K'UDIRINA

133 10 0
                                    

K'UDIRINA

      ®
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

      ©
EASHA MD

Dedicated to Maryamerh Abdulrahman (Kwaiseh)

              26

   Wattpad@ayshatmadu

   Dubanshi yake, duba mai cike da takaicin abinda ya aikata, cikin fad'a ya fara magana.

"Ashe Salim dama kai mutumin banzane ban sani ba? Ashe rashin mutuncinka ya wuce yanda nake tunani? Ka bani mamaki da har ka iya ma Farida rashin mutunci a gidan iyayenta ba tare da kaji kunya ba. Wai mai kake d'aukan kanka da rayuwarka ne?"

Mom ce ta fito ta dubeshi cikin takaici tace.

"Ka san Allah baka isa ka bad'a mana k'asa a ido ba, ina mai tabbatar maka in har ni na haifeka sai ka aureta. Sai inga ta tsiya."

Kanshi ya kuma dafewa cikin zafin zuciya ya mik'e hannunshi rik'e da kanshi ya fara hayewa sama. Gaba d'aya binshi suka yi da kallo suna mai mamakin halinshi.

Duban Dad tayi wanda har yanzu ranshi a 'bace yake, tace.

"Wai meke damun yaron nan ne?"

"Ki barni dashi zanyi maganin taurin kanshi da yake nuna min."

Komawa yayi ya zauna inda yake jin zuciyarshi na k'una, bai san yanda zaiyi da Salim ba.

"Gaba d'aya yaron nan na rasa irin zuciyarshi, shi kad'ai ya fita zakka a cikin gidan nan."

Gyara zama Mom tayi had'i da cewa.

"Yanda ka san wad'anda yake tare dasu suna mashi asirin da suke sawa yak'i mana biyayya."

"To wa sani ma, tunda yaje ya shige masu, bai san ba k'aunarshi suke ba. Abin hannunshi suke so, da zarar ya koma baida shi zasu gujeshi. Gaba d'aya ya fifitasu a kanmu. Wallahi yaci sa'a ba iya k'ark'ashina kawai yake samun kud'i ba, da sai ya gane bashi da wayau. Ko yanzu ma idan baiyi wasa ba, dai-dai nake dashi zaiga matakin da zan d'auka a kanshi."

Da sauri Mom tace.

"A'a Kada kayi haka. Duk hukuncin da zaka mashi banda wannan, kade mashi koma miye, bana ma son kana fad'in haka. Salim mu muka haifeshi mu muke da iko dashi bashi ke iko damu ba, idan yaga ka mashi haka, zai k'ara d'aukar zafi damu . ka barshi a haka, idan muka aura mashi ita ai dole ya zauna da ita."

"Hakane kuma. Zai ko gane mun isa dashi."

Shiko Salim tunda ya shige d'aki ya rasa mai ke mashi dad'i. Fiddo wayanshi yayi inda hotunanshi suke ya bud'e, k'ura mata ido yayi, ya shagala da kallonta. Magana yayi wanda ya fito fili.

"Ba yanzu naso na  furta maki abinda yake raina ba, amma ya zama dole na furta maki, tun kafin na rasaki."

Dogon ajiyar zuciya ya sauke. Aje wayar yayi ya bud'e drawer, magani ya d'auko tare da d'auko robar ruwa ya sha, kwanciya yayi had'i da rufe idonshi ko zai samu yayi barci, ya samu sauk'in zafin da zuciyarshi take mashi, tare da saukar ciwon kan daya addabeshi.

*** ***
Fitowa tayi daga d'aki cikin shigar atamfa yafe da gyalen da yayi shige da kayan jikinta, taddashi tayi a tsakar gida zaune yana jiranta.

"Yaya har na gama shiryawa zan tafi."

Ta fad'a mashi cikin girmamawa.

Cikin kulawa ya furta.

"To gashi kiyi amfani da wannan."

Hannu tasa ta amsa tare da godiya.

"Idan kinje ki gaida min da Umma."

"To zata ji." Ta fara tafiya, binta yayi da kallo yana mai jin son 'yaruwarshi a zuciyarshi.

Fitanta keda wuya, ta samu abin hawa da zai kaita gidansu Zarah, fad'a mashi inda zata tayi, ta shiga. Suna isa ta sallameshi ta shige gidan.

Zarah ce ta rugo da gudu ta rungume Islam had'i da cewa.

"Kash! Mai yasa ma nazo na tareki, bayan kin yadani kin canza k'awaye."

Ta idasa maganar idonta na kan Islam.

"Kai Zarah! Ai kin san banda tamkarki a duniyar nan, ba k'awar da zata kamoki sai dai ta bi bayanki."

Hararar wasa ta bita dashi, da murmushi d'auke a fuskarta ta furta.

"Eh ai kya fad'a min haka, tsarani lawyer."

Dariya suka yi gaba d'aya suka wuce d'aki, samun wuri tayi ta zauna kusa da Umma tare da dafata tana mai cewa.

"Umma ina wuni?"

D'auke da fara'a a fuskar Umma ta furta.

"Lafiya lau Islamuna, kin 'boye gaba d'aya."

"Wallahi Umma karatu ya 'boyeni."

"Kajita wai karatu, to waye baya karatun?"

"Umma kin jita ko?"

"Ni ba ruwana kunfi kusa."

Ta fad'a tana dariya.

Kayan biki ta ciro a jakarta ta mik'a masu had'i da cewa.

"Ga kayan bikin Yaya."

"Lallai har bikin yazo kenan? To Allah ya nuna mana."

Suka amsa da amin.

Nan ta d'an jima sannan Zarah ta rakota nan suka tsaya fira kamar kada a rabu.

Suna nan tsaye bakin titi dan jiran abin hawa. Wata mota ce ta tsaya kusa dasu, fitowa yayi ya tako inda suke, matashi ne da bai wuce shekara talatin ba, sallama ya masu, inda suka amsa.

Duban Islam yayi had'i da cewa.

"Idan ba damuwa ko zan samu number d'inki, saboda bai dace na tsaidaku a titi ba."

Kauda kanta gefe tayi ba tare data bashi amsa ba.

Fatima ce tayi magana.

"Kada ka damu! Bari na baka."

Bashi tayi yasa tare da mata godiya. Tafiya yayi ya barsu nan.

Islam ce tabi Zarah da harara had'i da cewa.

"Haba Zarah meyasa kika min haka? Haka kawai baki san mutum ba, baki san daga inda yake ba zaki bashi number d'ina?"

"To yi kukan mana, kin wani 'bata fuska kamar zaki yi kuka. Haba yarinya wannan had'd'd'an  guy d'in haka kike son wulak'antawa. Ga kyau ga kud'i, ni har gani nayi ma kunyi kama."

"Mutss! Kede kika sani, bade kud'in ba, kyan hali shine komai, ni bari kiga tafiyata, kina 'bata min lokaci. Amma ana jibi biki zaki taho dai ko saboda shirye-shirye?"

"Eh Insha Allahu."

Taran keke napep tayi dan ya maidata gida. Zarah ce ta k'ara ce mata.
"Kada fa inji kin koreshi, dan kin san dole ki rabu da Yaya Muhammad."

Harara ta bita dashi.
Sallama suka yi ta tafi.

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now