*K'UDIRINA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)
*52*
*Wattpad: Ayshatmadu*
Zarah ce ta nisa tare da cewa.
"Islam bud'e idonki muyi magana."
Bud'e idon tayi a hankali tana duban Zarah.
Dogon ajiyar zuciya tayi kana tace.
"Islam a matsayina na 'kawarki aminyarki ina so ki natsu ki maido hankalinki sosai ki manta da maganar Abdallah."
Hawaye ne ya zubo mata tace.
"Zarah ta yaya zan manta da maganar ba bayan ya riga ya shigo rayuwata. Zarah ban san yanda zanyi ba, ina cikin tashin hankali."
'Kara fashewa tayi da kuka! Ri'keta Zarah tayi tace.
"Na fahimceki Islam, ki kwantar da hankalinki komai zaizo da sau'ki, yanzu kiyi shiru ki saki jikinki na tabbata Yaya Muhammad zai fahimceki."
Share mata hawayen tayi da hannunta.
"Yanzu ki koma ki kwanta ko zaki samu barcin ya 'kara d'aukanki kafin drip d'in ya 'kare."
Komawa tayi ta kwanta d'in ta rufe idonta kamar mai barci.
Yaya Muhammad ne da Aunty Fatima suka shigo.
"Har yanzu barcin take bata farka ba?"
Cewar Yaya Muhammad dake 'ko'karin aje basket d'in abincin.
Zarah tace.
"A'a ta tashi."
Bud'e idonta Islam tayi ta dubi Yaya Muhammad dake kallonta.
"Islam ya naga fuskarki ya kumbura ko 'kara kukan kika yi?"
'Ko'karin mi'kewa tayi ta zauna ta jingina da 'karfan gadon.
Hawaye ne ya 'kara zubo mata. Ganin hawayen yasa duk ya rud'e ya fara tambayarta.
"Me kuma aka maki? Kiyi shiru kinga baki da lafiya."
Aunty Fatima ce tazo ta zauna kusa da ita tace.
"Islam akwai abinda kike so ne? Ko labarin da kika ji ne bai maki dad'i ba?"
Cikin kuka tace.
"Aunty Fatima na san labarinmu idan akwai wanda ban sani ba 'kalilan ne. Aunty Fatima kawai dai ina jin yanayina ne ba dad'i, ban san mai yake damuna haka ba, bana jin dad'in dukiyar gaba d'aya."
Ta idasa maganar had'i da kwanciya jikin kafad'ar Aunty Fatima hawaye na d'iga mata.
Yaya Muhammad ya dubi Zarah yace.
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanficLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.