K'UDIRINA
®
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION©
EASHA MDDedicated to Maryamerh Abdulrahman (Kwaiseh)
29
Wattpad@ayshatmadu
Wannan shafin naki ne ke kad'ai kiyi yadda kike so dashi Bilkisu Bilyaminu na gode sosai duk da wuni naso
"Wai ke wace irin macece ke? Kada ki manta a wurin aiki fa nake, mutuncin mace azo gida a sameta. Wannan wace irin rayuwa ce?"
Magana ta fara da raunanniyar murya.
"Salim ka taimaka min ka soni ka aureni, ba zan iya rayuwa ba tare da kai ba. Anya Salim ka san yanda d'acin rashin masoyi yake? Ka san soyayya kuwa?.."
Had'a hannayenshi yayi wuri guda ya k'ura mata ido yana kallonta sai kace mai karantar wani abu a kanta.
Ci gaba tayi da magana had'i da duk'awa k'asa gwiwoyin k'afarta a k'asa wanda har hawaye ya jik'a mata fuska.
"Salim ka taimaka min, kome kake so zan maka, abinda baka so zan kiyaye, idan har kak'i amincewa dani, tabbas zan iya rasa rayuwata."
"Farida!.." Ya ambata cikin runtse idonshi yana mai mutstsika idon nashi da hannu. K'ara ambaton sunanta yayi.
"Farida! Ki tashi ki tafi, inaso kiyi hak'uri dani, kisa a ranki iyayanmu basu yi tunanin had'amu ba. Bana so kiyi kuka dani kiyi hak'uri ina da wadda nake so. Dan haka ki cireni a ranki."
Zumbur ta mik'e daga duk'en da take, binshi tayi da kallo mai cike da mamaki, ga idonta daya kad'a daga fari ya juye kalar ja ta furta.
"Salim..!" Tana mai nuna shi da yatsa.
"Kana da wadda kake so fa mace? Haba Salim kada kamin haka. Duk duniya namiji d'aya nake so, kuma shi kad'ai zan ci gaba da so. Dan haka ina mai umurtarka daka cire son wadda kake ikirarin kana so..."
Maganar take sai kace wadda ta kamu da cutar hauka.
"Salim ka cireta a ranka, dole ka aureni, nabi da kai a hankali ya kakeso nayi?"
Fashewa tayi da kuka mai tsuma zuciya.
Runtse idonshi yayi. "Na tsani kuka, ki tashi ki fita."
Cikin kuka tayi magana.
"Wallahi ba inda zanje har sai ka furta kana sona."
"Oh! Wai ke wace iri ce haka? Ana so dole ne? Haba kin fara kaini mak'ura fa."
Samun wuri tayi ta zauna tana mai ci gaba da kukanta.
Ganin kukanta ya takura mashi dole tasa ya dubeta ya fara magana cikin natsuwa yanda zata fahimceshi.
"Kin gane Farida! Ba wai bana sonki bane, kinga akwai wadda nake so, so tunda kin matsa yanzu ki tashi kije gida anjima ina nan zuwa sai mu tattauna, kinga a gida yafi mutunci da tsari. Inma gobe kike son a d'aura auran ba damuwa sai ayi auran ko?"
Murmushi ne ya su'buce mata a fuskar dake jik'e da hawaye, kana tace.
"Salim da gaske kake min wannan maganar? Ko mafarki nake?"
D'aga mata kai yayi tare da lumshe idanunshi wanda shima d'auke yake da murmushi a fuskarahi.
"To shikenan bari na tashi naje, ina fa jiranka ka tabbatar da kazo fa."
"Kada ki damu zanzo."
Tashi tayi dan tafiya, kusa dashi tazo ta rankwafa dai-dai kumatunshi ta sakar mashi kiss, wanda nan take ranshi ya 'baci, dan banyi tunanin haka daga gareta ba. Amma tuna yana son ya rabu da ita lafiya yasa ya dai-daita fuskarshi.
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.