*K'UDIRINA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)
*53*
*Wattpad: Ayshatmadu*
Mi'kewa tayi ta fara shiryawa, ko powder bata shafa ba ta zura hijabi ta fito.
Samunshi tayi zaune kan kujera yana shan tea. Du'kawa tayi 'kasa had'i da ce mashi.
"Yaya na shirya zan tafi."
Hannu yasa a aljihu ya ciro kud'i ya mi'ka mata tare da cewa.
"Gashi ki tabbatar da kin samu abinda zaki ci kada ki zauna da yawa."
Hannu tasa ta amsa tare da mi'kewa cikin hawaye tace.
"To Yaya."
Har ta fara tafiya ya kira sunanta a hankali, tsayawa tayi ba tare data waigo ba, 'ko'karin goge hawayen daya zubo mata take yi.
"Islam ba kiranki nake ba kika tsaya."
Ya fad'a yana mai binta da kallo.
Dawowa tayi ta du'ka kanta na 'kasa. Tambayarta yayi.
"Islam meke damunki haka? Ki fad'a min baki da wanda kike dashi da zaki fad'a mashi damuwarki."
Shiru tayi ba tare da ta iya furta wata kalma daga bakinta ba. "Taya zan iya fad'a mashi damuwata wadda bana tunanin zai yarda da ita? Taya zan iya fad'a mashi Abdallah na za'ba a matsayin mijin da zan aura?"
Maganarshi ta tsinkaya cikin kunnanta, yana cewa.
"Islam tambayarki nake kin kasa bani amsa kin tasani sai shashshe'kar kuka kike min"
Da sauri ta d'ago ta kalleshi ta maida kanta 'kasa yayin da take jin saukar hawayen da har yanzu ya'ki tsayawa a jikinta.
'Kura mata ido yayi yana kallonta yana ayyanawa a ranshi Allah yasa damuwar nan data shiga kada ya kasance a kan Abdallah ne.
D'an gyaran murya yayi had'i da cewa.
"Islma fad'a min duk abinda ke ranki ni kuma na maki al'kawarin zan maki ko menene shi, zan tsaya maki koda kuwa ni zan rasa farin cikina inde har ke zai saki farin ciki."
Ya idasa maganar yana had'iye miyau mai d'aci.
Yawo ta fara yi da maganar a bakinta ta rasa ta yanda za tayi ta fad'a mashi. Zuciyarta ce ta fara ayyana mata da cewar. Islam yanzu kike da damar fad'a mashi kada ki bari damarki ta kufce maki. D'ago da kanta tayi ta kalleshi ta fara magana tana mai murza 'yan yatsunta.
"Yaya dama a kan Abdallah ne bana so ka rabani dashi duk da na gane ko shi waye zanso ka barni naci gaba da soyayya dashi. Yaya tabbas zanyi shari'a da iyayenshi tarayyata dashi ba zata hanani gurfanar da iyayenshi a gaban kotu ba."
Kallonta yake kallo mai cike da nuna bata da hankali bata san inda ke mata ciwo ba. D'an du'ko da kanshi yayi kusa da ita yace.
"Islam baki da hankali ne? Wanda suka yi sanadin rasa iyayanmu shine kike tunanin tarayya da shi? Kin san waye kuwa? Shine wanda iyayenshi suka kashe mana mahaifi da hannunsu. Sune suka rushe duk wani farin cikinmu, sune wad'anda suka ja dai-dai da dangin mahaifiyarmu na tsanesu saboda suma sun watsar da ita a lokacin da take naiman taimako..."
Numfasawa yayi ranshi yana 'kuna yaci gaba da magana.
"Islam ba zan ta'ba bari ki auri Abdallah ba dan farin cikinki ya fiye min komai, ba zan yarda ki shiga cikin 'kunci ba."
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.