"Wata d'aya? Ai yayi kad'an, yaushe na shirya?"
"Kada ka zamu Allah zai rufa asiri, shi ai so yayi ma a d'aura auran yau. Shine muka rok'i alfarma ya bar mana wata d'aya."
"To Allah ya kaimu. Bari mu samu a sai kayan sa ranar, sai in tambayeta kud'in sadakin mu gani."
"To ba damuwa. Allah ya rufa asiri."
Suka had'a baki da fad'in "Amin."
Tashi suka yi suka tafi suna mai tattauna yanda zasu yi.
Ya koma gida. Samun wuri yayi ya zauna cikin zumud'i ya dubi Islam tare da cewa.
"Ansa rana yau."
Cikin nuna jin dad'i da dariya a fuskarta tace.
"Kai Amma naji dad'i sosai! Na kusa samun uwa a gidan nan, dan Aunty Fatima tamkar uwa take a wurina."
Binta yayi da kallo yana dariya, dan ganin yanda Islam ke dariya.
"Amma fa wai wata d'aya suka sa."
"Wata d'aya kuma? Yaushe har ka shirya? Aure fa akwai kashe kud'i, basu san baka dashi bane?"
"Kede Allah ya shige mana gaba kawai. Yanzu so nake in siyo kayan sa ranar da za a kai masu."
"To Allah ya nuna mana, ya baku zaman lafiya."
"Amin ya Rabbi 'yar k'anwata."
*** ***
Tsaye take jikin mirrow d'in data maids hankalinta a kanshi tana ta d'aura d'ankwali. Lace ne tasa mai kyau da tsada pink mai ratsin blue da yaji stones. Duban kanta tayi ta saki murmushi wanda ya k'ara fiddo mata da kyawunta. Juyi tayi da jikinta wanda ta k'ara saki murmushi. Gyale ta d'auko blue ta yafashi akan kafad'arta, inda ta d'auki takalmi mai tsini kalar gyalen tasa, tare da jakarta wanda ake kira da side bag ta rataya. Key d'in motarta ta d'auka dake aje kan gado. Taku ta fara cikin natsuwa wanda in banda takun k'arar takalminta baka jin k'arar komai.D'akin Ammi d'inta ta shiga. Rungumota tayi ta bayanta tana mai fad'in.
"Ammina ni kad'ai."
Juyo da ita tayi da murmushi d'auke a fuskarta.
"Kai sweetheart! Wannan irin kwalliya haka sai ina? Kamar wadda zata wurin biki?"
Juya idanunta tayi tare da cewa.
"Wurin Yaya Salim zani na ganshi."
Dubanta tayi duba mai cike da k'aunar d'iyar tata da kulawa tace.
"To kina da tabbacin yana gidan ne idan kinje.""Eh to bana tunanin zai je wani wuri, amma bari nayi sauri naje kada ma ya fita."
Tafiya ta fara tana mai d'aga ma Ammi hannu. Itama d'aga mata hannun tayi d'auke da murmushi a fuskarta.
Fita tayi ta shiga motarta. Kunne kai tayi bakin gate wanda yaba mai gadi damar bud'e mata ta fice. Tafiya take cikin kwanciyar hankali, sai murmushi take, ga sautin wak'a na tashi a cikin motar a hankali.
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.