K'UDIRINA page 28

129 9 0
                                    

*K'UDIRINA*

        ®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

        ©
*EASHA MD*

*Dedicated to Maryamerh Abdulrahman* (Kwaiseh)

         *28*

  *Wattpad@ayshatmadu*

"To Islam ayita hak'uri, dan yanzu sai kin kai zuciyarki nesa akan auran da yayi, ki girmamata tamkar yanda zaki girmama yayanki, itama yayarki ce tunda tana auran yayanki. Duk abinda ta saki ki rink'a yi mata cikin jin dad'i. Ko ta saki ko bata saki ba ki zama mai taimaka akan ayyukan gida kada ki gaji kinji ko Islam?"

"Eh Umma naji, Insha Allahu zan zamo mai kiyayewa."

"Yauwa Islam! Allah yayi maki albarka."

Yaya Muhammad ne ya shigo ya samu wuri ya zauna tare da cewa.

"Umma kuna nan kenan?"

"Eh Muhammad.." Ta bashi amsa tare da d'aura wata maganar.

"To Muhammad sai kayi hak'uri, zaman aure daban yake, sai ka kai zuciyarka nesa kayi hak'uri da nauyin da Allah ya d'aura maka. Yanzu dole wasu abubuwan sun k'ara hawa kanka, ka samu kaga duka cikinsu ka farantama kowa, saboda kishin kayi ma d'aya baka ma d'aya ba, ko kafi damuwa da d'aya a cikinsu. Na san zaka ce mai zaija masu kishi a tsakaninsu alhalin ba kishiyoyi ba, ka auna kaga cikin 'ya'yanka idan ka nuna kafi son d'aya a ciki, to sai an nuna jin zafi. Dan haka ka kula tsakanin k'anwarka da matarka, Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya tare da albarka a cikin auranku."

Amsawa suka yi da "Amin."

"To ni zan wuce sai nazo ganinku."

Ta mik'e tana mai k'ara gyara mayafinta.

"To Umma mun gode sosai, Allah ya bar zumunci."

Har waje suka rakata, sannan suka dawo ciki, kayan data d'auka zata tafi dashi gidansu Zarah, shi ta d'auka kawai suka rufe gidan dan tafiya kafin taga yanayin zamansu sannan su idasa kwashe kayansu, dan shima bai kwashi kayan sawanshi ba, sai sababbin daya d'inka.

Tafiya suka yi tare da abokanshi guda uku, mota d'aya suka shiga. Lokacin da suka isa da Jakarta a hannu, ba kowa a d'akin. Duban Islam yayi yana mai cewa.

"D'an lek'a d'akin nan ki kirata."

D'akin dake k'asan ta shiga ta ganta zaune daga ita sai yayarta Habiba da ita d'aya ta rage bata tafi ba.

Duban Islam tayi data shigo, tana tambayar zuciyarta ita kuma wannan mai tazo yi?

Gaidasu tayi. Fatima ta amsa cikin sakin fuska tare da cewa.

"Islam ya gajiyar biki?"

Da murmushi d'auke a fuskarta tace.

"Aunty Fatima ke za a tambaya gajiyar biki."

"To kinde yo packing d'in kayanki ko?"

Karaf Habiba tace.

"Wane irin packing d'in kaya kuma? Ai ta bari ku gama cin amarcinku ko?"

Ta k'arasa maganar tana duban Islam duba na tsana, dan ji take daga ita har Yayan nata duk ta tsanesu.

Cikin yanayi na rashin jin dad'in abinda 'yaruwarta tayi tace.

"Haba Aunty Habiba! Dan me zaki fad'a mata wannan maganar? Idan bata zo nan ta kwana ba ina zata ta kwana?"

"Wannan ku ta shafa. Ni kinga tafiyata."
Ta suri gyalenta da key d'in motarta ta fice ko kallon su Yaya Muhammad dake zaune ba tayi ba.

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now