K'UDIRINA page 30

122 13 0
                                    

K'UDIRINA

        ®
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

        ©
EASHA MD

Dedicated to Maryamerh Abdulrahman (Kwaiseh)

                   30

    Haj Nafisa har yanzu kina raina ba zan manta dake ba, tabbas kin nuna min k'auna, shiyasa naga dacewar sadauk'ar maki da wannan shafin. Allah ya bar zumunci.

"Har kin dawo?"

"Eh Hajia na dawo."

Cikin kulawa da damuwa da yanayin da Hajia taga Islam ta tambayeta.

"Islam mai ke damunki naga kamar kinyi kuka?"

"La Hajia! Kuka kuma? A'a banyi kuka ba."

Islam tayi maganar tana mai k'ak'alo murmushi a bakinta.

"Ki fad'a min idan har wani abu yana damunki, kada ki 'boye min komai."

"Hajia ba abinda ke damuna kawai kaina ne ya d'an min ciwo shiya sani kuka."

Subhanallahi! Kinsha magani kuwa?"

Ta fad'a cikin damuwa.

"Eh Hajia na sha."

"Sannu kinji, Allah ya baki lafiya."

Wayar Hajia dake aje kan kujera ne ya fara k'ara.

"Yi Sauri ki mik'o min wayata kada ta tsinke."

Cewar Hajia tana mai mik'a mata hannu tun kafin ta d'auko.

Da sauri Islam ta d'auko ta mik'a mata, d'auka tayi had'i da sallama. Gaisawa suka yi, sannan ta d'aura da cewa.

"Babana wai yaushe zaka zo ne? Daga k'arshan wata gashi har wannan da muka shiga ya kusa k'arewa."

Cikin kulawa da girmamawa ya furta.

"Hajia kiyi hak'uri! Ni kaina ba haka naso ba, ayyuka suka sha min kai, amma Insha Allahu muna nan zuwa gaba daya muyi hutu a nan."

"To Allah ya tabbatar ya nuna mana ranar. Ina nan ina jira, ga Islam nan bari in bata ku gaisa."

Ba tare data jira jin abinda zaice ba ta mik'a ma Islam. Amsa tayi tare da yin sallama. Amsawa yayi cikin sakin fuska, ta gaidashi.

"Islam ya karatu? Ana maida hankali ko?"

"Lafiya lau."

"To Allah ya taimaka. Kina level nawa ne?"

Amsa ta bashi cewar.

"Ban dad'e da farawa ba ai, level 1 nake, sai dai mun kusa fara exams na second semester."

"Good! Allah ya taimaka Islam."

"Amin na gode.!"

Ta furta tana mai jin dad'in addu'arshi. Mik'a ma Hajia wayar tayi.

Sallama suka yi ta aje wayan, daga yanayin farin cikin da  Hajia ta nuna k'arara a fuskarta ya tabbatar ma da Islam Hajia ba k'aramin son d'anta take yi ba.

"Hajia ina lura dake duk sanda Babanki ya kira kina shiga farin ciki."

"Islam ba dole na shiga farin ciki ba, shi kad'ai gareni shi ya zame min komai, shi ya d'auke min komai na rayuwa, baya bari nayi kukan rashin komai."

Cikin tausaya ma Hajia tace.

"Ai haka akeso d'a na gari ya kasance, amfanin haihuwar kenan. Yanzu ba gashi shi kad'ai gareki ba, amma ya d'auke maki komai, d'aya tamkar da dubu."

"Sosai kuwa Islam."

"Allah dai ya k'ara bud'a mashi."

Cewar Islam.

"Amin."

Har k'arfe goma na dare tana wurin Hajia, sai da taci tuwo sannan tayi shirin komawa d'aki, sallama tayi ma Hajia ta tafi. Tana shiga parlour taddasu tayi zaune suna kallo ba tare data kallesu ba tayi d'akinta. Kallo suka bita dashi, Yaya Muhammad yana mamakin yanayin da Islam ta canza a lokaci guda.

Tana shiga ciki,kayan jikinta ta cire, kana ta d'auki na barci tasa ta kashe fitilan d'akin tare da hayewa kan gado, sai a lokacin ta tuna da wayarta dake kan gadon da tun dawowarta ta sakeshi a wurin.

D'auka tayi dan dubawa, 15 missed calls ta gani tare da text, dubawa tayi taga wanda ya kirata, Abdallah ne ya kirata har sau goma, sai kuma Yaya Muhammad har sau biyar.

Waro idanunta tayi tare da furta.

"Na shiga uku! Wannan kira haka?"

Duba text d'in tayi wanda yake d'auke da.

*Ina kika shiga haka?*

Sai d'ayan da yake tambayarta.

*Allah yasa lafiya?*

Kiranshi tayi wanda bugu d'aya ya d'auka tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, wanda ta jishi cikin wayar, tare da tambayarta.

"Ina kika shiga haka tun d'azun nake nemanki?"

"Kayi hak'uri! Na bar wayar a d'aki ina wurin Hajia."

"Haba gaba d'aya duk kin tada min da hankali! Ya kamata ki rink'a tafiya da wayanki."

"Insha Allahu zan rink'a tafiya dashi, yau ma mantawa nayi."

"Sai yanzu hankalina ya kwanta. Ina fa so inzo jibi. Dan ma ina tunanin gobe ba zan shigo gari  da wuri ba." idan na dawo da wuri kuma zanzo."

"To Allah ya kaimu ya dawo min da kai lafiya."

"Amin my wife."

Dariya tayi, sun dad'e suna fira sannan suka yi sallama. Addu'ar kwanciya tayi ta shafa duka jikinta tare da kwantawa.

*** ***
Washegari tunda asuba bayan ta gama laziminta, wanka tayi da sauri ta gama shirinta, d'aukar komai nata tayi ta wuce sashin Hajia. Ganinta da sassafe yasa Hajia ta bita da kallo tare da cewa.

"Islam ya na ganki da wuri haka? Duka fa yanzu k'arfe shida."

Ta fad'a idonta na kan agogo.

Dariya Islam tayi tare da duk'awa kusa da ita tana mai furta.

"Yanzu dai ina kwana?"

"Lafiya lau. Wai mai zaki yi da wuri haka kika shirya?"

"Hajia bafa wani abu bane, inaso ne kawai in tafi yau da wuri akwai abinda nake son inyi."

"Amma dai baki karya ba?"

"Eh." Ta fad'a mata a tak'aice.

"Yanzu dai ki hanzarta ki had'a abinda zaki ci. Dan ba zaki fita baki karya ba, ki duba ko k'wai ne ki soya ki had'a da tea."

Yanda Hajia ta fad'a, haka Islam tayi, kitchen ta fad'a ta had'a komai da sauri. Zama tayi ta karya, kana ta suri jakarta tare da kallon Hajia tana mai cewa.

"Hajia na gama, bari na tafi na gode sosai, sai na dawo."

Ficewa d'akin tayi tare da gidan da sauri, dan kada ta had'u da Yaya Muhammad. Dan har yanzu fushin da take da Fatima ya shafi yayanta.

*** ***
Kwance yake wanda gaba d'aya k'arar wayarshi ya addabeshi, silent ya maidashi, duk da haka gani yake hasken wayar ta addabeshi, hannu yasa ya kashe yana mai takaicin kiran da aka dameshi dashi.

Toilet ya fad'a yayi wanka, wanda yanda ake yanayi na zafi, duk da sanyin A/C dake tashi a d'akin bai hanashi sa 'yar riga mara hannu tare da wando three quarter. D'an jingina yayi da pillow dake gadon, yasa farin glass d'inshi wanda zai tabbatar maka da medical ne, tare da kunna laptop d'inshi yaci gaba da aikinshi da yake yi a ciki.

An d'auki mintuna yana nan a haka, k'arar bud'e k'ofa yaji wanda ya bashi damar d'agowa dan ganin mai shigowa. Farida ya gani ta shigo wanda kallo d'aya ya mata ya tabbatar da ranta a 'bace yake, wanda yanayinta zai k'ara tabbatar da kuka tayi.

Maida kanshi yayi yaci gaba da latsa Laptop d'inshi ba tare daya tanka mata ba.

K'arasowa wurinshi tayi.

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now