K'UDIRINA page 23

111 10 0
                                    

*K'UDIRINA*

         ®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

          ©
*EASHA MD*

*Dedicated to Maryamerh Abdulrahman* (Kwaiseh)

                *23*

"Fatima kin san komai a kaina, kin san bani dashi. Zanyi iya k'ok'arina, kiyi hak'uri da abinda zaki samu. Wata rana sai kiga kamar ba ayi ba."

Daga can 'bangaren da take rik'e da wayar tana sauraranshi tace.

"Kada ka damu, kai nake so ba wani abu ba. Ka kawo duk abinda ya sauwak'a, sai dai sadakin ko dubu arba'in d'in ne ka samu ya kai."

Cikin jin dad'i, da k'ara jin k'aunarta na shiganshi, sosai yake jinta a ranshi, yace.

"Amma naji dad'in maganarki amaryata, Allah ya bani ikon kula dake."

Dariya ta mashi ba tare da tace komai ba. Sallama suka yi ya aje wayar yana mai duban Islam dake zaune tana Jin wayar da suke.

"Kinji yanda muka yi da ita ko? Yanzu kinga zanyi amfani da kud'in da nake tarawa. Sai Wanda nake aje maki saboda registration d'inki, tunda ba a tashi yi ba."

"Eh hakan yayi, duk sai ka had'a muga yanda kud'in zai kama."

"Yanzu de dole in samu wani gidan, kinga yanda tsarin gidan nan yake gaba d'aya d'akuna biyu ne duk daban daban, dole yanzu in samu mai palour da koda d'aki biyu ne saboda ke."

"Hakane. Dan idan ma kace a gidan nan zata zauna bana tunanin iyayenta zasu yarda, tunda suna ganin inda sauran ke aure."

Cikin damuwa ya furta.

"Gaba d'aya Islam na rasa ta yanda zan 'bullo ma wannan hidimar, na hanga naga ba k'aramin hidima zanyi ba. Gashi inata juya wanda nake ajewa ina tunanin nawa za a samu."

Dubanshi tayi cikin tausayi da kulawa ta furta.

"Yaya kada kasa ma kanka damuwa, komai zai tafi yanda ake so da yardar Allah."

"To Allah yasa haka. Bari in d'auko asusun da nake tara kud'in."

Mik'ewa yayi ya d'auko suka fasa. Ya had'a kud'in gaba d'aya harda wanda yake tara na makarantar Islam. K'irgawa ya fara yi. Kud'in ya kama gaba d'aya dubu d'ari biyu da hamsin. Sosai suka nuna farin cikinsu.

"Kai Islam kinga ikon Allah! Ban ta'ba tunanin kud'in zai kai haka ba. Tunda jefawa kawai nake duk yanda ta kama."

Farin ciki d'auke a fuskarta tace.

"Ai sai mu gode ma Allah. Kuma ai kafa yi shekaru kana asusun nan."

"Shiyasa naki aje kud'in a banki in ba haka ba sai na kashesu."

"Yaya ba shiyasa asusun keda amfani ba, gashi munga amfaninshi."

"Sosai kuwa. Kinga yanzu ki tashi ki shirya muje kasuwa mu had'a lefe. Ina tunanin wannan kud'in zai ishemu mu had'a a talauce."

"Bari in tashi, koma bai isa ba, kafin bikin idan aka samu kud'in sai a idasa."

Mik'ewa tayi da yake a shirye take. Hijab kawai ta zira a kanta ta fito. Tafiya sukayi. Suna isa akwati suka fara siya d'an madaidaita. Sannnan suka siya kaya da bai wuce kala ishirin da biyar ba. A haka dai suka had'a lefe 'yan abubuwa kad'an ya rage da zasu idasa. Dawowa gida suka yi cikin farin ciki.

Islam sarkin azar'ba'bi bud'e akwatinan tayi ta fara shirya kaya a cikinsu, fuskarta d'auke da fara'a.

Kallonta yake cikin kulawa shima da murmushi d'auke a fuskarshi.

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now