K'UDIRINA page 56

81 11 1
                                    

*K'UDIRINA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)

      *56*

*Wattpad: Ayshatmadu*

Fita tayi ta samu Yaya Muhammad zaune ya rafka tagumi, yana ganinta da sauri ya sauke hannunshi yana mai dubanta.

Samun wuri tayi ta zauna, cikin sanyin murya tace.

"Yaya Abdallah ne ya kirani wai ga iyayenshi nan sun kusa k'arasowa."

Tana idasa maganar ta du'kar da kanta k'asa. Kallonta yaci gaba da yi kana ya nisa yace.

"Allah ya kawosu lafiya."

Mi'kewa tayi ba tare da tace komai ba ta koma d'aki. Fad'awa kan gado tayi tana mai sauke ajiyar zuciya. Ayshat ce ta dubeta tare da cewa.

"Islam mai ya faru kuma?"

D'an dubanta tayi kad'an tare da cewa.

"Mai kika gani?"

D'an ta'be baki tayi kad'an tace.

"Naga ba haka kika fita ba, ko auran ne ya fara girgizaki?"

D'an murmushi tayi kana tace.

"Kede kika sani."

Firansu suka ci gaba da yi.

*** ***
Isowarsu keda wuya daddy'n Ayshat ya fita ya shigo dasu cikin sitting room d'in Hajiya duk suka zauna aka gaisa.

Yaya Muhammad ne ya shigo d'akin wanda tun kafin ya shigo gabanshi keta fad'uwa.

Tsaye yayi yana kallonsu ba tare daya furta komai ba, "mutanan da ba zan ta'ba mantawa dasu ba a rayuwata, mutanan da suka tarwatsa duk wata farin ciki nawa, mutanan da duk duniya na tsani na sasu a idanuna. Na tsaneku na tsaneku ba zan ta'ba k'aunarku ba."

Duk wannnan maganar a zuciyarshi yake.

Ji yake kamar ya shakesu yaga suma basa numfashi kamar yanda suka raba mahaifinsu da numfashi ya bar doron duniya.

Lokaci k'ank'ani gaba d'aya idanunshi sun kad'a sunyi jajir kamar garwashi. Sai fidda numfashi yake da sauri da sauri.

Ji yayi an ruk'o hannunshi, da sauri ya dawo hayyacinshi, yana duban wanda ke ri'ke dashi.

Daddy'n Ayshat ne ri'ke da hannunshi yace.

"Muhammad mai ya faru da kai haka lokaci k'ank'ani ka fita hayyacinka?"

Girgiza kai yayi tare da cewa.

"Bakomai kawai dai hakanan."

Jawo hannunshi yayi ya zaunar dashi yace.

"Kana tunanin rabuwa da Islam ko? Aure ba yana nufin kun rabu bane kuna tare."

K'ok'arin saisaita kanshi yayi tare da gaida wad'anda ya tsana fiye da mutuwarshi.

Amsawa suka yi kana suka fara maganar abinda ya kawosu.

Baba Salisu ne yayi magana cikin nuna isa da tak'ama shi ga mai kud'i.

"D'anmu yaga 'yarku yana so shine muka zo nema mashi auranta."

Daddy'n Ayshat ya gyara zama tare da cewa.

"An baku kuma kamar yanda kuka sani dama ba dogon lokaci za a d'auka ba, sati biyu ne."

"Ba damuwa in dai kun shirya muma a shirye muke, fatanmu Allah ya basu zaman lafiya."

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now