*K'UDIRINA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)
*60*
*Wattpad: Ayshatmadu*
Duk girgizanshi da yake amma ko alamar motsi baya yi. Da sauri ya fita waje dan kiran mahaifinshi. Gidan suka shigo da sauri yayin da 'yan ganin son k'wak'waf suka mara masu baya dan shigowa.
Baba Nasiru dake ta faman sa'ba malunmalun ne ya samo ruwa da sauri ya watsa mashi.
Dogon ajiyar zuciya ya sauke yana bin kowa dake wurin da ido.
"Dan Allah ku fad'a min mafarki nake ba da gaske bane, ba zan iya rayuwa babu Islam ba. Abba ka duba min."
Fashewa yayi da kuka, gaba d'aya lokaci guda ya fita hayyacinshi.
Daddy dake tsaye cikin 'bacin rai yace.
"Abdallah ya zama dole ka cire wannan yarinyar mara tarbiya a cikin zuciyarka. Duk da wulak'antamu da tayi ka kasa cireta a ranka? To bari kaji na rabaka da ita ba kai ba ita, mai zaka yi da talaka irinta ga 'ya'yan manyan mutane da suke binka zaka nace ma wadda bata gaji arzik'i ba."
Islam ce ta dubashi cikin tsiwa da nuna tsantsar k'iyayya da bayyana k'arara a fuskarta tace.
"Har kun kai matsayin da zaku iya ma wasu gorin arzik'i? Zanso ku tuna matsayin da kuke a da kafin ku kai haka, da can ku masu arzik'in ne ko daga baya kuka yi? Idan kuma da arzik'i aka haifeku ina so in sani ku fad'a."
Daddy'n Ayshat ne ya rik'ota ya shiga cikin gida da ita har d'akin Hajiya ya zaunar da ita. Samun wuri yayi shima ya zauna yayin da Hajiya itama ta shigo d'akin tana mamakin wannan al'amarin.
Daddy'n Ayshat ne ya dubeta yace.
"Dama Islam haka kike baki da kunya? So kike a tafi dake duniya? Kina tunanin duk wanda yaji labarin abinda kika yi zaiyi sha'awar auranki? Mai ya maki da baki tashi yanke hukunci ba sai a bayyanar jama'a ki lalata auranki?"
Kuka Islam ta fara. Hajiya ta dubeta tace.
"Haba Islam ai iyayenki ne da zaki zauna kina masu rashin kunya irin haka ba tare daya kinji komi a ranki ba. Miye dalilin hakan?"
Cikin kuka tace.
"Hajiya wad'annan azzaluman ba zasu ta'ba zama iyayena ba, na tsanesu bana k'aunarsu. Tabbas koda na nace ina son auran Abdallah har a cikin zuciyata ba da gaske nake ba, irin wannan ranar nake jira da nima zan fara d'aukar fansar abinda suka mana."
"To amma meyasa tun kafin ranar baki fasa auran ba sai a yau?"
" Tun daga ranar da na gane Abdallah ba k'aramin k'aunata yake ba ya zurfafa abin, yana ikirarin ba zai iya rayuwa ba tare dani ba yasa na d'auki alwashin sai na tarwatsa farin cikinshi dana iyayenshi. Na d'auki wannan ranar da muhimmaci saboda zan kunyatar dasu a bainar jama'an da suka gayyato, ban damu da tafiya dani a bakin duniya da za ayi ba tunda na fara cimma burina."
Daddy'n Ayshat dake zaune yace.
"Hajiya nifa ban fahimci komai da kuke magana a kai ba?"
Yaya Muhammad da suke a tsaye suna jin abinda ke faruwa yace.
"Daddy magana ce mai tsawo.."
Saida ya duba mutanan dake wurin yaga ba bak'on fuska a ciki, Mommy ce da Ayshat yasa yaci gaba da magana.
"Daddy wad'annan da kake gani sune suka tarwatsa mana rayuwarmu gaba d'aya."
Nan ya kwashe komi ya fad'a masu. Ba k'aramin tashin hankali Daddy ya shiga ba.
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.