*K'UDIRINA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Dedicated to Maryamerh Abdulrahman* (Kwaiseh)
*34*
*Wattpad@ayshatmadu*
Mommy Amina ce ta fito ta shiga dashi d'akinta ta mashi wanka ta shiryashi cikin riga da wando na barci, nan palour ya dawo yaci gaba da wasanshi.
Gajiya yayi da wasan ya kwanta nan kan kujera yayi barci.
Karime ce ta fito palour dan yin kaye-kayen kayan dake wurin, ganinshi yana barci yasa ta d'aukeshi ta kaishi d'akinshi da tuni a gyare yake, wanda aka k'awatashi komai na d'akin kalan blue ne.
Shimfid'eshi tayi tare da rufeshi da bargo.
Ta fita had'i da ja mashi k'ofar ta rufe.
Barcinshi yake cikin kwanciyar hankali.
Mommy ce ta fito ta tadda bata ganshi ba, ta tambayi karime dake gyara wuri.
"Ina Muhammad d'in?"
Fahimtar abinda ta fad'a yasa ta bata amsa da.
"Yana d'aki yayi barci."
Girgiza mata kai tayi d'auke da murmushi a fuskarta, kana tayi d'akin nashi, zama tayi kusa dashi tana mai addu'a, sai da ta gama sannan ta shafa mashi a jiki, ta mik'e taja k'ofar tayi d'akin Daddy.
*** ***
Washegari da asuba Daddy da kanshi ya shigo ya tadashi suka tafi masallaci, suna dawowa ya koma barci, bai tashi ba sai misalin k'arfe goma na safe. Hajara ce ta shigo, ganin ya tashi ta had'a mashi ruwan wanka, ta mashi wanka, Mommy ta shigo ta kalleshi da fara'a, shima dariyar yake mata."My boy ka tashi?"
Duk'awa yayi har k'asa don gaidata.
"Mom ina kwana?"
"Lafiya lau."
Ta furta tana mai dafa kanshi.
"Sannu da k'ok'ari Hajara."
"Yauwa Hajia."
Ta furta tana mai d'an russuna kanta.
Duba mashi shadda tayi d'inkakke mai had'e da malum-malum da babanshi yasa aka d'inka masu suka yi anko.
Hajara ta mik'a mawa tare da fad'in.
"Kisa mashi wad'annan."
Samun wuri tayi ta zauna tana kallonsu.
Shiryashi tayi ta karya mashi hula ta sa mashi.
Mom dake zaune tana kallonsu cikin dariya ta furta.
"Wow my son.!"
Rungumeshi tayi da dariya har yanzu a fuskarta."Kaga yanda kayi ka fito a bahaushenka."
Hajara ce ta hard'e hannunta tana kallonsu tana murmushi, dan ji tayi duk sun birgeta.
"To yanzu muje muyi break ko?"
Kama mashi hannu tayi suka fito a tare Hajara na biye dasu a baya.
Daddy dake zaune a kan dinning ya bisu da kallo ko k'iftawa baya yi, d'auke da murmushi a fuskarshi, yana mai jinsu a zuciyarshi.
K'arasowa suka yi, Muhammad ya duk'a har k'asa ya gaidashi.
D'agoshi yayi ya d'aurashi kan cinyarshi, hannu ya mik'a mashi suka gaisa, tare da cewa.
YOU ARE READING
K'UDIRINA
Fiksi PenggemarLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.